← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 165

Sashe 122

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

junanku? Bayan na mutu? When when when? Ta tambayi Ameer ta tambayi Maleek ta tambayi Namra dake dafe da kunci tana hawaye. Kwana nawa ya rage min? Kullum kokarin gada kanku nake amman sai kara bandarewa kuke yi? Ni haka zan gama rayuwa cikin bakincikin yaya? Why? Kuma ace duk saboda mace kuke wannan abun? Ni kadai ce uwa? Ba ku san abun da yake damuna ba, a kullum kara min bakinciki kuke Maleek ya sauke ajiyar zuciya a hankali. I'm sorry Ummi ban yi saboda na bata ranki, abun da Ameer yayi ne ya wuce hankali, please forgive me amman zan tabbatar masa da cewar be isa ya dauke Waira daga gidan nan ba, ko da kuwa hakan na nufin yaki Fita yayi daga falon bayan gama fadar hakan, Namra kuma ta haye sama tana kuka sosai. Mahmood ya watsawa Ameer wani banzan kallo ya fice a fusace. Sai aka bar Ameer a tsaye jiki babu karfi kamar wanda aka sarewa ga i ya kasa motsawa daga inda yake saboda gorin da Namra da Maleek suka masa ta ce. Ummi ta kalleshi a hankali tana hawaye. Are you happy now? Dan farinciki da kowa ya tashi da safen nan ka wargaza shi, ga breakfast dinka can ka ci kafin ka fita Ta zagaye shi ta haye sama, tana shiga dakinta ta dauki wayarta ta kira Ya Maryam domin take kallo a matsayin uwa a yanzu kuma ita ce abokiyar shawararta. Ya Maryam ta numfasa bayan ta gama sauraren Ummi ta soma bata shawarar abun da take ganin zai fi zame mata mafita. Ba zaki iya zabe wa zai aureta a cikin yayanki ba, kuma irin wannan rashin jituwar dake tsakaninsu zai iya haifar da gaba da kiyayya da zata shafi yayansu kuma ta cigaba da bibiyarsu har bayan rayuwarki, ni dai a nawa ganin karki bari kowa ya aureta a cikinsu Ni ma na yi wannan tunanin, kuma abun da ya faru a yau ina yi ma Ameer uzuri, a yadda na fahimta yana da saurin fushin zuciya, kuma a yadda Waira ta fada masa kai tsaye za a kaita waje karatu dole yayi zaton saboda shi ne, na san be kamata yayi magana a tsaye ba, amman.... Ta yi shiru. Ya Maryam ta ce Zahra kina son Ameer da yawa ko ba haka ba? Ko wane a da irin yadda Allah yake dorawa uwa soyayyarsa a zuciyarta, Ya Maryam ina jin kamar na cutar da yaron nan, ina jin kamar rashin kasancewarsa a kusa da ni ne ya haifar duk wani hali da yake ciki, wata kila da yana tare da ni da haka be faru ba, kuma idan ban so Ameer ba waye zai so shi? Mahaifinsa be raye a yanzu, Abiey baya son Ameer ko kadan na lura da haka, a dan lokacin da ya rage min ina son na kyautata masa, ko da shi zai munana min idan bana raye zai yi nadama kuma zai gane na nuna masa soyayya Haka ne, maza da yawa basa son an matansu, kalilan ne suke so, balle kuma Abiey da yake da riko da kasa manta abubuwa, sai hakuri Amman su mata suna son yayan mazanjensu ko? Na rike nasa yayan kamar nawa, hakan be isa ya saka shi son Ameer ba? Rayuwar namiji dabam take da ta mace, haka ma zuciya kuma hakan ba yana nufin baya sonki ba, na fi kowa sanin Abiey na kaunarki Maso uwa ya so andanta Ya Maryam, idan bana raye alaka zata yanke tsakanin yayan Abiey da Ameer Dole ki jajirce ki ga komai ya daidaita tsakaninsu, saboda gaba, kuma ina son na ja hankalinki karki sake yi ma dayansu irin wannan hukuncin na duka a gaban Ameer, idan ma zaki yi to ki kebe kowa dabam Kuma ki saka addu'a a gaba kina rokon Allah ya hada kan yayanki nima zan taya ki, ina nan zuwa satin sama In Shaa Allah Toh Ya Maryam Na gode Allah kawo ki lafiya Daga haka suka yi sallama. Ummi ta aje wayar ta mike tsaye ta shiga bedroom ta wanke fuskarta ta fito gyara daurin dankwalinta sannan ta fice daga dakinta zuwa dakin Waira har lokacin kuka take idonta ya kumbura sosai har wani numfashin take sama_sama saboda kukan da take. Ummi ta karasa cikin dakin ta zauna bakin gadon Waira a yayinda Waira take zaune kasa, this is the first time da ta ji bata son zaman Waira a gidan ba dan ta gundira da ita ba sai dan matsalar da zamanta a gidan zai haifar ga an da take neman hadin kansu. Me yasa kika fadawa Ameer za a kaiki wani gurin karatu? Idan ina bukatar ya sani ni zan fada masa ba ke ba Waira dake zaune kasa ta dago ta kalli Ummi tana jan numfashi kamar zata shide. Shi ya tambaya me yasa nake kuka? Ummi bana son na bar gidan nan please Ya zama dole kuma, domin Ameer da Maleek fada suke a kanki, ni kuma hadin kan yayana nake bukata ba watsewarsu ba, saboda ke yau Maleek yayi ma Ameer gori, saboda ke Ameer ya fadi maganar da bata dace ba akan Abiey, saboda ke Waira hadin kan yaya zai tarwatse, fada suke akanki Saboda me? Ummi ta kasa bata amsa sai ma mikewa da ta yi tsaye ta nufi gurin da take aje uniform ta dauko mata. Tashi ki saka uniform kin yi wanka? Eh na yi wanka Okay ki saka uniform dinki lunch box dinki yana dinning zan yi ma driver magana ya kai Ameer fa? Ya fita daga rayuwarki daga yanzu, ki manta da shafin rayuwarsa, ki goge shi a zuciyarki Waira kallon rashin fahimta kawai take yi ma Ummi har ta fice daga dakin. Da tunanin Waira ta saka uniform din bata damu da yadda fuskarta take da jurwayen hawaye ba ta sauko ta dauki lunch box dinta. Waira zaki iya gane garinku? Ta juyo da sauri ta kalli Ummi dake saukowa. Aa ba zan iya ganewa ba, a ka'ida sarki yace idan na gudu ba zan iya gane hanyar gida? Ummi ta zauna a one of dinning chairs tana kallonta. Me yasa kika gudu? Waira ta sauke kanta kasa wasu hawayen na cika ramen idonta, bata tunanin ta taba fada musu dalilinta na guduwa idan na ta fadawa wani a cikinsu Ameer ko Jabir da ta sakewa da yawa. Wani aka kashe aka ce ni na kasheshi kuma ban aikata ba, kuma idan na kai wasu shekaru za a bani sarautar tsafin garin ni kuma bana so saboda zasu kashe ni ne idan na mutu Ta aje lunch box din ta bude hannun uniform dinta ta nunawa Ummi wani tabo dake hannunta. Gadon mu ne, idan an haihu ake mutuwa, a cikin wannan tabon ina ganin abun da ya faru da mutum a baya, ina iya kashe wani idan ina so, ta ciki na iya gane ciwonki da damuwar da kike boyewa ta Ameer, tun kamin ki fada, ta ciki dazun na ga abun da Abiey yayi magana da ke, da zarar na rumgume mutum zan iya ganin komai ko na san komai Ummi ta mike tsaye tana kallon Waira da mugun mamaki. Kina tsafi kenan? Ban taba yi ba, sun ce sai na girma zan iya saffara komai yadda nake so, a garin mu kowa matsafi ne sai dai wani ya fi wani karfin tsafi, wanda ba dan garin ba baya shiga, rayuwarmu da ta ku akwai banbanci addininmu dabam da na ku, a yanzu na saba da nan dan Allah karki ce zaki maida ni gida Ummi Ummi taja dogon numfashi ta sauke tana Ya sunan garinku? Garuk... A lokacin da na gudu daga garinmu na boya a gurin duwatsu a nan na fara haduwa da Ameer Okay ki je waje na yi magana da direba zai sauke ki school Waira ta durkusa kasa ta kama kafar Ummi. Ba tsafi na yi ma yayanki suke so na ba, ni ma ina sonsu duka, ina kaunarsu dan Allah kar hakan ya saka ki maida ni Garinmu ko ki koreni daga gidanki, kashe ni zasu yi, na san za su bibiyeni a duk lokacin da suka tashi kasheni, amman for now ina son zama da ku please, tsafina ba zai muku komai ba, ba zan cutar da ku ba, idan kuma baki yarda ba, toh ki kira min Sulem zan zauna a gurinsa Tashi Waira tafi direba na jiranki karki yi latti Ta mike tsaye ta share hawayenta ta gyara hannun rigarta ta dauki lunch box dinta ta fice daga falon still tana hawaye. Tana fitowa Maleek ne farkon wanda ta fara cin karo da shi, tsaye a balcony din kamar mai jiranta bata yarda ta kalleshi ba, ta fara sauko a staircase din dake gurin shi kuma ya bita da kallo kamar zai kamota ya cinye. Ta isa gurin motar da direba ya saka ma key ya bude gidan baya yana jiran isowar Waira. Ta shiga gidan baya ta rufe motar, sai ga Maleek ya iso yayi ma direban alama da ya fito daga cikin motar ba musu ya fito Maleek ya shiga yaja motar aka bude musu gate. Suna kama hanya ta gyara madubin gaban motar ta saita fuskar Waira, ita kuma ta ki dagowa sai kuka ke cinta. Waira.. Idan baki ra'ayi ba za a kai ki ko'ina gurin karatu ba, zaki zauna a tare da mu Ta dago ta kalleshi ta cikin madubin yadda idonta ya kumbura yayi ja abun har tsoro ya bashi. Ya Maleek can you do me a favor? Uhm-Hmm Dan Allah ka daina fada da Ameer, shi ma zan masa magana, Ummi ta fada min a yanzu kun yi fada saboda ni, kuma ita tana ganin kamar laifina ne, har na fada mata abun da be kamata ta ji ba, kuma na ga tsoronta da fargabar zama da ni a cikin idonta, ta fara tambaya ina ne garinmu, tace zamana a gidanta ba zai yiyu ba, Ya Maleek bana son komawa garinmu kashe ni za su yi.... Ta shimfida masa irin labarin da ta fada ma Ummi, kuma ta nuna masa hannunta sai hawaye take kamar ba gobe. Tsayar da motar yayi ya faka gefen titi ya dauki tissue ta bude motar ta fito
Chapter 122 · 0% Book details