← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 165

Sashe 46

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

da haurowar Nimra da Hanne. Karbarta yayi a hannun Ummi tana kiran sunanta. Waira... Waira... Ta kalleshi daman hankalinta be gushe ba, tsorata kawai ta yi sai kuma hawayen jinin dake fitar mata a ido. Mi ya same? Ummi ta fada masa iya abun da ya faru da kuma abun da take tunanin ko Waira ta ga wani abun ne, Mahmood ya sake ta, ya shiga dakin yana dubawa da dan tsoro ko zai ga wani abu be ga komai ba. Dan Allah Hanne da Nimra a saka mata kaya zan je na shirya na kaita asibiti yanzu nan Ummi na rufe baki Maleek ya iso gurin cikin wani irin zafin rai da shi kansa ba zai ce ga daga inda yake zuwa masa ba. Be tambaye miya faru ba sai kallon kofar dakinsa dake bude yayi yana kokarin fahimtar abun da ke faruwa, Waira na ganinshi ta yi saurin tashi ta rike Ummi. Daki ta shigar min? Ni ta zo nema Idan ta sake shigar min daki sai ta bar gidan nan, and idan na sake ganinta tsaye a gabana sai na mata dukan da sai ta kusa mutuwa...! Magana yake cikin wani irin zafin rai kamar ba shi ba har hade hade hakora yake yana nuna ta da yatsa. Ummi ta tura masa Waira da karfi. Gata nan ka kasheta Maleek, idan ka gama da ita ka kashe ni ka kashe kanenka gasu nan Waira ta juyo da gudu ta dawo gurin Ummi ta riketa, ba dan ta fahimci abun da Ummi take fada ba sai dan turata da Ummi ta yi a gurin Maleek kuma bata manta shi ne ya mareta ba. Are you a gay? Me mata kuka maka? Ba mace ta haife ka ba? A cikina ka zauna Maleek for more than nine months na haife ka na raine ka na ci kashinka da fitsarinka har ka yi wayo ka girma, sai a yanzu zaka ce ka tsani mace, ka tararda yarinya tana zubar da jini baka damu ba sai zancen dukanta kake yi ka kashe ta Maleek sai na san ka haihu, idan ba zaka iya zama da mu ba ka tattara komai na ka bar gidan nan, ai ka yi dukiya ka yi hankali ka gi wayon da zaka iya zama kai kadai a gidanka then move out, ka bar ni ni da yayana mu sakata mu wala, i can live without you Maleek tun da na rayu babu dan'uwanka... Ka je ka rayu da mazan da kake so na yafe ka, na gaji da wulakancinka... Wani irin fada Ummi take masa ko'ina ana jin muryarta idonta har ya kade yayi ja sosai, su kansu ba su taba ganin bacin rai da fadanta kamar haka ba, ta fisge hannu Waira da karfi ta nufi dakinta da ita. Nimra da Namra suka bi bayan Ummi Mahmood ma ya rufa musu baya, aka bar Maleek shi kadai a tsaye, Hanne ma sauka ta yi da sauri kasa. Daker Maleek ya cira kafadarsa ya shiga dakinsa ya maida kofar dakin ya rufe ya jingina da kofar ya rumtse ido sai hawaye suka sauko masa ta gefen ko wane ido, ya jinke hannayensa sosai. Ya dauki lokaci a haka sannan ya bude idom ya nufi inda keys dinsa suke ya dauka ya fice daga gidan gaba daya. Mahmood na shiga dakin, Ummi ta dakatar da su daga yi mata wata magana da ta dangancin Maleek. Kar wani yayi min wata magana akan Maleek, and i meant it, enough is enough na gaji kowa ya tafi gurin sha'aninsa, Mahmood je ka shirya mu kai yarinyar nan Asibiti, Namra wuce ki tafi gurin aikinki, and you Nimra ki sama mata tufafin da zata saka zan shiga na yi wanka Haka ta rabawa kowa aiki sannan ta shiga bandakin, kamar yadda ta umarta haka kowa yayi, ba ma kamar Mahmood da ya san condition dinta shi ya tsoron tashin hankalinta fiye da komai. A falo ya fito ya zauna yana jiran saukowarsu, Namra tuni ta wuce gurin aikinta Nimra kuma ta taimakawa Waira ta saka wando da riga domin su ne kadai suka yi mata a cikin tufafinta shi ma wandon dan yana gajere ne sai ya saukowa Waira saboda tsayinta be kai na Nimra ba. Ummi ta fito da shirinta suka wuce tare Mahmood da be samu tsayawa ya karya ba a ranar, daman Abiey tuni ya fice daga gidan bayan sun yi sallama da Maleek da ya dawo bangaren Ummi a dazun da abubuwa marar dadi suka faru. Sai ya rage Nimra ce kadai a gidan, hakan ya bata damar shiga bangaren Abiey ta shiga har dakinsa tana bincike inda yaks aje abubuwansa ta har ta samu sa'ar gano inda keys din motar ta yake ta dauko ta fito waje ta bude motar tana duba ko'ina. Har da addu'a take Allah ya sa ta sarewar saboda ta farantawa Ameer rai, can kasan kujera ta hango abu mai kamar akwaiti da sauri ta dauka tana budewa sai ta yi arba da abun da ba dan ta ganta a hannunsa yana busa ba da ba zata iya kiransa da sarewa kai tsaye ba, saboda ya sabon samfur ne. Da sauri ta fito motar ta rufe ta maida key din inda ta dauko shi ta dawo dakinta ta dauki hoton sarewar ta turawa Ameer sannan ta boye box din a karkashin gadonta. AMEER POV. Ya aje wayar yana murmushi ya cigaba da saka maballan rigarsa. Good Girl yanzu sai zancen haduwa zan yi wannan wasan da kyau After ya gama sakawa ya sake daukar wayar ya mayar mata da amsa. Idan ba zaki iya zuwa can ba, then mu hadu a Galadimawa inda muka taba zuwa it's a safe place babu wanda zai gan ki kuma yanzu nan zan tafi sai kin iso Tana gama rubuta mata amsar ya kashe data shi ya saka wayar aljihu ya dau ki abubuwa da ya san zai bukata ya fice daga dakin. Sai da ya zabi motar da ta yi masa sannan ya saka kanwarsa ta dauko nasa key motar a bangaren mahaifinsa ya karba ya hau ya kama hanyar Galadimawa. Ya isa in time saboda yayi abun da ya saba wato gudu da mota, ya ki ya kunna data shi balle ya ga abun da Nimra zata fada masa so yake ya cilasta ta baro gidansu zuwa inda yake bukatar ganinta so that ya san idan ya fara tasiri a zuciyarta ko akasin haka, yadda ta nuna masa ba zata iya zuwa gurin da suka saba haduwa da farko ba ya nuna tana tsoron yan'gidansu sun ganta kenan kamar yadda ta fada masa cewar idan mahaifinta ko wani ya gani bata san iya hukunci da za'ayi mata. Yana zaune cikin motarsa ya hango yarinyar da suka yi fada a gurin aikin mahaifinsa an sauke ta a wata motar da bata gurin aikin ba, 206 Saurayi a ciki yana sanye da kananan kaya kamar yadda Ameer ma ya saka kananan kayan, ita kuma tana sanye da rigar gurin aikin sai skirt ta dora after dress sai mayafin rigar da ta yafa tana rataye da jakarta daya hannunta na rike da bakar farar ledar dake dauke da rubutun kamfanin. Bude motar yayi ya fito ya nufi inda take tana tafiyarta a hankali. Miye a cikin ledar nan? Ta tsaya sai ta juyo ta kalleshi kamar ba zata ce komai ganin shi ne, sai kuma ta daure ta ce. Abinci ne? Hmmm-uhmm wato kin yi sa'a ba a koreki ba bayan fadan da kika yi da ni, and now sata kike mana a gurin ko? Kalmar sata ta bata mata rai, sai dai mai nema baya fushi kamar yadda Kakarta ta fada mata dole ta hakurewa wani abun. Aa ni ban taba sata ba, mai gurin ya amince mana mu rika diba idan ya rage ko kuma idan mun san babu shi a gida Oh Really i will ake him then, but before that bari na fada miki wani abu karki sake saka rigar kamfaninmu kina yawo da ita samari na dauki kala kala kuna iskancinku idan an gani sai ace a karkashin mahaifina kike aiki, and consider yourself a matsayin korrriya a gurin nan Ta daka masa tsawa domin kalmar iskanci da ya jefeta da shi ya bata mata rai. Sai me? Idan ka koreni rai ka acire min? Kuma ni ba yar iska ba ce ban san miye iskanci ban hada hanya da shi ba, amman kai ka sanshi saboda aikinka ne abun da kake yi ne, kuma ka bakar shegiyar shinkafar ku nan ka dauka ka tafi da ita Ta jefa masa shimkafar, har ta juya ta fara tafiya sai kuma ta dawo ta iso har inda yake ta kama hannunsa yaja kamar wani yaro haka ya rika binta har cikin unguwar ta shiga da shi har cikin gidan ta tsaya da shi kofar dakin ta bude kofar dakin. Ga gidan mu nan ka ga dakin da nake rayuwa nan, idan ka iya ka kore ni a nan din ma, sannan ka raba ni da duniyar gaba daya, sai na san ka kai tsohon shege, idan baka gode ni'imar Allah ba zaka godewa zabarsa, ba dai ka zabi wulakanta bayinsa ba saboda ya daukaka ya baka abun da bayinsa suke nema a karkashinka? Ka ji tsoron karshenka Wadanda suke cikin gidan suka fito suna kallonta da shi, Mamanta ma ta fito da sauri tare da kakarta dake lullube da zane zata fita bara. Miya faru Humaira? Mamarta ta tambaya sai Humaira ta fashe da kuka ta shige falon ta bar shi a gurin tsaye. Kakarta ta taso ka iso inda yake tana kallon fuskarsa da wani irin kallo kamar zata cinye shi. Jika na, ka yi hakuri idan wani abun Humaira ta yi maka, kai namiji ne, karfi da zuciya da fushi ba daya ba, a inda ta nuna maka a nan muke rayu, bata da kowa sai Allah marainiya ce ubanta ya rasu kuma da aikinku da dogara da shi take biyan makaranta tana mana hidima har ta yi ma kanta wani lokacin, mahaifiyarta bata sana'ar komai ni kuma kakarta bara kawai na iya, dan Allah karka koreta karka mata wani abun ka yi jinkan na kasa da kai, duk wanda ya
Chapter 46 · 0% Book details