← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 165

Sashe 32

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

daya, ta fara ci da sauri, ko tsayawa bata yi ta tauna da shi da kyau take hadewa tsabar yunwar da take ji, ta sake miko hannu ta dauki na biyu ta cinye ta dauki na uku har ta cinye Apple din guda uku sannan ta miko hannu ta dauko gorar ruwan, murda ta yi sai ta ji mabudin da karfi ba kamar na dazun da aka bata ba, hakan ya saka ta turo gorar waje, Dr na ganin haka sai ya dauki gorar ya bude mata ya sake ajewa, sai gashi ta ziro hannu ta dauka ta sha ta turo masa rabi. A nan ya lekata sai ta sako masa ido tana jin sake jiki da shi ba kamar sauran da take ganinsu kamar dodo ba. Baby Girl zo nan Ya mika mata hannu, kalmar Baby Girl ya zauna a kanta, tun a jiya da ya furta mata ba kalmar kawai ba, har da wasu maganganu da aka yi ta dauki wadanda ake yawan furtawa duk kuwa da kasancewar bata san ma'anarsu ba. Kallon hannunsa dake sanye da safa take kamar mai tunanin zuwa, ganin hakan ya saka ya dawo ta hannu ya cire safa daman ba a san likita da kyama ba, ya sake mika mata hannu, ta dade tana kallon hannun kamin ta yarda ta mika masa nata, tana sai ya riko hannun ya janyota alamar yana son ta fito, tana ganin haka ta yi saurin sakin hannunsa, be gaji ba ya sake mika mata hannun yana furta mata sunan da yake son ta saba da shi, wannan karon buge masa hannun ta yi domin ta sanar da shi cewar ba zata fito ba, murmushi ya sake mika mata hannu a karo na uku. Baby girl Ta miko masa hannun ta kama hannunsa ya janyota sai ta somawa fitowa a hankali, tana lekowa ta ga ba shi kadai ba ta yi saurin komawa. Juyawa yayi ya kallesu Kun tsoratata Fita suka yi daga gurin suka ja mata curtains din suka labe suna lekonta. Baby girl... Ya fada bayan ya mika mata hannu, sai ta buge masa hannu a karo na biyu. Lekawa yayi ya ga irin zaman da tayi sannan ya daga kansa ya saka hannunsa yana tafiya da yatsunsa kamar tafiyar mutun kamin ya kai inda take sai ta buge masa hannu. Lekawa yayi mata fuska sannan ya mika hannunsa ya rama bugun da tayi masa a hankali, sannan ya janye hannun da sauri, kamin ya sake mikawa ta sake bugewa, haka suka yi har sau biyar sannan ta yarda ta rike hannunsa ta leko kamar wata bera ta kalli gurin ganin babu kowa ba kamar dazun ba ya saka ta fito gaba daya taba kallonsa da idonta kamar za su masa magana. Saurin kawarda idonta yayi daga barin kallon rabin kirjinta da ke waje, zagen dake kan gadon na asibiti ya dauka zai nada mata a jikinsa sai ta buge zanen, ganin hakan ya saka ba tare da kyamar komai ba ya cire lab coat din dake jikinsa ya saka mata sannan ya fara kokarin mikewa da ita tsaye a nan wata sabuwar rigimar ta bullo ita san ba zata mike tsayewa, ganin take kamar wani abun zai mata, har sai da ya kama rigar ya fara saka mata button din da karfi, sannan ta kalli rigar da take jikinta ba wannan karo na farko data saka rigar data rufe jikinta har guiwarta ba domin tana saka gown da take a cikin tufafin kala uku da suke duniya, abun da bata taba ba shi ne saka tufafin da engine ya saka har aka saka wani anini a jiki. Kallon rigar take sosai kamin ta kalleshi idonta sun yi zurun zurun irin na wandanda yunwa ta samu sa'arsu ta yi musu kamun kazar kuku, ga dan karen tsoron dake fuskarta kamar yayi magana. Murmushi ya saka mata a kokarinsa an kwantar mata da hankali da kuma sakawa ta aminta da shi. Ya akai tufafinta sika yage? Ya tambaya domin ya san suna bayan curtains din a boye suna lekenta. Dazun da Doctor Mu'azu yace a fito da ita ayi mata allura saboda ko an bata maganin ba zata sha ba, shi ne ta yi ta kokawa da mutane har ta barka kayan Kamar ance mata kamata za su yi sai ta juya da sauri zata koma kasan gadon hanzarin riketa Dr Shuraim yayi sai ta juyo ta rumgume kam tana kuka jikinta ko'ina rawa yake, ba a taba mata daukar karfe aka soka mata a jiki ba sai wannan karon da ta samu kanta a duniyar da bata san kowa ba kuma kowa be santa ba, yadda ta kamkame shi ko kwakkwaran motsi kasa yi yayi. Hankalinta be kara tashi ba sai da Police din da aka bari ya tsareta ya leko dakin da uniform dinsa wannan karon bakin wando ne da riga sky blue a jikinsa, a nan ta kwala wani irin kara da siririyar muryarta irin karar nan dake shiga cikin kunne ta hana kwakwalwa kwanciyar hankali da sukuni, har sai da Dr Shuraim ya rufe kunnensa. Fita fita fita Dan sanda ya fita waje, sannan ta yi shiru ta kara kankameshi, tana wani numfashi kamar zata shide, jikinta rawa yake ta ko'ina tana daga kai sama kamar ta ga abun tsoro. Dr Shuraim be yarda yayi motsi ba har sai da ta samu natsuwa sannan ya dagota jikinsa ya kama hannunta mai ciwo a hankali ya duba, sai ta yi saurin fisge hannun ta boye bayanta, sai dai bata yarda ta sake rigarsa da dayan hannunta da yake lafiya ba, gaba daya a firgice take wata rayuwa take gani da bata mafarkin yi ba, ga wasu mutane da bata san inda suka fito ba, komai ganinsa take kamar mafarki. Tausayinta sai ya kama shi sosai domin yadda hawaye ke mata zuba abun tausayi ne sosai ga wanda ya san zafin hawaye. Zaunawa yayi saman gadon sai ta zauna daf da shi kamar zata shige a jikinsa ta saki rigarsa ta kama hannunsa ta rike, shi kadai ne mutumen da take jin zata iya aminta dashi, ko ba komai shi ya bata irin abun da take iya ci kuma yayi kokarin fahimtarta har ta sake jiki da shi. Dr Tafiya za'ayi da ita Dayan police din da ya iso ya fada yana leko gurin. Yanzu? Eh daga can office aka ce mu taho da ita za a wuce da ita Abuja ne? Gurin me? Yarinyar da bata da lafiya? Sun ce za a kula da ita a ne a can za su sama mata wani Asibitin, kamin a gano inda yan'uwanta suke, baban yarinyar da aka tsince ta a motar ne zai rika kamin a gano danginta Shiru yayi be ce komai ba, domin shi ma ya san yadda kasar take cikin domin yana cikinta, baya son ya shiga hurumin sa ba nashi ba, ba dan haka ba zai tambaya ya ji ko an hukunta wanda aka kama motar tata. But a yanzu ba shi ne babbar damuwarsa ba, damuwarsa ina za a kai wannan yarinyar? Da gaske rika ta din za'ayi ko kuma so ake a yi mata wani abu a rufe case din? Idan ma da gaske ne abu ne mai wahala ta yarda da bisu idan ta bisu kamin ta saba abu ne mai wahala domin ya lura da yanayinta tana da wuyar sabo. A take ya ji tausayinta ya cika masa zuciya sai dai babu yadda zai yi ya hana faruwar hakan domin ba huruminsa ba ne. Okay zamu shiryar takardar transfer, wace asibitin za a kaita a Abuja? Ba mu da masaniya akan wannan Ya kamata ku sani, saboda kar a cutar da yarinyar nan, ina ganin huruminku ne Eh zamu sani ai dole, for now dai ba mu sani ba saboda case din a hannun manyan mu yake, su za su kula da komai Daga haka be sake cewa komai ba, har aka dauko masa tarkadun da komai suka miko masa yayi rubutu a kai sannan ya mikawa police din file dinta ya mike tsaye, tana ganin haka sai ta mike tsaye, a karon farko ta lura da fankar dake lake a sama tana bada iska, tun da take a rayuwarta bata taba sanin wani abu makamancin wannan ba sai yau, kallon fankar take sosai tana mamakin minene a gurin. Bata ankaro ba ta ji an taba hannunta dubawar da zata yi sai ta yi arba da masu bakaken kayan nan na jiya suna kokarin bata da mutumen da take jin kamar ta dade tare da shi. Wani irin kara ta saka tana fisgar hannunta tana son ta kubuce daga rikon da suka yi mata amman ina karfi ba daya ba, ko a babba balle ita da take matashiya, da karfin tsiya suka rabata da Dr da zuciyarsa ke masa ba dadi shi ma jin yake kamar ya dade tare da ita, musamman da be san inda za a kaita ba, Allah kadai ya san abun da za'ayi mata wata kila cutar da ita za ayi be sani ba. Fashewa ta yi da wani irin kuka ta fara fisge fisge police din ya dauke ta sama sai ta miko hannu tana son riko Dr Shuraim daya fito waje ward din yana kallonta zuciyarsa na masa ba dadi, hannu kawai take miko masa alamar ya rikota tana girgiza kai tana kuka sosai kamin ta kai bakinta ta gantsawa Police din cizo ba shiri ya sake ta sai ta rugo a guje ta gurin Dr Shuraim ta rumgumeshi da karfi tana kuka, dayan police din ne ya zo zai rikata sai Dr ya dakatar da shi. Kyaleta Hannu ta kai ta bugu Dr Shuraim da mugun karfi da kafa bakinta a kirjinsa ta cijeshi tana dukan kirjin nasa, so take ta ce miyasa zai bari a tafi da ita amman bata da bakin fadin haka domin bata jin yaren da suke fahimta kamar yadda su ma basa iya fahimtar yarenta. Sai dai kwarewa irin ta masu basira da hikima sai ya fahimcin haushinsa take ji, hannu ya saka yana rarrashinta. Yi hakuri ya isa Shiru ta yi kamar ba ita ce ta bude baki tana ihu ba, sai ta yi tsit ta kwantar da kanta a jikinsa kamar mage ta
Chapter 32 · 0% Book details