← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 165

Sashe 135

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuma ba zai raka ni ba... Kallonta yake yana kokarin fahimtarta, tunanin sai ya zame masa biyu, bayan ganin da yayi ma Ameer yana kallon Nuwaira da kuma bugun motar da yayi and now ita tama kuka take. Do you miss him? I don't know Ta fada cikin kuka sannan ta mike tsaye ta nufi stairs still tana kuka, bin ta yayi da kallo har ta shige sannan ya mike tsaye ya nufi dinning, Coffee ya hada ya zauna a gurin yana sipping Coffee a hankali his mind is somewhere else sai tunani yake yi. The following Day da wuri kowa ya shirya, Ummi ta cika ma Nuwaira bayan motar da zasu tafi da kaya bayan kayanta da suke gidan, ta bata wasu ga kuma wasu da ta samu a gurin Daddyn da Namra, chocolate da biscuits ma kala kala Ummi ta yi mata bag dinsu dabam kuma ta girka mata abun da zata iya ci, ta hada mata tea a madaidaicin flask ta dafa mata eggs. Bayan an saka komai police din da za su zakasu suka iso, Nuwaira ta fito tana kuka domin bata son barin gidan saboda sabon da ta yi, kusan kowa na gidan ya zame mata kamar dan'uwa, su suka cike mata gurbin abubuwan da ta rasa suka dandana mata dadin duniya suka cireta daga kuncin da kazanta da cutar da take ciki. Jerawa suka yi a balcony din har Abiey da Namra Mahmood da Ummi, Abiey da Mahmood ne kawai ba su yi kuka ba, Ummi kam ba a magana daman ita gwanar kuka ce, Namra ma da ba komai ke saka ta kuka ba sai da ta yi hawaye, saboda kukan da Nuwaira take, one after the other ta bisu da kallo dukansu sun jera babu Ameer, a lokacin ne ta gane cewar shi ma ya zama wani bangare na rayuwarta domin rashin ganinsa a cikin mutanen da take kallo a matsayin danginta. Ta takowa ta rika hannun Ummi ta saka a fuskarta Ummi na gode, kin zama uwata ban san dadi uwa ba sai akanki ban san miye dangi da yan'uwa ba sai da na hadu da ke, kin haska zuciyata kin zama sanadiyar yayewar kuncina, sanadinki nake iya magana da yaren da ba nawa ba, na san abubuwa da yawa ta dalilinki kin min gata da ban isa na biyaki ba kuma ba zan iya biyanki ba Ummi tana son ta yi mata magana ta fada mata abubuwa kuma ta yi mata godiyar da ta zama silar samun kan Ameer amman ta saka saboda kuka. Allah ya baki lafiya, Abiey na gode, Anty Namra Thank you Ta kalli Mahmood sai yayi mata dariya ita ma dariyar ta yi cikin kuka, kamin ta kalli Abiey dake tambayar ina Ameer. Ina Ameer? Tun jiya yayi mata bankwana maybe ba zai iya ganin tafiyarta ba ne Maleek ya bashi amsa, yana bude motar ya shiga baya. Ummi ta ji tausayin anta Ameer, Abiey ya daga masu hannu sannan ya juya ya shige ciki. Maleek yaja motar police daya yana bayan motar, Nuwaira kuma tana can seat din baya na karshe zaune ita kadai. Maleek na ja motar suka fita daga gidan ta ji kamar an cire mata rayuwa sai kuka. Har suka fita daga Abuja bata daina kuka ba, sai ka rantse gidan iyayenta ne zata bari a kaita wani gurin dabam. It takw them 8hours kamin su isa Kt from Abuja, saboda yanayin tafiya da kuma dab tsawar da suka yi. Hotel suka yi kama police din dakinsu dabam separately, Maleek ma dakinsa dabam Nuwaira ma aka kama mata dakin, sai dai ta kasa natsuwa tun da suka iso har sai da Dr Shuraim ya iso gurin, Maleek be yarda ya bar su sun kebe dabam ba, ya kira Nuwaira ta fito reception din ta hadu da Dr Shuraim, ganin Maleek ne kadai ya hana ta rumgumar Dr Shuraim domin ta yi marmarinsa ba kadan ba, and shi ma yayi marmarinta ba kadan ba, kamin ya fara bata labari ita ta fara bashi and all of her story abun da ya faru tsakaninta da Ameer ne, a yanzu da baya kusa da ita take marmarin take missing dinsa and the saddest part is be rakota ba da zata zo. Saurayinki ne shi Ameer din? Ta yi jimmmm for tunani kaminnta girgiza masa kai da sauri. Aa shi ma kamar kai yake Can kuma ta dan turo baki. Ya dan fika so na kadan Dr Shuraim yayi murmushi. Waya fada miki? Yanzu dai gidanmu zamu tafi ki kwana a can kamin gobe sai na rakaki mu tafi tare ko? Ta dan leki Maleek dake zaune gefe yana ta danna wayarsa, sai dai hankalinsa yana kan su not gurin wayar da yake dannawa kawai yana pretending ne. Ba zai bari ba Dr Shuraim ya juya ya kalli Maleek ya kalleta. Saboda me? Ko da na lura yana azabtar da ke ko? Shiyasa kike son Ameer din da ban sani ba, na lura da hakan Ya daina yanzu, baya min komai Hmmm gashi ya tsare mu a nan, bari na masa magana Dr Shuraim ya juya ya kalli Maleek ya zai yi magana Maleek ya dago kai ya mikawa Nuwaira waya. Gashi Ameer ya kira za ku gaisa Cikin wani irin murna da farinciki marar misaltuwa Nuwaira ta karbi wayar ta mike tsaye ganin video call ne ta fice faga gurin. A nan Maleek ya mike tsaye ya kalli Dr Shuraim ya ce. Ba zata bi ka ba, zata zauna a nan ne har zuwa goben da zamu tafi that's the rule zaka iya tafiya idan ka gama Yana fadar hakan ya nufi hanyar shiga cikin hotel din ya bar shi a gurin tsaye da mamaki, a yanzu Dr Shuraim ya kara yabawa da rashin kyaun halin Maleek da kuma rashin mutuncinsa. Allah kadai ya saka Dr Shuraim tsayawa a gurin tsayawa a gurin shi ma dan kar Nuwaira ta dawo bata tararda da shi ba ta ji babu dadi, rakiyar da yayi niyar yi musu ma fasawa yayi domin ya fahimci ba jutuwa za su yi da Maleek ba. Harabar Hotel din ta fita gaba daya, tana gaisawa da Ameer a video. So ya kike? Ba lafiya kalau ba i miss you me yasa baka zo? Gashi idan na tafi garinmu babu wanda zan sakw gani, kuma babu waya Zan saka Maleek ya baki waya zaki karba? A garin mu ba za a yarda ba, ba au yarda da irin wadannan abubuwan ba Shikenan zamu yi bankwana daga yanzu kenan? Ba zaka kira ni anjima da kuma gobe da safe ba kuma da dare? If Maleek ya yarda Zai yarda zan masa magana, bari na kai wayar gurin Sulem ku gaisa Sunan Shuraim kawai da ta ambata sai da ya ji gabansa ya fadi, ba dan kar ranta ya bace ba da ba zai gaisa da shi ba. Sai dai ba zai iya gudun abun da ta bukata ba domin ba zai jure gani bacin ranta ba. Okay bari na ga mutumen da ya sace zuciyar Waira I'm Nuwaira now no more Waira Ta gyara masa Yeah that's right Nuwaira nice name i like it Ta yi dariya, sannan ta isa ta mikawa Shuraim wayar. Sulem gashi zaka ga Ameer din gashi nan zaku ce ina wuni wa juna Shuraim ya karba yana murmushi. Hello I'm Dr Shuraim i guess you didn't know me amman Maleek ya san ni, because Namra ta yi introducing dina gurinsu As her boyfriend? Yeah as her fiance i think Sai duk suka yi dariya Ameer ya dan ji sanyi a dansa jin cewar Shuraim yana da wadda yake so. Nuwaira tana yawan ba ni labarinka, I'm the first person da na tsinke mata zoben daka bata abun da tunani ya bani kai saurayinta ne so I'm little bit jealous Shuraim yayi dariya. I'm her besty ina tunanin, domin nine mutumen farko da ta fara haduwa da shi bahaushe kuma ta jidadin haduwar da shi, you don't have to be jealous bana cikin game dinki, and ta min complain cewar baka rakota ba why? Ameer ya dan yi shiru. Bana son ban kwana ne that's i hate good bye, and tace ta tsane ne Ta yi saurin amsawa cike da shagwabar da bata san tana yi ba. Aa ban ce na tsane ka ba i didn't say that Ameer yayi murmushi ya ce Ki kaiwa Maleek wayar zan yi magana da shi Sannan yayi sallama da su ya sauka. Shuraim ya kalleta yana reading mind da face dinta Me yasa kika tsane ne? Ban ce haka ba fa, kawai dai bana son halinshi ne sometimes kuma yana batawa Ya Maleek ni kuma bana son a bata masa Saboda shi kike so? Ta yi kamar bata ji ba. So you love Maleek yaron da bashi da kirki yanzu nan ya gama fada min maganar banza ya tafi, bayan kuma ya san yar'uwarsa nake so at least na cancanci mutuntatawa a gurinsa ko yaya ne, kuma saboda shi ba zan rake ki garinku ba gobe kuma ba zai bari ki tafi gidan mu ba, daman na fada mikin wannan yaron takura miki yake baki yarda ba A take ta ji ranta ya bace, akan me wani zai batawa Shuraim dinta rai, bacin ran ma kuma akanta. Ya mike tsaye ya dauko ledar dake gefensa ya aje mata a gabanta. Ga tsarabata nan, zan tafi. Wata rana zaki gan ni a garinku idan sun yarda ko da yake ban san ya zan fara neman baki ba. A nan wani sabon hira ya kaure a tsakaninsu, ta fara fada masa rules and regulations na garinsu da kuma matsalolin da take tunanin zata fuskanta idan ta koma har sai da ta bawa Shuraim tausayi. Me zai saka ba zaki zauna a nan ba? Kirana suke yi dole sai na tafi No wannan abu ne da zaki saka rayuwarki a hatsari baki bukatar yin haka Garinmu ne dole na tafi Ya kai hannunsa ya shafa kanta. I Wish zan iya yin wani abu, Allah ya sauya tunaninsu kuma tsareki Ameen Ta sauke kanta kasa hawaye na mata zuba sannan ta dauki ledodin da wayar Maleek ta yi tsaye tana kallon Dr Shuraim har ya fice. AMEER
Chapter 135 · 0% Book details