← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 165

Sashe 33

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

rufe ido gam, mutane suka yi cincirodo sai kallon ikon Allah suke, daga ma'aikan Asibitin har wandan ake jinya da masu jinyar, wadanda ba sun da zamanta ba a gurin ba ma sai da suka sani, har yan wani Ward din sai da suka zo kallonta. Dr ka samu mata Wani likitan ya fada yana zolayarsa, Dr yayi murmushi be ce komai ba, ya kalli police din ya ce Bari na dauko kayana sai mu tafi da ita a can Hakan zai fi kam, domin abu ne mai wahala ta yardar ta bisu Shi ne abun da kowa ke fada, Dr ya daga kansa ya samu daker da cire hannunsa daga rikon da ta yi masa, sai ta kara kankanme jikinsa. Tana jin ya fara tafiya sai ta taka ita ma amman bata yarda ta bude idon ba, takawa take tana jin kamar tana taka ruwa saboda sanyin tile din bata taba tafiya a kansa ba, daker ya samu ya fita daga gurin, Office dinsa kam sai wani ne yaje ya dauko masa kayansa ya kawo masa, tana ta jin hayaniya mutane yayi yawa ta san sun fito guri mai mutane da yawa, a hankali ta bude idon ta kalli yadda gurin yake wasu na kallonsu wasu kuma na da hada hadarsu, dagowa ta yi ta kalleshi sai yayi mata murmushi sai ta sake rufe idon, sai da ya isa gurin motarsa ya bude sannan ta sake bude idon sokoko ta yi tana kallon motar at first bata ji tsoro ba sai mamaki tana kallon motocin da ba daya ba, ta kai hannu zata taba wani motar dake kusa da ta Dr yayi ma motarsa key karar da ta yi ya saka ta zabura ta dauke hannunta da sauri tana tasa motar a firgice, take hankalinta ya tashi ganin haka ya saka Dr ya ce. Mota zamu shiga Sunan mota ta fara rikewa, domin shi ta taba ji a bakin Eid. Outarrr Ta maimaita sunan a ranta tana tuna yadda yake fada mata cewar wasu mutanen na dabam a wata duniyar suna hawanta su yi tafiya, bata taba sanin haka motar take ba sai yau, Dr ya kai hannu ya bude motar yayi mata alama da ta shiga da hannu, a take ta lake masa kafada alamar bata zata hau, he never thought da gaske take har sai da yayi unkurin sakata da karfi sai ta sake shi ta ruga zata fita daga gurin sai kuma ta rasa gurin waye zata tafi mutanen dake gurin sun mata wani iri da bata saba da su ba, ga gurin ababen hawan sun yi yawa ba mota kadai ba har da babur. Gudu take tana neman gurin boya ta rasa gurin wa zata tafi mutane sai kallonta ake kuka take sosai tana waige waige ta gudu nan ta dawo nan haka take har ta samu gurin wata fulawa ta boya ta nade guri daya kamar macijiya ga hannunta sai zafi yake mata zuciyarta na bugawa da mugun karfi kamar zata fado. Dole fa sai da karfi za a shigar da ita motar nan in ba haka ba, ba zata shiga ba kana ganin wannan yarinyar kasan daga wata duniyar ta fito Police din ya fada, Dr Shuraim ya sauke numfashi cikin damuwa yana kallon inda ta gudu ta boya. Ya za'a tafi da ita Abuja nan ne? Ayi mata allurar bachi kawai Dayan ya fada yana ganin kamar hakan shi ne mafita. Ba'ayi ma mutun allurar bachi hakan nan kawai ba tare da lalura ba, da zaku aminta zan tafi da ita gidanmu for a while kamin ku tafi da ita Aa ba zai yiyu ba, mu umarni aka ba mu kuma ba zai yi mu saba umarnin ba Ya nufi gurin ya risina ya leki inda take gaba daya a firgice take hawaye har sun gaji da ita a idonta sun kumbura mata idon fatar idonta ta yi masa ja, fuskarta ma ta yi kamar an mareta. Eid.... Eid... Eid... Shi ne kawai abun da take fada tana jin kamar ace yana jinta ya zo ta yafi da ita, a yanzu kan ta shiryar fuskantar hukuncin garinsu siye da wannan rayuwar da take bata tsoro, rayuwar da komai na su ya banbanta da nata, ina ma mafarki take ba gaske, bata da kowa a duniyar nan bata san kowa ba, ba su da abubuwa irin nata, zuciyarta kuma ba raya mata cutar da ita za su yi. Khadeeja Candy Copyright 2023 KHADEEJA CANDY 18 A hankali ya risina kusa da ita ya mika mata hannunsa. Zo mu tafi Ta kalli hannun nasa hawaye shar a fuskarta gashin kanta dake cinkushe ya kara watsewa ya baibaye fuskarta wani ya sauko har bayanta, kallo daya zaka yi mata ka san a firgice take. Na kurame yayi mata ya nuna ta ya nuna kansa sannan ya jikansa da hannun guri daya, ya sake mika mata hannunsa sai ta daga kai ta nuna mishi mota ta girgiza kai, alamar ba zata shiga ba ta hade hannayenta ta rufe kunnenta. Iskar bakinsa ya busar yana tunanin yadda zai yi ta aminta ta shiga motar. Ba zata shiga da arziki ba, kawai ka bari a sakata da karfi idan ta gaji dole ta hakura ai Daya daga cikin police din ya fada yana nufo inda take rakube, babu yadda Dr Shuraim ya iya sai hakuri ya kawar da kai, ko bata fada masa ba ya san bata taba ganin mota ba balle har yace ta saba shigarta, yanayin shigarta da kalamanta sun nuna ba a irin duniyar da yake rayuwa ta rayu ba, Allah kadai ya san daga wace duniyar aka fito da ita. Hakan nan ya ji ihun da take a lokacin da police din ya rika ta yana damunsa, wani irin fisga take kamar babu ciwo a hannunta musamman da ya danneta da karfi ya saka ta a motar Dr Shuraim sai ta rika yin wani irin abu kamar zata shide ta mutu gaba daya. Sai da Dr Shuraim ya rufe kofofin motar ta ko'ina sannan ya yi ma motar key madubin gaban motar ya saita baya da shi so that ya rika kallon fuskarsa da shi, sai dai me ta sauka daga kan kujerar baya ta zauna a kasa ta takure duk rashin fadin gurin ta takure ta zauna a haka ta boye fuskarta ta rufe ido, tsit ta yi kamar ba ita ce take ta ihu ba, a yanzu ta gane wani abun ake yi ma ihu wani tsoron kan sai dai ka boye kanka ka saurari sakamakonka. Each and every minute sai ya juyo ya kalli bayan motar domin ya tabbatar tana lafiya, motar police din tana gaba yana biye da su har suka isa, state CID dake Katsina, a nan ta zama abar kallo a gurin wasu police din da labarinta ya iso musu kamin a kawo ta gurin. Motar aka bude gaba daya ana kallonta dayan ya fara cika umarnin shigabansu na kokarin fitowa da ita a nan ta fara sabon ihu sai da ta kuka gurin tana lakewa ciki. Idan ba yanzu za a tafi da ita ba, a bar a motar har zuwa lokacin da za a tafi da ita please, saboda bata natsu da kowa ba a nan It's very unusual police su yarda su bar wani a hannun wani, sai dai yanayin fuskar kalama da mutuncin da Dr Shuraim yake da shi a fuska ya saka DPO ya aminta bayan ya duba id card din aikinsa kuma aka hada shi da wani police daya da zai bishi su je ganin muhallin da za'a ajeta, sun amince ne sanin babu inda gurin da za'a ajeta ta natsu kamar a gurinsa domin ihun da take ba karami ne ba, kuma abu ne mai wahala ta yarda ta zauna a hannun a yanzu, gaba daya ko idonta bata yarda ta bude ba tun da suka saka ta a motar balle kuma ta kalli inda aka kawo ta ko kuma mutanen da suke gurin, gashi ba a yau za'a tafi da ita ba sai gobe da safe za a tafi da ita Abuja, ba ita kadai ba tare da motar Nimra za a kai. A motar Dr Shuraim ya barta bayan sun isa gidan police ya shiga ya gaisa da mahaifiyar sannan ya fito yayi musu sallama. Mahaifiyarsa Hajiya Hajara ta fito waje tare da kanwar Dr Maimoon suna kallon motar kamin Dr ya iso har Maimoon ta ita gurin motar tana kokarin budewa. Maimoon karki bude, ku shiga ciki idan ta ganku ba zata yarda ta fito ma bata son mutane tsoro take ji Ikon Allah Cewar Hajiya Hajara da gutun mamakinta domin bata taba jin mutumen dake tsoron mutane ba sai wannan bakuwar da aka kawo musu da ba zato babu tsammani, a kokarinta na kyautata masa ita da yarta suka fice daga gurin, shi kuma ya kai hannu ya bude motar ya taba ta, sai ta fara ihu. Shiiiiiiiii Baby Girl Ya kama dayan hannun mai ciwo ya rika mata a hankaloli, dayan hannunsa kuma yana rike da hannunta na hagu, yatsunta ya fara kallo sirara ne irin na mata akaifar mai kyau irin mao tsawon nan mai laushi, sai dai dattin dake ciki ya saka akafair ta yi mata kamar ta kwaba laka, ya sake hannunta ya mike tsaye ya cire key motar ya sake dawowa gabanta ya resina ya kama hannun a nan ma bata fasa halinta ba sai da ta yi masa ihu, sai dai be kula ba ya saka abun cire akaifa nails dake lake da keys din ya fara katse mata farcen, ko kadan bata jin ciwo amman sai ya mutsa fuska take tana. Ash ash ash ash ash ash ash... Kamin ta fisge hannunta ta bude ido domin ganin abun da yake mata, ta duba hannunta sai ta ga an yanke mata farce, ta kalleshi kamar za ta yi kuka sai yayi saurin nuna mata nasa hannun da babu farce ko daya. Bata yarda ba sai ta nade hannun ta maida baya, ko kadan be tirsasa kansa cewar sai ya yanke mata ba, sai ya saka abun a aljihunsa ya mika mata hannu alamar ta fito, a nan fa tace masa bari na duba inda nake, kallon iya inda idonta zai kai
Chapter 33 · 0% Book details