Sashe 70
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
ka koma yin dabanci ba a san yayan masu arziki da wannan dabi'ar ba Yau na fara, kuma kina yin wasa zan yanka wuyanki ko na fada cikinki kin ga dai ba za ayi min komai ba ko? Idan na kashe ki an kashe banza dan haka ki bini a hankali Toh... Yanzu gida zaka kai ni? Saboda gani direban ki ba Amman Wallahi tallahi na rantse da Allah ni ban taba iskanci ba, dan Allah karka lalata min rayuwa Ameer Ni na taba iskancin, negative mind daman shi ne a ranki, you should be praised kin shiga motata ma ni me zan yi a jikinki? To miyasa zaka dauke ni a motar kana ta tafiya me zaka yi min? Dan Allah karka yi tsafi da ni toh Dodona baya son irin jininki Cikin dabara ta kai hannu ta murda gambun motar da zimmar ta bude sai ta ji shi a rufe. Na shiga uku na lalace Ta fara kuka, hankalinta ya tashi sosai domin bata san manufar Ameer na yi mata haka ba, kai ta zai yi wani gurin ya aje ko ya hukuntata akan abun da ta yi ko kuma wani abun zai mata. Ni zan iya baka hakuri a bainar jama'a idan dan abun da na yi maka ne, zai saka ka hukunta ni, dan Allah dan darajar iyayenka ka yi hakuri Kallonta kawai yayi ya dauke kai, yadda ta makure a cikin motar ta zama marainiyar gaske duk sanyin ac motar ita gumi take ga idonta ya zurma kamar zuru. Faka motarsa yayi gefe ya bude ya fita rike da wukar da kuma wayarsa da key motar da Daddy ke kira. Yana piciking kiran Daddy ya tambaye shi. Kana ina Ameer Ya juya kalli inda yake. Wani guri Daddy? An fada min ka shiga har gurin da ake dafa abinci ka dauki wuka, me zaka yi da ita? Wani zare na yanke a jikin tayar motata Ameer ba ka min karya karka fara, ni nasan ko me zai faru ba zaka yanke zare a jikin motarka ba Yayi dariya. Daddy maganar gaskiya wata yarinya na yi ma barazana da ita Subhanallahi barazana da makami Ameer? Kar zuciya ta dauke ka ka aikata kuskure, ka zo ka same ni gida yanzu nan, sai mu ji idan akwai matakin dauka kamata a adauka akan yarinyar kuma na ji abun da ta yi maka Ba wata babbar matsala ba ce Daddy karka damu Na ce ka zo mu tattauna, kuma karka tana yar mutane Ameer dan Allah Okay Daddy gani nan zuwa Ya sauke wayar ya nufi motar ya cire key ya shiga ya zauna, tun da suka kama hanya suna tafiya bata ce masa uffan ba sai share hawaye take gabanta na zillo tana ta tunanin inda zai kaita zuciyarta sai sake sake take mata. Tafiya mai nisa suka yi sannan ya shigo umguwar manyan mutane ya fama gaban wani katon gida da gate din gidan ma ya isa bakauye kallo. Wani karamin littafi ya dauko ya fara rubutu, yana yi tana leko har ya gama ya nade takardar ya mika mata sannan ya bude gurin daya aje wayar Nimra ya dauko ya mika mata. Shiga gidan nan ki kai wannan wayar tare da takardar nan, amman idan kin shiga ki ce ke kawar Nimra ce kin zo ganinta, sai idan kun kebe zaki bata Wallahi ba wata Nimra yanke min kai za'ayi wannan katon gidan na yan mafiya ne Kwarai kin san mahaifina kudin tsafi yake da su Ta lake kafada tana kuka. Ni ba zan shiga ba, Allah ya fika Ke look babu abun da za'ayi da katon kan nan naki, yarinyar da kika rika zagina kwanakin baya saboda ita, to gidansu nan, so nake ki shiga ciki ki kai mata wayar nan da wannan takardar, daga nan sai ki duba lafiyarta daman na ga kin damu da ita ai Idan aka kashe ni hakkina yana kanka Idan baki shiga ba, zan saka wukar nan na yanka ki, ko kuma na dauke ki na kaiwa abokaina su yi miki wulakanci son raina, dan haka ki zabi Ameer me yasa kake mugu ne? Kana ta daukar hakkin mutane da basu maka komai ba Toh bari na zabar miki a cikin ukun Zan tafi, ka bude min motar Idan na bude miki motar kuma ki gudu, na biki da wukar nan ko kuma na aika har gidanku a daukoki ai kin san dai na san gidanku ko? Ta daga kai, ta zabi shiga ne saboda shi ne mai sauki a cikin hukuncin abubuwan uku da ya shar'anta mata ta zaba, ta san ko da masu fille kai ne zata musu addu'a, idan kuma abun da ya fada ne a ciki idan ta aikata ga huta. Ta karbi wayar da takardar ta saka a jakarta sannan ya bude motar ya fita ya zagaya bangarenta ya bude mata ta fito. Kina yin wani abu kin san sauran Me yasa kai ba zaka shiga da kanka ka bata ba, idan har da gaske gurinta ka zo Ki kwankwasa kofa a bude miki Ya koma cikin motarsa ya zauna yana kallonta tana kallonsa, yana ganin ta matsa jikin gate din ya danna mata horn ta koma. Cikin tsoro ta kai hannu ta kwankwasa kofar gidan dake rufe sai da ta yi haka sau uku sannan aka bude kofar ganin mutumen daya fito yana sanye da uniform din police ya saka ta dan ji sanyi a ranta, ta juya ta kalli motar Ameer yayi reverse da ita zat tafi ya barta a gurin. Na zo gurin Nimara ne Ta fadi sunan a birkice tsabar tsoro da rashin rike sunan da ta yi. Ke wacece? Kawarta ce Police din ya kalleta kasa da sama, shi dai be san yaran gidan na da kawayen da basa da motoci ba, yanayin mu'alamarsu ya saka ba kasafai suke zuwa gidan kawaye ko kawaye su zo nemansu ba, idan ma sun zo suka zo da manyan motoci ne, sai dai Humarai a kasa ta zo duk kuwa da ya hango motar da ke kokarin juyawa wacce yake kyautata zaton a ciki aka kawota. Kun yi da ita zaki zo? Eh ga ma wayarta a hannuna tace na zo mata da shi Ta saka hannu a jaka ta dauko wayar tana nuna masa. Toh jira a nan ina zuwa, wa a ce mata? Ka ce... Ka ce... Ka ce.. Aisha Humaira ce Ameer Aisha Humaira Ameer? Ya maimaita sunan sai ta daga masa shi. Yeah Okay shigo sai ki jira nan Ya matsa jikin kofar ya samu shiga sai ya rufe gate din ita kuma ta tsaya kusa da inda ya nuna mata jikinta na rawa gabanta na faduwa. Kamin yau idan wani ya zo yace yana son ganin masu gidan kai tsaye masu gadin suke ba shi damar ya shiga domin haka Ummi tace musu, sai dai Umarnin da Abiey ya bada na cewar kar a sake Nimra ta fita gidan ya aaka suka tsaurara tsoro gudun kar wani abun ya faru a dora laifin a kansu. *Littafin WANI GARI na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660* MALEEK POV. Yana shiga dakinsa ya shiga closet dinsa ya aje jakar ya fito ya sauko downstairs ya zauna a dayan side din da kujeru suke, sosai ya maida hankalinsa gurin plasma dake kunne yana kallon film da MBC 2 suke hakawa. Sai da suka tafi talla tukuna hankalinsa ya kai gurin wayarsa dake kan ayan set din kujerun tana ringing da hanzari ya isa gurin ya dauki wayar tare da amsa kiran da ya biyo bayan miss calls din dake bayyana a saman kiran. Maleek kana ina? Ina cikin gida, bana kusa da wayar ne Ka same ni bangarena zamu gaisa da mijin Namra, na kusa karasowa Okay Kuma ban ce ka zo min da kananan kaya ba Yayi murmushi kawai ya sauke wayar yana kallon kansa domin kananan kayan ne a jikinsa. Haurawa yayi sama ya canja tufafin jikinsa zuwa shadda ash color ya fesa turare ya saka kular Zanna bukar yar ubansu, ya canja talkamin kafarsa ya saka wandanda za su dace da shaddar jikinsa be damu da duba madubi ba domin ba yin kyau ko akasin haka ne a gabansa ba burinsa yayi shigar mutunci kamar yadda mahaifinsa ya bukata, be fice dakin ba sai da ya murza wani karamin turare a hannunta ya shafe hannunsa zuwa wuyansa, ya dauki wayarsa ya saka aljihu sannan ya sauko stairs din yana wani irin kamshi na tashin hankali kamar shi ne angon. Kofar fita falon ya nufa tana tafiya kamar mai tausayin kasa. Entrance din bangaren Ummi ya tsaya yana kallon gate din gidansu, a hankali ya juyo yana kallon motar Shuraim sai ba motar yake kallo kai tsaye ba, kyakkyawar halittar Allah mai matukar burgewa da daukar hankali yake kallo, Waira ce tsaye jikin motar can side din da ace bata mike tsaye ba ba zai iya sanin tana gurin ba, ita ma bata mike tsaye dan sanin cewar shi ne tsaye a gurin ba, sai dan kamshin turaren da ya kaiwa hancinta hari ta kasa jurewa har ta leko a zatonta zata ga Sulem dinta ne sai ta yi arba da abokin fadanta. Yayi kyau, kyau da ake kira da kyau irin kyaun dake fitar da asalin kyau da siffar kyau a jikin namijin, da haramun ne ka yi masa kallo daya ka dauke ido. Hular kansa ta zauna das kamar sai da aka sauna kalar zaren da girman aka zaka masa domin shi kadai kawai. Shaddar ta haska fatarsa ta kara masa kwarjini da cikar izza irin ta jinin sarauta, daga ita har shi sun dauki lokaci suna kallo junansu, ko wane na tantance kyaun dayan jinsinsa. Waira ce ta fara sulalewa kasa ta zauna tana rike da zomonta, a lokacin da idonshi suka daina ganin kyakkyawar fuskarta sai hayyacinsa ya dawo jikinsa ya dauke kai ya sake maidawa gurin gate din yana hade yawun bakinsa da suka tsinke... Me kike yi a nan wa kike jira, duk baya bukatar amsarsu, yadda aka yi ta fito daga cikin falon ta zauna a gurin ne abun tambaya a gurinsa, jira ko me