Sashe 36
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
na fito mata a idon amaimakon hawaye, babu wanda ya kula a cikinsu, saboda Hajiya Hajara ta ja mijinta gefe ta inda zai kalli TV da kyau, Maimoon kuma tana kitchen tana mulka tuwon shimkafa da tun kamin magariba ta gama miyarsa. Hannu biyu Waira ta saka ta taba jinin dake zubo mata ta kalla, take hankalinta yayi mugun tashi domin bata hawayen jini Eid ne yake hawayen jini idan yayi kuka, kukansa kuma yana nufi abubuwa da yawa abu ne mawuyaci yayi kuka idan kuma yayi to ta ace masa ne. Tsafi aka jefata da shi ko kuma Eid ne a cikin wata matsalar wata kila kuma Eid din ne a kusa, ta leka falon tana kallon ko'ina kamin ta dawo ta sake boyewa daga nan kukanta ya tsaya. Tana ta sauren abun da zai sameta. Ina take? Shi ne abun da Dr Shuraim ya fara tambaya a lokacin da ya shigo falon, Mahaifiyarsa ta fada masa inda take boye. Gurin ya nufa ya lekata har ta zabura sai ta tuna tafiya yayi ya barta sai ta koma ta zauna ta hade fuska ta juya masa baya, shi kam ba ta fushin da take yake ba jinin da ya gani a fuskarta da hannunta ne ya daga masa hankali. Ya aje ledar maganin dake hannunsa da sauri ya kama hannunta yana dubawa. Ina kika samu jini? Ta kalli hannayen nata, sai ya juya da sauri ya kalli iyayensa. Ta jima kanta ciwo ne? Miy faru? Jini ne a fuskarta da hannu Subhanallahi jini Hajiya ta karaso tana dubawa. Tun da ka fita bata fito daga gurin nan ba, in da ba ta jiwa kanta ciwo ba, to babu wanda ya taba ta, sai dai ko idan ciwon dake hannunta ne No duba da kyau ki gani, babu jini a hannunta ko kadan Ya nuna mata hannun, kamin ya shiga yi ma Waira na kurame, yana nuna jinin yana tambayarta da hannu a ina jinin ya fito. Sai ta nuna masa idonta a nan ya maida hankali gurin idon sai ya lura har yanzu akwai sauran jini a ciki dubawa yake sosai ko zai ga inda ta ji ciwo a idon har jini yake fito mata. Yarinyar nan abar tsoroce Shuraim ka yi saurin hannata musu ita kar ta mutu a hannunmu, tun da nake a rayuwata ban taba jin mai kukan jini ba amman yau Allah ya nuna min, anya mutum ce kuwa? Idan kuma mutum ce to sun riga sun bada jininta mutuwa zata yi Cikin yanayi dake nuna be jidadin maganar Hajiyarsa ba ya juyo ya kalleta. Haba Hajiya, yanzu da ace tana ji ai sai ki saka ta shiga tashin hankali, ba a saurin yake hukuci ga abun da baka sani ba To sannu Malam, ga zahiri kana gani zaka ce kar a yanke hukunci ku ji min wani ikon Allah, Doctor ka ga wani abu? Kukan jini yarinyar nan take Mahaifin Shuraim ya turo wheelchair dinsa da kansa irin ya karaso gurin da mamakinsa yana kallonta ganin ido yayi mata yawa ya saka ta boye fuskarta. Bata son kallo, bari na mata allurar sai na kaita dakin Maimoon ta kwanta Ba dai Maimoon ba kam Shuraim ta cinye min a ana kwana, ko kuma ta mutu ace ita ta kasheta? Aa lalala ni ai lamarinta a yanzu ya ba ni tsoro, bana jin zata kwana a gidan nan ma ka maida ita inda ka daukota can gurin police din su sai su sama mata inda zata kwanta Bude baki yayi zai yi magana sai mahaifinsa ya goyawa Hajiya baya. Gaskiya, karka aikata irin kuskuren dana aikata wanda nake nadama har yanzu, garin taimako ka jefa kanka da mu a matsala, ko kuma ita yarinyar ma gaba daya Bata yarda da kowa yanzu Abba kai ma ka gani kuma idan nace zan maidata fitina ce Bata yarda da kowa idan za a kaita abujar kai zaka kaita ne? Ji min wata maganar banza? Karka janyo mana masifa Shuraim dan Allah ka maida yarinyar nan gurin tun ranka be bace ba Waira ta dago ta kalli Shuraim tana iya fahimtar fada ake masa, wata kila kuma duk saboda ita ne. Hajiya mun riga mun yi magana da su, sun ce da safe za su zo su dauke ta sai kuma yanzu na maida musu ita? Idan na kaita a can wani abun ya sameta still ba mu fita daga zargi ba Kara ta mutu a hannunsu, duk abun da zai sameta ya sameta a can, ba nan ba, ka tashi ka kai yarinyar nan na ce maka Shuraim Ta daka mashi tsawar data saka shi sa hannu biyu ya dafe kansa da hannu biyu. Waira ta sakarwa Hajiya Hajara ido daman tun da suka dannenta suka mata wanka take tsoronsu balle kuma yanzu da take yi ma Shuraim fada har ya rike kansa. Shikenan zan mai da ita Yanzu kuma ba sai anjima ba, daman can ban da karanbani dauko ta ba, haka kawai daga yarinya tana kuka sai ka ce sai ka zo mana da ita Tausayinsa sai ya kama Waira ta san duk saboda ita ake masa fada, ba zata fadi abun da suke cewa ba, amman ta san akanta ne suke masa fadan, shi ma tausayinta yaji hakam ya hana shi yi mata allurar da ya siyo sai ya bude maganin kawai ya balla ya saka mata a baki, sai ta bude bakin a hankali saboda yarda da ta yi da shi ba zai cutar da ita ba ya saka mata maganin ta fara sotsawa jin yana da daci ba a yadda ta yi tsammani ba ya saka ta yi yunkurin zubarwa sai ya girgiza mata kai. Maimoon kawo ruwa Ya kwalawa kanwarsa kira, sai gata da kofin ruwan data debo a tap ta mika masa ya karba ya kai mata a baki, abun ka da wanda be saba ba da zo hade maganin sai ya tsaya mata a makoshi ta kasa hadewa ta dawo da shi a hannunta, sai ya karba ya balla wani ya bata ta kora mata da ruwa a dole ta hade da sauri haka yayi ta mata har ta anye sannan ya rika hannunta suka mike tsaye. Ya nufi gurin da ta zubar da kayanta ya dauka ya mika mata ta rike da hannun da baya ciwo, shi kuma ya rike wuciyar hannun ya jata suka fice daga falon, binshi kawai take kamar wata igiya har ya isa gurin motar da suka shigo dazun, a tsoro ya kamata jikinta ya fara rawa a taken hawayen na jini suka fara mata zuba, shi kanshi yayi mamakin ganin hawayen jini a idonta. Bude motar yayi ya dauko tissue ya goge mata hawayen, hakan nan ya ji yana sha'awar rumgumarta saboda ya kwantar mata da hankali, ba dan yau kadai ba har da gobe dan ya san da mota za aje da ita Abuja. Rumgume ta yayi yana shafa bayanta alamar rarrashi, yanayinsa sai yayi mata kamar na Eid da baya son kukanta. Bata san lokacin data kankameshi ba ta fashe da wani irin kuka mai karfi, jikinta na bata rabuwa zai yi da ita, bata san yaushe zata sake ganinsa ba, haka kuma bata san hannun da zata fada ba, bata san waye zai fahimce kamar shi ba. Dagota yayi ya duba idonta a yanzu din ma hawayen jinin ne, ya dauko wani tissue ya goge mata sannan ya bude mata front seat, wani irin dauke numfashi ta yi ta kalleshi, sai ya dafa kafadarta zai shigar da ita sai ta rufe ido gam jikinta ya fara rawa, hannunsa ya saka ya bude mata idon tana kallonsa sai ya girgiza mata kai, bata fasa hawayen ba, shi kuma be fasa goge mata ba har ya zaunar da ita cikin motar, sai ta ki yarda ta zauna a inda ya zaunar da ita ta sulale kasa ta matse kanta ta zauna a inda ya kamata ce kafafuwanta ne a gurin. A hankali ya rufe motar saboda kar ya daga mata hankali ya zagoyo ta dayan side din ya shiga ya saka maganinta da tufafinta a back seat ya kunan motar a hankali ya fara tukawa kadan kadan har ya fice daga gidan. Ganin ta ki daina hawayen kuma ta kasa rufe idon ta kasa daina kallonsa ya saka yayi mata murmushi ya mika hannunsa ya rike hannunta. Tausayi take ba shi sosai, ya san zata san wahalar rayuwa a inda zata je, idan ma ta rayu kenan idan kuma ta mutu fa? Kamar yadda mahaifiyarsa tace? Ko kuma yadda yake zargin tsafi za'ayi da ita? Tafiya yayi mai nisa har sai da fita unguwar, gidansa incomplete building ne, be gama ba balle yace ua tafi can ya kwana ba kuma zai iya kwana a hotel ba, gashi baya jin zai iya kaita gurin police din a yanzu idan wani yayi kokarin keta haddinta fa? Yadda take da masifar kyaun nan zata iya jan hankalin wani ya ji yana sha'awar yin alfasha da ita. Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya dauki hanyar gidan nasa da yake ginawa gimbiyarsa dake Abuja, da kansa ya fita ta bude gate din ya shiga da motar sannan ya dawo ya rufe gate din, fita yayi ya zagaya side din da take ya kwantar da kujerar ya dagota ta dora masa ya share mata hawayen, babu haske a gidan a dole ya bar hasken motarsa a kunne ya kunna na wayarsa. Ita dai kallon gurin kawai take ya dauko carpet ya shimfida a gafenta ya zauna kasa ya jingina jikinsa kusa da kujerar da take zaune saboda ta samu natsuwa. Be daga daga gurin ba har sai da aka yi sallah Isha'i be sha wahala samun ruwa da bula ba saboda akwai rijiya a gidan, kuma akwai butocin da masu aiki suke amfani da su su yi sallah ko kama ruwa a duk lokacin da aikin ya kawo su, da kansa ya bude rijiyar ya debo ruwa ya zuba a bukatar yana juyowa sai ya ganta tsaye bayanshi, murmushi kawai yayi ya zauna bakin rijiyar yayi alwala ta sake biyoshi har inda ya aje carpet din dake ta zauna a kasa tana kallonsa har ya gama Sallah. Rikata yayi ya maida ita cikin motar ya rufe, sannan ya