Sashe 18
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
fito ya saka tufafin da ya siya ya bar nasa a gurin ya dauki kudin da rikonsu dole kawai suka zame masa da Atm ya saka aljihu sannan ya dauki wayar da Nimra ta bashi, Hotonta ne shimfide saman screen din wayar tana murmushi ta sha kwalliyar zamani har ta sauya kamanni. Samun kansa yayi da tsayawa kallon hoton sannan ya saka wayar aljihu ya dauki ledar biscuits dinsa da lemu ya fice daga dakin. A dole gurin hutarwasu ya tsaya bayan ya fito Masallaci yayi sallah, sai da aka gama wanke motar aka goge sannan ya shiga, ya kama hanya, be bar garin Kano ba sai da ya siya Soap da yawa ya wasu abubuwan bukata ya zuba a motarsa, shagon da ya siye kayan ba su karbi dala ba sai ATM ya ba su suka cire kudinsu, sannan ya kama babbar hanyar fita daga Kano ba dan ya san garin da zai tafi ba. Yana tukin yana cin biscuits da lemun da ya siya, not his regular biscuits da lemu sai ya ji tas din wani iri ba irin wadanda ya saba ci ba, sai dai ba laifi wannan ma yana da dadi. Hakan wata zuciya ke raya masa ya koma garin Kano ya shige gidan Hajiya Jamila yayi zama, sai kuma ya ji ba zai iya ba, a ganinsa ita ma ai saboda mahaifinsa ya santa, after that kuma zata iya fadawa mahaifinsa cewar yana gurinta, a yanzu be bukatar wani abun da ya shafi mahaifinsa. Driving kawai yake heading to Katsina ba dan yana da kowa a garin ba, ba dan kuma ya san kowa ba, Impact ba dan yana sha'awar zuwa garin ba sai dan ba shi da gurin zuwa. ...WANI GARI... _Na Khadeeja Candy_ Namra ta matsa kusa da ita ta karbi wayar ta duba hoton, sai gata suna kallon kallo ita da Nimra, sai a yanzu Namra take tuna ta sha ganinsa a media amman how come ta ganshi a fili bata gane shi ba. Nimra ta yi baya ta zauna saman kujera ba tare da tace komai ba, Namra shiru ta yi gudun kar ta furta abun da zai saka jefa yar'uwarta cikin matsala, domin idan Ummi ko Abiey suka san cewar ta bashi motarta za su yi mata fada sosai. Ummi da wani abu mai kama da kashi ya tsoki kahon zuciyarta saboda ambatar sunan Ameer da na mahaifinsa da Mahmood yayi ya saka ta kasa zama ta kuma kasa motsawa zuciyar sai ciwo take mata. Ummi Namra ta kira sunanta ganin yadda ta tsaya kamar hoto, da sauri ta kalli Namra irin kallon kamar bata cikin hayyacinta, wani abu take ji mai kamar kuka kuma ba kukan ba, ba zata iya kiran da damuwa ba, haka kuma ba almara ba ce, wata kila mamaki take na sunan da ya zo daya, wata kila kuma wani bangare na zuciyarta gaskiya yake fada mata cewar Ameer dinta ne. Ko shiyasa Abiey yace a bar magana sun yi solving matsalar da mahaifinsa.? Daker ta iya tara yawun bakinta ta jika makoshinta sannan ta juya ta cira kafarta da take jin kamar ta shekara bata taka ta ba, ta fara tafiya. Ummi lafiya Mahmood ya tambaya domin hankalinsa yana gurinta, Nimra kam nata hankalin yana can gurin wani tunanin na dabam. Na'am Ummi ta amsa sannan ta juyo ta kalleshi gaba daya a rikece take irin rikicewar abun da kake tsammani ko tsoron ya faru, irin rikicewar wanda hankalinsa ke daf da gushewa, ba kuka take ba sai dai kana kallon fuskarsa kasan akwai tashin hankali a zuciyarta da fargaba. Lafiya Ya sake tambaya hakan ya hanyo hankalin Namra gareta, Hajiya Zahra ta kasa cewa komai kallonsa kawai take amman hankalinta da tunaninta suna wata duniyar ta dabam, ba tare da ta sake ce masa komai ba ta juya ta fara takawa suka bita da kallo har ta haye sama ta shige dakinta. Sai ta maida kofa ta rufe ta nufi gadonta ta zauna kwakwalwarta na tuna mata da abubuwan da suka faru a baya, yayin zuciyarta take soyuwa da kuskuren da ta aikata. A hankali Namra ta turo kofar dakin ta shigo rike da jakar Hajiya Zahra da wayarta da ta bari a falo. Ummi ga wayarki da jaka Wannan karon tana dagowa sai hawaye suka sauko mata, a sanyaye Namra ta ake jakar saman gadon ta zauna kusa da ita. Ummi lafiya? Sai ta yi saurin share hawayenta. Tsoro nake kar..... Kar.... Kar... Yaron ya sake yi ma Maleek wani abu.... Ta fada ba dan komai ba sai dan ta kawar da tunanin Namra akan hawayenta. In shaa Allah ba zai sake ba, ko da ba a hukunta shi ba ai ya tsorata da yadda aka dauki abun da muhimmanci kuma kin ji har mahaifinsa ya kore shi Ummi ta juyo wasu hawayen na taruwa a fuskarta ta rike hannun Namra. Toh idan ya fada wani halin fa, nuna min hotonshi Namra To koma minene ai shi ya jawa kansa, kuma hukuncin da mahaifinsa yayi zai saka dole ya kiyaye gaba Ta fada tana daukar wayar Ummi ta shiga google ta kama hotonsa ta nuna Hajiya Zahra. Hannu biyu Hajiya Zahra ta saka ta karba kamar wanda aka bawa sakada, gabanta na wani irin bugawa da ya wuce kima kanta har sarawa yake, hotuna ne da yawa a zube ko wane da kalar style dinsa, hannunta na rawa ta saka yatsanta ta taba daya sai ya bude a babban hoto, zaune yake akan kujera ya saka kananan kaya wando da riga ya dan karkata fuskarsa kadan ya kalli wani wajen dabam. Kamanin Deen ta gani zube a fuskarsa ciki har da hade rai da haske. Da gaske sunansa Ameer? Kuma dan Mr Bashir ne? Ta tambaya. Ummi gashi ma kina gani a rubuce Namra ta amsa mata tana kallonta, sai ta daga kai ta sake girgizawa. Tun tana kallon hoton da kyau har ta koma bata ganin komai sai duhu hannu ta saka ta fara shafa wayar. Namra Hoton ya bata, dawo min da shi na sake gani Ummi ai kin jika wayar da hawayenki ba zaki iya gani ba Sai a lokacin ta san hawaye ne ya rufe mata ido take ganin duhun. Hannu ta saka ta share amman suka ki tsayawa tana kokarin ganin bata yi kuka a gaban Namra ba amman abun ya ci tura har sai da ta fashe da kuka mai karfi, ta saki wayar hannunta ta saka hannayenta ta rufe fuskarta. Subhanallahi Ummi lafiya? A take hankalin Namra yayi matukar tashi, sai ta rumgume mahaifiyarta tana rarrashinta, can kuma ta sake ta mike tsaye ta fice daga dakin da sauri, bata dade ba ta dawo dakin tare da mahaifinta Nimra da Mahmood suka shigo daga baya Maleek ya shigo dakin ya tsaya jikin kofa ya rumgume hannayensa, yana kallon Namra dake fadawa Abiey abun da ya faru. Ummi ta cika daukar komai da girma, ko karamin abu ne sai ta dauka ta saka a ranta Maleek ya fada, duk a tunaninsu saboda abun da ya faru ne take kuka ban da Abiey da ya san dalilin kukanta. Ku fita waje bari na yi magana da ita Fita suka yi daga dakin cikin damuwa, ko a tsakaninsu wani ya shiga damuwa damuwa suke da Matsalarsa balle kuma uwa kamar Ummi. Sai da suka fice sannan ya zauna kusa da ita ta kalleta da duba na tsanaki da natsuwa ya ce. Wannan kukan duk na minene? Na fada miki an yi solving matsalar nan komai ya wuce, kuma na miki alkawari iri haka ba zai sake faruwa ba Sai a lokacin ta samu damar dago kai ta kalleshi da jajayen idanuwanta. Abiey ka san yaron nan? Ni ban taba ganinsa ba Amman kasan mahaifinsa? Aa na dai yi magana da step mother dinsa Ta hade kuka daker. Mahmood.... Mood.... Ya ce dan Mr Bashir ne kuma yan Kano ne Eh haka ne, mun yi magana da ita kuma ta tabbatar mana cewar ba zai sake ba Ta kai hannu ta dauki wayarta ta bude ta nuna masa hoton Ameer, karba yayi ya duba. Oh shi ne wannan yaron kamar mai natsuwa, Allah ya shirya na fadawa Maleek kar na sake ganinsu tare Ranka ya dade Ameer ne, Ameer..... Ameer... Wane Ameer kuma? Gangan yayi mata haka saboda ya kawar mata da tunanin da take. Dana Ameer... Wani irin deep breath Abiey yayi taking sannan ya ce. Kina da wani a bayan Maleek da Mahood? Hajiya Zahra ta kalleshi da duba na irin wanda yake son yayi wasa da hankalinta ya juya tunaninta. Ameer ana na farko da na fara haihuwa, an da na haifa da Deen, ka kalli fuskarsa sunansa da sunan mahaifinsa Wani irin kallo Abiey yake mata mai kama da harara zuciyarsa ta hau bugawa da mugun karfi. Wata kila ba ki gane ba ne Na gane shi Ameer ne Wallahi, ta ya zan auri ubansa na haife, na kwana da shi a raina na tashi da shi har yau tunanin Ameer be bar raina ba kuma ka fada min cewar ban gane ba, wannan ana ne Abiey jinina ne, ka daina canja min tunani Abiey mu ba yara ba ne Mikewa yayi tsaye ya daka mata tsawa da sai da ta zabura. Kin gane shi saboda har yanzu kina rike da shi da ubansa a ranki, na dade da sanin cewar Mr Bashir yana garin nan tare da Iyakinsa sai dai ban san akwai alaka tsakanin ansa da Maleek ba, da ban bari abun ya kawo haka ba, ni da ke mun dade da rufe babin Deen da duk wani abu da ya shafe shi, a dai kin riga kin siyar yana da rayuwarsa da iyayensa a yanzu, yana da dangi da yan'uwa, ba san ki ba be san da labarinki ba, so this should be the last time da zaki sake yin maganar Ameer a gidan nan, kar son zuciya ya saka ki rusa rayuwarsa da ta wanda kika bawa, karki ruguza farincikin Mr Bashir da shi kanshi Ameer din, and mafi muhimmanci yarana ba su san da wannan maganar ba, ba su san ma kin taba auren wani kamin ni ba, karki kawo mana wani bakon al'amari a gida, na fi son yayana