← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 165

Sashe 96

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

lokacin da maciji ya cije ni a daji, ban manta ba i will hate you more Zan zo Ya amsa ba tare da shiri ba. Yanzu? Gobe ina zuwa school da safe Zan same ki school din Kasan ina ne? Ki turo min address a waya Okay zan aje waya Good night Good Night Yeah Good Night Sai ta sake fada. Good night Okay sai da safe Sai da ta yanke kiran sannan ya fito daga dakin ya jefar da wayar akan bed, shi yana da alot of questions da zai mata, sai dai hakan ba yana nufi ko da ya tafi ya shiga gidan ba sai dai ya tsaya daga wani gurin ta zo ta same shi. Bata manta ba, mata suna rike abun da yayi musu ciwo a zuciyarsu Ya fada yana tuna zancen da ta yi masa cewar ya barta a daji bayan maciji ya cijeta. Storyteller He said, sannan ya nufi bathroom dinsa. UMMI's POV. Ummi da mamaki take kallon Waira, bata taba tunanin tana da wayo ba irin yau, a yanzu ta gane Waira ta tashi daga karamar yarinya da take mata kallo zuwa baba mai wayo da basira. Domin bayan maganar farko data rada mata cewar zai zo ta tambaye bata sake ce mata komai ba, ita ta tsara masa komai. Baki taba fada mana cewar kin san Ameer ba Waira, ashe shi ya dauko ki ya saka ki a motar Nimra? Ban san waya saka ni ba, amman dai na ganshi kuma ya gan ni, yana kallona a lokacin da maciji ya cijeni na yi ta neman taimakonsa be taimaka min ba har na suma ban san an saka ni a mota ba, ni dai na gani a wani guri tare da Sulem Ummi ta shafa kanta ta sumbaceta ta rumgumeta. Ina kaunarki Waira, yanzu kin san abun da nake so da ke, gobe idan kin tafi school, school bus ba zata dawo da ke ba, ina son ki roke shi ya kawo ki gidan nan, na san zai yi domin na lura kina da wani sirri a muryarki da mu'alamarki dake karya duk wata izza da fushi ko girman kai a gurin namiji, daman ko wace mace da yadda Allah ya halicceta, kin ga ni da ina kamarki farinjini na yi sosai da kiriniya, step father na ya sha wahala ta a lokacin har karyashi an yi saboda ni, Mamana kuma ba a magana Allah dai yayi mata rahama (Lallai kam dan mahaifin Deen da Deen sun sha duka saboda Zahra) Waira ta amsa. Toh Ummi, amman Ya Maleek ba zai yi ihu ba? Ba zai yi ba, babu abun da nake bukata a yanzu kamar kusanci da Ummi ta dago Waira daga jikinta. Gobe zan miki cake mai dadi ki tafi da shi Okay Ta nufi upstairs tana jindadi zata ga Ameer a gobe ta yi masa tambayoyi akan abun da ya shige mata duhu. She wake-up early saboda ta kwana rumgume da baby rabbit dinta da kuma tunanin haduwarta da Ameer. Tun asuba ta sauko kasa da zomonta ko wanke baki bata yi ba, ta nufi kitchen domin ta san Ummi ke shirya mata abun zuwa makaranta kuma tun da har ta fadi cewar zata yi mata cake. Ta leka Kitchen din kamar yadda ta saba sai ta samu Ummi da Mahmood a ciki yana taya ta aiki. Da kuzarinta ta shiga Kitchen din. Laaaa Ya juyo ya kalleta yana murmushi. Laa zaki ce yau ni nake taya Ummi aiki ko? Ya daga kai. Daddy ne ya raba mana aiki, yace yau idan na gobe Maleek ne, jibi Namra gata kuma ke, haka zamu yi ta yi har mu saba Ta juya ta kalli Ummi. Ummi Good Morning Good Baby tafi ki wanke fuska ki yi wanka, zan hada miki tea yanzun nan kamin cake ya zama ready Okay Ta juya ta fito daga kitchen din ta nufi stairs. hakan yayi daidai da shigowar Maleek falon, daman idan ya gama sallah azuba baya tashi a masallaci sai ya gama azkar dinsa, sannan yake shigowa gidan. Tsayawa ta yi sai da ya iso inda take ta gaishe shi kamar yadda ta Ummi ta koya mata. Good Morning Tsaye yayi yana kallonta sai ta sauke idonta kasa. Morning Ya amsa sannan ya wuce ya fara taka stairs din, bayansa ta bi, sai gashi ya tsaya ya juyo ya kalleta. Waye Ummi ta ce ki dauko waya a kira jiya da dare? Malamina A take ta kirkiri karya ta fada masa abun da ba halinta ba. Domin bata yin karya mo matter what, a yanzun ma tana tsoron ya ce zai dake ta ne. Be ce mata komai ba ya juya ya haye sama, sannan ita ma ta shiga dakinta. Karfe bakwai da rabi school bus ta faka kofar gidan, sanin lokaci yayi ya saka Waira ta aje kofin tea da take sha ta ta dauki jakarta dake gefenta ta mike tsaye. Ummi time yayi Ummi ta so daga kujerarta ta matsa kusa da Waira ta sumbancin goshinta. Allah ya miki albarka, ga cake din na musamman ne na yi, yayi dadi sosai ki ci da yawa Okay Ummi Thank you Ta karbi cake din ta nufi hanyar falo, Ummi kuma ta kalli Mahmood ta ce. Please fita ka fadawa driver bus din ba shi zai dawo da ita ba, za a zo a dauke ta ne Mahmood Ummi take yi ma magana amman Maleek ne yayi tambaya. Waye zai dauke ta? Ummi ta kalleshi. Ni zan je na dauke ta, ina son na gwada driving ne yau Maleek ya juyo yana Waira da Mahmood ya rufa nata baya domin cika umarnin Ummi. Ba driver makarantar ke da alhaki ba, principal dinsu ke da alhaki, dole idan za a yi haka, ni ne zan kira na sanar musu ko kuma Abiey Ya fada bayan ya juyo da kansa. To ka sanar musu Zan sanar musu, sai muje tare mu dauko ta, Abiey ya ce mu daina barinki kina aikin wahala Ya fada sannan ya mike tsaye ya bar dinning din. Ummi ta bishi da kallo tana tunanin yadda zata bullowa lamarin. Tashi tai ita ma ta nufi stairs sai da ta fara leka dakinta ta samu Dr da yaranta wato Jabir, Umar Juwairiyyya da kuma Yesmin sai yarta Namra suna karyawa, bata ce musu komai ba ta saki kofar dakin. Ta juya tana kallon bangaren da dakin Nimra yake, a take idonta ya cika da hawaye, takawa ta yi ta karasa har bakin kofar dakin ta murda kofar ta bude ta shiga ciki. Katon hoton Nimra dake manne ta fara kallo hawaye na mata zirya, sannan ta kalli wanda suka yi tare. Allah ya miki rahma yata Ta furta cikin kuka sannan ta karasa ta zauna saman gadonta kamin ta kwanta ta lumshe ido tana kuka. Kamar yadda Ummi ta bukata Maleek ya kira makarantarsu ya sanar musu school bus ba zata kawo Waira ba zuwa za'ayi a dauke ta, as the result of shi zai je ya dauke ta tare da Ummi. Misalin sha biyu Ameer ya bar office ba dan ba shi da aikin ba, sai dan yana son ya cikawa Waira alkawarin da ya daukar mata, almost three days to four be je office ba sai dai kasancewar ya tashi da dan kuzari kuma da marmarin office din domin a yanzu takure yake yana bukatar abun da zai saka shi mantar da shi damuwarsa. Daga office din ya dauki hanyar makarantarsu, sai gashi ya tararda abun da ya fi tsana wato traffic, ko kadan baya son tsayawar da motoci suke, ba dan akwai motoci a gabansa ba babu wanda sai hana shi jan motarsa yayi gaba, ko da kuwa a kasar da ake cin tarar mutun ne idan ya karya irin wannan dokar balle a Nigeria da yake ganin komai yayi be yi laifi ba. Ana sakin traffic din yaja motarsa ba tare da lura da tsohuwar da ta zo da gudu zata karbi sadaka a gaban wata mota dake gefensa ba, a lokacinta na hanzari ta wuce kamin ya tashi motar yayi daidai da jan motar da yayi sai jin yayi ya bugu abu, da sauri yayi baya sai ya sake jin ya taka abu tsayar da motar yayi ya bude ya fito. Rayuwar Abuja ba ta yi ba wani lokacin, domin ba kowa yake damuwa da abun da ya dame wani ba, ba kowa ne ya tsaya kallon abun da ya faru ba, kowa ta tsabgar gabansa yake, few mutane ne suka iso gurinta mutanen da take bata a tare da su sune a suka fi yawa sai kiran Allah suke ganin yadda ya taka kafarta sai jini take. Taohuwar kuma sai ihu take kana ganinta ka san ta gama fita hayyacinta domin ya taka kafarta sosai a reverse din da yayi baya. Kansa ya shafa ya busar da numfashi. Innalillahi akwai yan'uwanta a nan? Ya tambaya yana kallon mutanen abokan bararta. Aa amman dai na san gidansu Cewar wata tsohuwar, kamin dayar ta ce. Akwai waya a jakar buhunta a dauko a kira iyalin Kamin a kira iyalinta a yanzu dai ina son wani ya bini mu tafi asbiti Wacce ta fisu sauran kurciya ta kamata sai wasu mazan suka rika ta aka ciro kafarta daga karkashin motar, Ameer ya bude bayan motarsa aka saka ta, sannan dayar ta shiga ya rufe motar ana Allah ya sauwake. Da ada ne babu abun da zai saka Ameer tsayawa ba, ba tsohuwa ya kada be ko jajarin da aka haifa fa yau ne ya kade ba zai tsaya ba, kuma babu wanda ya isa yayi masa wani abu. Idan ma wadanda suka san shi ne sai dai aka kara a gidansu Mr Bashir ya dauki nauyin jinyar, wani lokacin kuma idan accident ya faru sai da ya ciro kudi ya watsa ma mutum yayi tafiyarsa. Amman yau shi ne da bude motarsa a saka masa wanda ya kade har jini na bata masa mota. Ban da private hospital din da suke zuwa be san wata asibiti ba dan haka can ya nufa da ita. Kai tsaye aa wuce da ita Emergency bangaren yan hadurra, a waje ya tsaya shi da macen da ta rakota ya karbi wayarta a jakar
Chapter 96 · 0% Book details