Sashe 72
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
tambayarsa mahaifinsa. Tana nan, ya bar aiki yanzu saboda shekaru sun ja kuma yana fama da ciwon sashe ba komai yake iya yi ma kansa da kuma spinal cord injury Dole... Abiey ya fada sai duk suka kalleshi har Ummi dake kokarin nuna masa abun da yake ba daidai ba ne da ido, balle kuma Maleek da Mahmood da ba su fahimci komai ba, Shuraim ma kallon Abiey yayi da karshen zancensa ya biyo tare da kora da hali. Mun gode sosai da gabatar da kai Shuraim sai ka ji daga garemu Abiey ya mike tsaye ya fice daga falon, Ummi ta bi bayansa. Abiey na shiga dakin ta rufe shi da fada. Abun da ka aikata be kamata, yaron nan be san abun da mahaifinsa ya aikata ba, kuma be kamata laifin mahaifinsa ya shafe shi ba Toh me kike tunani? Na bada yata aure ga zuri'ar Dr Hamid? Ko kin manta waye shi? Kai da kake kokarin ganin sirrin nan be fita ba, kuma kai zaka ce ba zaka aurawa yarka wanda take so ba, saboda laifin da bana jin yaron nan ya san mahaifinsa ya aikata Kika san wane kalar hali da shi? Ana son idan zaka yi aure ka zabawa yarka miji na gari To me ye aibun Shuraim? Karka rusa farincikin Namra saboda wani selfish interest na ka, Nimra ta yi kuskure kuma addini ya haramta aurenta da Ameer amman Namra fa? To kake duk yaran su taro suna mana kallon azzalumai? Ka fi kowa sanin meye so karka saka yarka a damuwa saboda abun da wani ya aikata, Namra tana son yaron nan kuma idan har bincike ya tabbatar da ba shi da matsala za mu aura mata shi Tana kaiwa nan bata tsaya jiran abun da Abiey zai fada ba ta fice zuwa part dinta. Bayan fitar Abiey da Ummi Shuraim ya mike tsaye yayi musu sallama ya fice falon tare da abokinsa. A waje suka samu Waira tsaye gurin motarsa ta ci kuka har ta gaji ta barwa Allah, tana ganinsa ta mike tsaye da sauri tana kallonsa, ya karaso kusa da ita yana kallonta da damuwa a fuskarsa. I'm sorry... Sai kawai ta fashe da kuka ta rumgumeshi. Ai ga irin ta nan yanzu idan suka leko suka ganka fa? Ko fitowar da muka yi hakan be kamata ba ko sallama baka yi ma Namra ba, kuma kamata yayi ka bari sai kowa ya fice tukuna Abokin ya fada cikin rada yana waige waige kamar marar gaskiya. Ba damuwata ba ce kai baka ga abun da suka mana ba? Ai ba ni nace ta rumgume ni ba, daga ni bata jindadinsu Ya dago kanta ya saka hannu ya share mata hawayenta. Waya kawo ki nan? Mutanen nan masu bakin kaya Murmushi ne ya bayyana a fuskarsa jin yadda ya tambaye ta ta amsa masa da saura. Yanzu kin iya hausa kenan? Na iya rubutawa wani ina karantawa ina ji duka amman bana iya fadar duka, ko turanci ana koya mana a makaranta Cikin kuka take fada masa tana kara komawa jikinsa ta rumgumeshi. Su waye mutanen da aka kawo kin gurinsu? Miye alakarki da su? Suna nan, Ummi kadai take so na da Nimra, amman Namra bata so na da Ya Maleek tsawa ma yake min amman Mahmood na so na Abiey ma baya so na Me aka kawo ki yi gurinsu? Dan girman Allah da darajar iyayenka ka shiga motar nan mu tafi, ba mutunci ba ne a tararda kai da yarinyar nan ina ruwanka da alakarta da mutanen gidan? Kai dai abun da ya kawo ka dabam, kar ma ja a fara yi mata fada ko duka Rokon da abokinsa yayi masa ne ya saka shi dagota daga jikinsa. Zamu tafi Baby Girl amm... Bata iya jira ya karasa naganar da zai yi ba ta fashe da kuka tana girgiza masa kai. aa aa aa nooo karki tafi, ka zauna a nan ina so, Shuraim ina sonka, ina sonka so much Sonshi take da gaske amman ba irin na soyayya ba, irin son nan dai da take yi ma Mahmood da Ummi, sai dai hakan ba hana jin wani iri ba, gaba daya sai ji kamar kar ya tafi ya barta duk kuwa da kasancewar ba tafiya ce ta barin garin Abuja gaba daya ba, tafiya ce kawai ta barin gidan for now. Zan dawo ba tafiya zan yi gaba daya ba Ta girgiza kai alamar ba zata yarda ya tafi ba, ihun da take ne ya saka Maleek fitowa waje daman tun da Shuraim ya fito zuciyarsa take waje, Yesmin ma fitowa ta yi waje tare da Mahmood. Keeee.... Waira ta kalli Maleek. Sake shi kuma ki yi shiru da bakinki Ta yi shirun kamar yadda ya fada mata. Matsa gefe Ta matsa yana kallon Shuraim hawaye na sauko mata wasu na bin wasu. Shuraim ya kalli Maleek sai ya ji baya sonsa saboda yadda yake matsawa Waira da kuma yadda ya ga tsoronsa a fuskarta. Zan dawo na ce, ki daina kuka share hawayenki Ta saka hannu biyu ta share hawayen wasu an zubo mata. Shuraim ya shiga motar abokinsa ya tuka suka fice daga gidan zuciyarsa cike da tausayin Waira. Suna ficewa daga gidan Waira ta auna da gudu cikin gidan wato part din Ummi tana kuka kamar ranta zai fita. Ita fa bata.... Mahmood zai yi magana Maleek ya tari numfashinsa rai a bace. don't tell me rubbish please... Barin gurin suka yi shi da Yesmin, shi kuma ya tsaya yana ta kallon harabar gidan. Daga bisani ya kalli gate din gidan da aka buga, kamin Police din dake gadin gurin shigo da wata matashiyar yarinyar, har ya fara danna waya ya kara a kunne sai kuma ya nufo cikin gidan sakamakon hango Maleek da yayi tsaye. Wata yarinya ce ta zo yanzu, tana son a barta ta shigo cikin gurin Nimra, tace ita kawar Nimra ce ga wayarta ma a hannunta zata bata, ni kuma Alhaji be fada min cewar wani zai zo ya ga Nimra ba kuma yace karmu kuskura mu bar Nimra ta fita, shiyasa na ce ta jira sai na tambaya idan an santa ko kuma an san da zuwanta Kamin Maleek ya yi wata magana suka ji ihun Ummi, Maleek ya juya ya koma cikin part din Abiey da sauri, a nan suka sha banban da Mahmood da ya fito dauke da Nimra kamar matacciya Namra na bayanta tana kuka, Humaira na ganin haka ta juya da sauri ta bude gate ta ranta a na kare, kamar mahaukaciya haka ta fara waigen inda zata ga motar Ameer, tana hango motar ta baza da gudu tana isa ta bude motar ta shiga da sauri. Tuka tuka tuka kar su biyo mu? Su wa? Ya tambaya hankalinsa kwance. Ban sani ba na ce ka ja karsu kama ni Rufe bakknta ke da wuyaya hango police din dake gadin gidan da kuma masu farin kaya sun fito da gudu sun nufo inda suke, da karfi ya ja motar suka hau titin da gudu... *Littafin WANI GARI na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660* Ummi ce ta fara zaunawa bakinta a bushe saboda kuka, sannan Abiey ya zauna a dayar kujerar dake fuskantar wacce Ummi ta zauna cikin damuwar data gagara boyuwa a fuskarsa. Likitan da zai kai akalla shekara 37-40 ya kalli Abiey cikin natsuwa ya ce. Bana son na daga muku hankali, amman gaskiya rayuwar yarku tana cikin hadari, ban sani ba ko kina da masaniyar damuwar da ta jefata a wannan halin ko kuma aa, mun yi iya kokarin da zamu wajen ganin komai ya daidaita, Alhamdulillah kamar yadda kuka gani she's alive amman irin rayuwar dake daf da zaba mata mutuwa, domin har yanzu bugun zuciyarta be dawo daidai yadda ake sonsa ba, matsalar karamci numfashi kuma mun shago akanta saboda tukunyar iskar Oxygen da muka saka mata wacce ta taimakawa numfashinta tafiya yadda ya kamata Ummi ta kalli Abiey hawaye na sauko mata kamar ba gobe. Doctor zamu iya yin maganar daga ni sai kai? Saboda kar hankalin mahaifiyarta ya tashi Hankalina ya riga ya tashi Abiey, tsoro kawai nake ji kar mu rasa Nimra, saboda ba zamu iya bata abun da take so ba. If na canka daidai kamar kun san damuwarta Likitan ya tambaya sai Ummi ta daga masa kai. Toh shawarar da zan baku gaskiya ku bata abun da take so, idan akwai wanda take son aura ko ta aura aka raba ta da shi to ku nemo shi, domin zuciyarta na bugawa fiye da kima kuma abun da nake son na tambaya shin ta dade da wannan ciwon ne? Ban sani ba, amman dai tsakanin kwana hudu zuwa biyar akwai wanda ta rabu dashi saboda wasu matsaloli,ban sani ba ko shi ya haifar da wannan matsalar Yeah daman ana samun irin haka, amman ba kasafai ba gaskiya sai ga mutum da suka dauki abu suka saka a rai, kamar wadanda suka rike abun sosai a ransu ko kuma ba su taba samun irin wannan damuwar ba sai a lokacin, but most of the time ciwon zuciya yana farawa da ciwom kirji rashin samun wadataccen numfashin ciwon kai da canjin bachi da dandano abinci wani lokacin ma har abincin baka so. Sai dai bugun zuciya abu ne mai matukar hadari da akan iya rasa rai ko rayu, musamman ma irin nata da duk kokarin da muka yi mun kasa samun daidai bugun zuciyarta, wannan ya saka na bukaci ganinku, saboda na fada muku gaskiya idan akwai abun da zaku yi wanda kuka san shi ne silar ciwonta sai ku aiwatar saboda samun lafiyarta Ummi ta fashe da kukan data kasa rikewa, ta tashi da sauri ta fice daga office din. Tana tafe tana hawaye har ta iso kebantaccen dakin da aka aje Nimra na masu hannu da maiko, a nan ta samu damar daidaita nata numfashin ta yaki zuciyarta har kukan ya tsaya mata, sannan ta tura kofar akin ta shiga. Namra da Mahmood ne a cikin dakim tsaye suna kallon Nimra dake kwnace sanye da oxygen ta lumashe ido kamar mai bachi, har sai da Ummi ta karaso kusa da