Sashe 67
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
son Ameer ba, kuma ba zan fasa aurensa kamar yadda nake da niya ba, ko kun daura min aure da wani ba zan zauna ba, kun san fi kowa sanin addini ya hana auren dole, hakkin da nake da shi akanku ne ku aura min wanda nake so Enough Nimra....! Mind you ina lallabaki ina daga miki kafa ne saboda kar damuwar ta yi miki yawa, amman ba kiji na fada miki ba zaki auri Ameer ba, ko da kuwa shi kadai ya rage a duniyar nan, ko zaki gudu ki tafi wani gurin idan ma wannan ne abun da kike da kuduri har yanzu to ki daina, gurin kowa zaki je ko ki kai kararmu ba za ki auri Ameer ba Saboda me? Nimra ta tambaya a tsawace sai Ummi ta daka mata tsawa. Saboda Addinin Musulunci ya haramta aure a tsakaninku Ta ina? Ummi kin san me kike fada kuwa? Ameer fa musulmi ne, ba kafiri ba. Duk wank abun da zaki fada ba zai hana aure a tsakanina da shi ba, matukar ba gawata kike son gani ba. Saboda Nonon da Ameer ya sha ya saki shi kika kama kika sha har na yayeki, yadda aure yake haram a tsakaninki da Maleek haka ya haramta tsakaninki da Ameer Nimra ta yi murmushin takaici, abun is some how amman ta san wannan duk shiri ne Ta nan kuma kuka bullo...? Ummi ta dauke ta da mari. This is Reality Nimra ki dawo hayyacinki... Wai so kuke ku haukata ni? Ta fashe da kuka.... Nimra kuma ta dafe kunci tana kallon Ummi... *Littafin WANI GARI na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660* Kallon da ya fi kama da na ga mahaukaci Namra ta fara yi mata ganin ta zo a guje ta rumgume mata bako. Yarinyar nan fa bata da hankali Ta fada ta karasa inda suke zata janyo Waira da kafafuwanta ke lake da na bakonta sai Shuraim ya ja baya ya girgiza mata kai yana murmushi kana ganin fuskarsa ka san farinciki a ciki shimfide. Waira ta dago ta kalleta sai ta saka hannunta ya shafa fuskarsa ta ja kumatunsa har sai da ya kyalkyale da dariya mai sauti, ita ma ta fashe da dariyar ta kara rumgume shi kam kam kamar za a kwace mata shi, ta kasa yarda Shuraim din ta ne, mutumen da bata taba tunanin zata sake ganinsa ba a rayuwarta, mafarkin be taba kawo mata zai dawo gareta ba. Baby Girl Namra ta kalleshi da yanayin mamakin da kuma kufula da kishi a lokaci daya na rumgumar wata macen da bata san alakarsu ba. A zatonta ita yake kira shi kuma da Waira yake ita ma Waira ta san da ita yake domin a zatonta ita kadai ce yake cewa Baby girl. Ta sauke kafafuwanta ta sauko tana rike da hannunsa dayan hannunta kuma tana nuna masa zoben dake wuyanta. Sulem... Your ring Ta saka hannu ta rika zoben yana dubawa fuskarsa dauke da murmushi. Hakan yayi daidai ta fitowar abokinsa dake cikin motar ya nufo su yana murmushi with confused a the same time. Ban taba tunanin zan sake haduwa dake ba, lokuta da dama ina tunaninki na ce yanzu ko ina yarinyar nan take, tana raye ko mace ko wani abun ya same ta, wata kila saboda hankalina ya kara kwanciya Allah ya sake hada mu so that na ga yadda kike rayuwa Maganar yake kallon idonta masu matukar daukar hankali. Sulem.... Ina son Sulem.... So much so much Tana fada tana juya kai wani kalar farinciki da nishadi ne a zuciyarta da baya misaltuwa. Shuraim ya saka hannu ya taba fuskarta gaba daya ta bata masa da masoyiyarsa Namra dake gurin farincikin sake ganinta ya mantar da shi cewar shi suriki ne a gidan. Kin yi kyau sosai, kin canja Waira kamar bake ba Ta yi murmushi ta sake rumgumeshi, a nan ya dago sai suka yi ido hudu da Namra da fuskarta ke hade sai ya dan rage murmushin da yake yaja baya ta cire jikinsa daga Waira, abun ka da mai dauki sai ta kama hannunsa ta saka cikin nata ta sarkafe. Waira Ta juyo jin an kira sunanta a tsawace ta kalli saitin katon windows din falon Ummi da aka bude ta kalli Maleek dake tsaye. Shigo ciki... Sulem ne... Sanin kamar ba zai maimaita mata furucin ba ya saka ta saki hannun Shuraim idonta na cika da kwalla. Sulem karka tafi... Shuraim da abokinsa sun dauke idonsu daga kallon Maleek, Shuraim ya kalli Waira yayi mata murmushi. Ba yanzu zan tafi ba, idan kuma zan tafi zan miki magana je ana kiranki Aa ka zauna duka a nan please Sulem... Shuraim... Ya gyara mata, a kokarinta na gyarawar sai ta sake furta sunan a yadda take fada. Sulem.... Yadda ta kira sunan ma ya masa dadi, sai kawai yayi murmushi ya kalli Namra da har lokacin ta saka sakim fuska. She's my patient Just... Ta tabe baki tana yatsina fuska kamar ta ga abun kazanta. Murmushi kawai yayi ya duba agogon hannunsa kamin ya kalli abokinsa da shi mamakin yake ya ce. Ma maybe ka manta ta amman na sha baka labarinta Abokin ya dan yi murmushi be ce komai ba sai kallon fuskar Namra yake yana karantarta. Ba dan kar yace ta wulakanta shi ba da a gurin zata barshi tsaye, for which reason zai rumgume wata a gabanta, at first ma ta dauka wata alaka can sai bayan sun gama murzar juna zai ba fada mata cewar patient dinsa ce. Bismillah.... Ta masu ishara da hanyar part din Abiey. Na dauka wata alaka ce mai karfi a tsakaninku Suna tafiya ta fadi haka sai ya kalli yanayinta ta da ya canja ta kasa sake fuska har lokacin. Murmushi yayi ya juya ya kalli kofar part din Ummi inda Waira ta shiga ya sake juyo suka cigaba da tafiyar. Wata kila kina nufin alakar jini, amman a gurina alakar da zaciya zata samu samu kwanciyar hankali idan ta san wanda take tausayi yana cikin koshin lafiya ita ma wata alaka ce mai karfi, da kin san yadda na damu da aka dauko yarinyar aka ce za a zo da ita Abuja, da kin taiyani murnar ganinta da na yi a gidanku, ko ba komai na san zata samu kwanciyar hankali da tsoro a nan Haka ne ina taya ka murna Congratulations Sulem Ta fada tana dariyar yake, a badini bakar naganar ce ta yi masa, sai dai shi kuma be fahimta ba domin be fashinci komai ba. Iyakar kokarin da ta yi na danne abun da take ji a zuciyarta ne ta kula da shi yadda ya kamata sai dai duk wani dauki da murnar da take na zuwansa ya ragu a ranta. Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka Waira ta shigo falon da kofarsa take bude tun a fitar da ta yi da gudu bata tsaya rufe kofar ba, maida kofar ta yi ta rufe sai ta tsaya jikin kofar tana taba hannunta ganin fuskar Maleek a hade. Ba ki da hankali? Ta yi bako ya zo gurinta kije kina ruining abun da ta shirya, ji yadda kika fita da gudu kafafuwa tsil tsil kamar tsuntsuwa, ku a garinku ba ku da tarbiyar girmama bako ne? Haka ake tarbon bako? Yana mata fada tana turo baki daman tuni hawaye ya cika idonta domin bata so rabuwa da Sulem dinta ba, gashi kuma yanzu ya tsare ta da fada. Takawa ta fara yi ta bi ta gabansa zata sai ya daka mata tsawa. Ba magana nake miki ba shi ne zaki wuce Zabura ta yi ta hawayen dake makalle a idonta ya sauko saman kyakkyawan kumatunta, hakan kuma ba karamin kyau ya kara mata ba, dana da kwarjinin da har kuka kyau yake mata idan tana yi. Sulem ne ai Ba Sulem ba sule, ina kika sanshi? Ta kai hannu ta rika sarkar wuyanta ta soma magana muryarta na karkarwa irin wanda kuka ke daf da subucewa. Ya bani wannan ya saka min Miya faru? Mahmood dake saukowa stairs ya tambaya ganin hawaye na sauko mata wasu na bin wasu. Wallahi yarinyar nan bata da hankali yau na gani, wanda zai auri Namra ne ya zo sai kawai ta tafi ta rumgumeshi baka ga yadda Namra ta bata rai ba, idan ba hauka ba ina aka taba haka Toh ai Sulem dina ne Ta fada tana kuka. Mahmood ta sauko gaba daya ta tsaya inda take. Wane Sulem Sulem Ta nuna masa sarkar wuyanta. Oh na gane kai ta san shi fa, idan bata san shi ba ai ba zata je haka nan ta rumgume shi ba, ka gane Sulem din da take yawan magana, aiko ni ma zan so ganinsa ko dan na ji inda suka san juna tun da bata fada mana ba, waya sani ma ko an'uwanta ne You miss the point ko yaya ne be kamatadaga ganin mutum an gayyato shi kije ki rumgume shi ba, wannan ai rashin tarbiya ne da sanin ciwon kai, she's so annoying sai ta rika yin abu kamar wata yar jaririya Mahmood ya zauna. Maybe daukin ganinsa take kuma ita ai ba musulma ba ce wata kila al'adarsu haka ake tarbon mutum Tsaki yayi ya nufi hanyar fita daga falon, Mahmood ya bishi da kallo baki saki, sai a yanzu shi ma yake mamakin sbun da Maleek yayi kamar ba shi ba, da can babu ruwansa da duk wani abun da ya shafi Waira, wata kila saboda kanennsa ba su taba rumgumar wani a gaban idonsa balle ace ya tsawata musu ita kuma ya ga ta yi dole yayi mata fada. Maleek be duba yiyuwar akwai alaka tsakaninsu ba, shi dai abun da idonsa ya gane masa ne be masa dadi ba, domin be ga dalilin rumgume mijin da kanwarsa zata aura Da Waira ta yi ba, yanayin yadda ya ga fuskar yar'uwarsa ta sauya baya tarin farincikin data wuce ta gabansa ta fita da shi ya sosa masa rai, wata kila yana taya yar'uwarsa kishi ne, ko kuma yana ganin rashin dacewar hakan da gaske. Bayan fitar Maleek Mahmood ya kalli Waira yayi murmushi Karki