← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 165

Sashe 24

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

Copyright 2023 ...WANI GARI... Khadeeja Candy_ Wani sabon tunanin ne ya zo masa hakan ya saka shi canja shawara, gefen hanya ya rika bi har ya samu wani Karamin shagon siyar da kaya, wani almajiri ya samu ya aika shi kiran mai shagon kasancewar akwai glass sai an bude za a shiga, ba shigar ce matsala ba rashin talkami da kuma rigar jikinsa ce matsala domin baya son ayi masa kallon mahaukaci. Almajirin na isa sai gaai shagon ya fito ya biyo bayansa. Tun kan ya isa Ameer ke masa kallon kasa da sama. Riga nake so wacce ta fi ko wace tsada, sai talkami idan kuna da su Shi ne abun da ya fada ya mika masa Atm din hannunsa tare da fada masa code. Akwai amman ba mu da machine din cire kudin, sai dai makocina shi kuma sai ya cire carjin dinshi Ba matsala Ya fada ba tare da ya kalleshi ba, domin mutane kazanta suke ba shi a yanzu, Waira ma dake bayan motar jin yake kamar tana saman jikinta ne, kazantar dake jikinta ta lake masa a zuciya ya kasa manta abun da ya gani. Yana ji yana gani ya bata minti talatin a gurin kamin mutumen dake shakar Ameer ya kawo masa rigar da talkamin, domin jikinsa na bashi ba Ameer ba mutumen kwarai ba ne ganin sabuwar mota da aka buge gabanta gashi babu riga a jikinsa kuma babu talkami hakan na nuna sato motar yayi ko kuma wani abun dabam. Kallo daya Ameer yayi ma rigar da talkamin ya san ba ajinsa ba ne, sai dai babu yadda zai yi dole ya saka a haka, sai da yayi tsaki sannan ya karba tare da ATM din, a gaban mutumen ya saka rigar sannan ya ja motar yayi gaba, tafiya mai nisa yayi sannan ya saka talkamin ya faka motar gafen titi ya fita zuwa gurin wani mai shagon POS ya mika masa ATM din. 300k nake so Ranka ya dade ba za su samu ba, sai zuwa anjima sai dai 100+ idan kana so Ba ni Mutumen ya fara aikin saka ATM din, dayan dake taya shi aiki kuma ya fara karga kudin, fuska babu annuri Ameer ke fada musu pin din, in less than 20min aka ciro kudin aka bashi ya karba, be damu da saka su aljihu ba ya riko su a hannu domin sun masa kazanta kasancewarsu tsofin kudi wasu ma sun yage sa'arsa daya sun saka masa su a leda. Bude motar yayi ya shiga ya dauki hanyar Kano sai da ya kusa isa gurin da police ke bada Hannu sai ya samu guri gefen titi ya faka motar inda ba za su hango shi ba, ya fita ya zagaya bayan motar da ya bude ya saka hannunsa ya warware nadin da yayi mata da carpet fuskarta ta fito, hakan nan ya samu kansa da tsaya yana kallon yadda hawaye suka bushe a fuskarta ga gashin kanta ya kara yamutsewa, abun ka da marar juriya sai amai ya sake cika masa baki da sauri yaja baya ya fara kwara amam dake fitowa daker domin babu komai a cikinsa sai yunwa, ya amayar da dan abun da ya ci jiya, gashi yau be saka komai a cikinsa ba. Cikin motar ya koma ya dauko gorar ruwa ya wanke bakinsa da fuskarsa, after that ya tuna ya taba abubuwa da yawa da be kamata hannunsa ya kai a fuskarsa ba tare da ya wanke ba. Ohhhhhh Ya furta yana jin wani irin bakin ciki, a sake ya bar motar kamar yadda ya bar bayan motar ma a bude, ya dauki kudin dake ledar ya bar ATM din da komai a ciki, ya fito daga gurin zuwa gurin babban titi tafiya yayi mai nisa a kafa sannan ya tsallaka dayan side din da zai maida shi cikin KT yana tafiya yana taron mota har ya samu wanda bata da mutane da yawa ta tsaya, one after the other ya rika bin mutun biyu da suke bayan motar da kallo kamin ya kalli direba da yake ganin idan ya shiga motar kamin su isa KT ma mutuwa zai yi, domin irin motar nan ce da bata da Ac glass din motar ma a harfice yake balle kuma mutanen ciki. Ku tafi kawai Bayan ya gama bata musu lokaci, be tsaya jin abin da za su fada ba yayi gaba abunsa, can kuma ya sake taron wata motar, yayi haka ya kai sau biyar sannan ya samu wanda mutun biyu ne kawai a gaban motar bayan babu kowa, sai dai ita ma bata da Ac kuma motar kasuwace irin mai rawa din nan idan ana tukawa, hakan na dai ya daure ya shiga yana jin wani zazzabin wahala na taso masa, tasha ya fada masa za su kai shi he can pay ko bawa suke so shi dai bukatarsa ya ganshi a tasha. Kamar yadda ya bukata haka suka kai shi har cikin tashar KT suka ce zai ba su 3k saboda lura da suka yi da alamar yana da su, ba musu ya bude ledar ya cire kudin da za su fi haka ya mika musu, sannan ya saka ragowar kudin aljihun wandonsa guda biyu ya bude motar ya fita. What if wanda ya san shi ya ganshi a nan? Wannan ai zai zame masa abun kaskanci Shi ne abun da ya fara zuwa masa a rai, hakan ya saka shi nufar wani mai tereda dake siyar da facing cap ya siya ya saka ya siya bakin glass ya saka ya rufe idonsa. Sannan ya nufi gurin da yan union suke da su ya fara magana ya fada musu shatar mota mai kyau zuwa Kano, ya fadi inda za'a kai shi bayan yayi musu karyar motarsa ta lalace kuma tafiyar gaggawa ta kama shi, tun da yake a rayuwarsa be taba sanin haka tasha take a yamutse da mutane ga hayaniyar da yake ganin da ace shi da tuni ya kurmance, duk wani information na shi sai da suka karba sannan suka hada shi da direban da zai kaishi Kano, ba laifi ya samu mota mai dan kyau domin tsab take matsalar kawai bata da Ac, ba su bar gurin ba sai da ya siye lemu cake tare da ruwa da dan biscuits sannan suka kama hanya, direban ya tsaya ya sha mai a gidan mai dake hanyar fita KT sannan suka kama hanya. Kamin su isa Kano Ameer yayi amai ya kai sau hudu saboda warin man motar da yake ciki yana damunsa. Kwanta yayi jikin motar yayi relaxing yana tunanin mahaifinsa, wannan kadai ya isa ya fahimci cewar mahaifinsa yayi masa gata, domin be san duk wannan wahalar ba, idan zai yi tafiya kamin time din tafiyar yayi an shirya masa komai, sannan jirgi yake hawa ba mota ba, sai idan zai isa Airport ko kuma daga Airport zuwa gida ne kawai yake hawan mota sai kuma yawon cikin gari, motar ma sai wanda ta amsa sunan motar da ba kowa ya isa ya hau ba, ya kwanta a gado mai kyau gida mai kyau tufafi baya saka mai karamin kudi, kudin Naija ma idan ba ganin dama ba ba zai rike ba sai Dollars kuma babu mai ce masa dan me? Wani lokacin ma a private jet ma za a kai shi inda yake so na mahaifinsa , tun da yake a rayuwarsa be taba hawa motar haya zuwa wani gurin ba sai a yau. Sai a yanzu yake jin be kamata ya bijirewa umarnin mahaifinsa ba, mi zai saka yayi haka? Why? Gashi makiyinsa ya samu yadda yake so bayan raba shi da abokansa, ya busar da iskar bakinsa ya dago kadan yana kallon hanya sosai yake son yin bachi amman ya kasa saboda babu ac a motar kuma iskar dake shigowa ta gilashin motar yayi masa yawa, abu ne da be saba da saba da shi ba. Haka dai ya daure har suka isa kano. GRA suka shiga direban be sauke shi ko'ina ba sai cikin gidan Hajiya Jamila. Yana fitowa motar ya ciro kudin aljihunsa gaba daya ya mikawa direban. Ka kara da wannan A firgice direban ya fito daga cikin motar gaba daya ya zagayo inda Ameer yake tsaye ya fadi kasa ya rike kafafuwansa yana masa godiya har da hawayensa, shi kansa Ameer ba zai fadi ko nawa ne kudin ba, balle kuma wanda aka bawa kyautar domin babu wanda ya kirga a cikinsu, sai dai ganin yan 1k da yawa ya san kudi ne mai yawa. Ba wani kudi ba ne fa Ameer ya fada domin ba ga wani abun godiya da mutumen zai masa ba, akan abun da be taka kara ba balle har ya karya. A gurinka ba komai ba ne ranka ya dade, amman ni a gurina kudi ne mai yawa, da tsoro na kawo ka Kano ashe ban sani ba rabo ke kirana, motar nan ba tawa ba ce amman ka ga abun da Allah yayi min Ameer ya dan ji wani irin for the first time domin yau ne karo na farko da yayi sadaka, not just sadaka wannan ne karo na farko da yayi ma wani abun kirki kuma har aka masa godiya, this is the first time da ya kyautataw wani. Tabe baki kawai yayi ya nufi cikin gidan da harabarsa ma ta ishe talaka da wani bakauye kallo domin kana ganin gidan ka san Ameer ya isa har ya wuce, a tunanin direban gidansu Ameer ne, shi kuma ya zabi zuwa Kano ne saboda ba zai iya jure tafiya a Abuja a motar haya da babu ac ba, kudin dake aljihunsa ma ya bashi kyautar su ne saboda baya jin zai sake taba kudi mai datti again, daman ya matsu su fita aljihunsa sai yake jin kamar tsukarsa suke. This is the second reason da yake son zuwa gurin Hajiya Jamila kullum kofar falonta a bude take not like gidansu da sai danna ko ka yi knocking za a bude maka, talkaminsa ne abun da ya fara cirewa sannan ya shiga falon. Hajiya Jamila dake zaune kam carpet rike da carbi ta dago ta idonta dake sanye da gilashi ta kalleshi, a take annashuwa da farinciki suka wanke zuciyarta har suka kasa boyuwa sai da
Chapter 24 · 0% Book details