Sashe 80
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
zata zabi rike shi ne a ko wane hali ta shiga, yaran da muke naman Allah ya ba mu, amman ita ta samu ta wofintar? Wannan ai kamar butulcewa Ubangiji ne. Bayan rabuwar mu da Mr Bashir ya dade be yi aure ba, saboda ya gwada son uwar yaro sai dai tsoron saurayinta da ya dade yana farautarta yayi masa shigar rago, daga baya sai ya bar kasa tare dan saboda yana matukar kaunarsa da ya dawo kuma sai be zauna a Kano ba ya zauna a Abuja, ya saka ansa makaranta mai kyau da yayi wayo sai ya fitar da shi waje, a duk tsawon lokacin nan kullum ina bibiyar rayuwar yaron ina zuwa ganinsa wannan ya saka shakuwa da aminci a tsakaninmu, amman ko na rana aya ban taba jin mahaifiyar yaron ta zo ganinsa ba, ban taba jin ta kira waya ta tambaye lafiyarsa ba, daga baya ma sai na samu labarin cewar ta haihu tana rayuwarta ta dabam, har sun bar garin Kano, sai dai ban san inda suka koma ba, na yi matukar takaici Ameer da yaron nan be girma a hannuna ba, da na nuna masa soyayya da gata fiye da yadda mahaifinsa yai masa, da be san wani abu maraicin rashin uwa ba... (Full story yana a cikin littafin farko wato CIWON SO labarin Zahra da Abiey da Deen da kuka Hajiya Jamila da mijinta Mr Bashir har ma da wasu, mai son zai iya min magana ya siya domin shi ma na kudi ne 08036126660) Tare da shesshekar kuka ta karasa labarin.. Ameer ma hawaye ne ke sauwa daga cikin idonsa suna jika kumatunsa sannan su isa saman rigarsa. Wa... Wa.... Ne... Ne... Wa... Wa.. Wa.. Nan.. Na.. Na.. Nan... Ya.. Ya... Ya... Yar..... Yaron...? Yana tambaya kalamansa na tsinkewa, numfashi na ta kaiwa huhunsa hari.... Ka yi tunani mana Ameer... Waye ya rike yaron? Meyasa mahaifinka be taba nuna maka hoton mahaifiyarka da ya ce ta mutu ba? Har yau be tana nuna maka danginta ba? Shin bata da family ne? Ko na rana aya yan'uwanta ba su tana ziyararka ba, kai ma baka taba zuwa ba, amman na mahaifinka suna yawan zuwa, kuma ya sansu, be fada maka inda aka binneta ba bayan mutuwar da yayi maka karya ta yi? Baka yi tunanin yadda kake fari kal kamar an larabawa ba? Mahaifinka kuma baki ne? Kai ba ka dubi madubi ba? Ta ina kake kama da Mr Bashir? A hanci ko ido ko haske fata? Mr Bashir ya boye maka wannan gaskiyar ne baya son ka sani har sai bayan ransa, baka yi tunanin miyasa yake ta mallaka maka dukiyarsa ba? Ko wane abu ya ce ya baka a saka shaida da sunanka, miyasa be ba kanenka ba? Saboda ya san baka gadonsa, babu wanda ya san kai ba dana ba ne, sai shi da ni da kannensa, duniya tana kallonka a matsayin an Jamila da Bashir, har matarsa da take cikin gidansa a yanzu bana jin ta san da cewar kai ba an Mr Bashir ba ne, saboda ya boye wannan sirrin da nufin ya zauna har bayan ransa Wani irin abu ne ya ratsa zuciyar Ameer ya rabata biyu... How could I believe this? Me zai saka na yi maka karya? Bayan kuma kai ka bukaci sanin gaskiya, kuma ka bukaci kar na boye maka? Ban san dalilin na son dawowa a gareka ba yanzu, ban san me take nema ba, ba zan iya fadar abu da ta shirya ba, amman uwar data ba rike anta a lokacin da yake bukatar lokaci ba, bata rumgume a lokacin da ya fi kowa son dumin jikinta ba, bata cancanci kasancewa da shi a lokacin da ya saba da wasu iyayen da babu ita a ciki ba, da ace tana kaunarka Ameer da ta kashe aurenta ko kuma ta fasa auren mutumen da take aure a yanzu ta auri Mr Bashir saboda ta rike yaronta, miyasa ma zata cefanar da kai tun kana ciki? Ni fa kawai wadda ta yi shege na so na karba domin su daman basa bukatar yaran, sai gashi na samu mai halal, anya tsananin talauci ko neman mafita na saka uwar da ta amsa sunan uwa rabuwa da anta? Amman ban san manufarta na aikata hakan ba. Zan dauki hoton takardar yarjejeniyar da muka yi da ita na turo maka yanzu a whatsapp, domin tabbatarwa da kuma yarda da abun da na fada maka zaka iya zuwa ka tambaye idan har yanzu tana ajeye da takardar zata suna maka, sannan kuma zan hada ka da Yaya Dr Hamid dake Katsina domin ya warware maka zare da bawa, idan har gaskiya ta bayyaba mararan Ameer Zahra na bukatar amsa tambayoyinka... Bayan bayyanar gaskiya Ammy, bana bukatar ta a kusa da ni, bana son yawun bakina ya hadu da nata Ya danna red circle ya yanke kiran, kansa yayi masa nauyi kamar an dora masa dotsin dala, kwakwalwarsa ta rikece ta birkita tunaninsa da abun da ya kamata yayi tunani da wanda be kamata ba duk kuwa masa yake, har wani na shiga cikin wani. Ya cire wayarsa dake phone holder ya shiga whatsapp dinsa da sauri, chat din Ammy ya shiga kamin ta turo masa hoton har ya kagu... Yana kokarin fita ya kirata sai ga hotuna guda hudu sun shigo sun bude kansa. First picture ya fara dubawa dokokin yarjejeniyar ne haka ya duba su har zuwa na karshe da inda Zahra da Hajiya Jamila suka saka hannu amincewa, sai kuma hannun lauya da na shaidu wato Dr Hamid. Ya jefar da wayar a kujerar dake kusa da tashi ya tashi ya daman motar a kunne take takata kawai yayi da karfi.... WAIRA POV. Zamanta ta yi a cikin motar bayan sun iso saboda tana tsoron kar taje bude motar ta bata masa mota da hannunta da ya lalace da chocolate, har sai da Jabir ya fita ya zagaya ya bude mata sannan ta fito ta dauki ledar. Thank You Ta furta in soft voice tana murmushi shi ma murmushin yayi mata, hakan nan dai take burgeshi, daman can Jabir yana da saurin sabo da mutane domin wayeyen mutum ne da ya iya jan mutane jiki. Kin ga mun fita kina kuka yanzu mun dawo kina dariya Ta sake yin murmushi mai sautin, har ta juya sai kuma ta juyo ta kalleshi. Zaka kira kin Sulem? Ko mu je? Inda yake? Ta daga kai. Toh ai kin ga ni ban ga Sulem din ba balle na san yadda fuskarsa take ba, kuma ban san masaukinsa ba, labarinsa kawai aka ba ni, kuma babu number sa a nan ban san number shi ba Ka sani Ta fada da kamar shagwaba tana son dawo masa da kukan, a iya gaskiyar take fadar ya nemo mata Sulem ko ya kira mata shi, bata gama wayewa da abubuwan garin ba dan haka ba san idan baka da number mutum baka iya kiransa ko kuma shi idan ba shi da number ka ba zai iya kiranka ba, ita dai tana ganin ana waya a kara waya a kunne a ji magana, kuma a iya saninta garinsu idan ana neman mutum ba shi wahalar ganewa. Idan ina da number shi me zai hana na ki kira miki shi? Ba ni da number shi Kana da Idonta har ya fara zubar da hawaye. Matsawa yayi kusa da ita ya ciro wayar ta shi ya mika mata. Idan kina da mumber shi saka a kira shi Ta kalli wayar ita dai tana jin ana cewa numbers kuma ana nuna mata su a makaranta, does that mean kowa yana da number shi kenan, sai ta kama ring din dake wuyanta, ta duba S ne a jiki tunanin ya bata cewar number Sulem dinta kenan. Na shi alphabet ne, ka saka S Jabir be san lokacin da dariya ta subuce masa ba. Ba haka ba ne, ita number kira ai tana da yawa ba kadan ba ce balle ace daya, kuma kin ga number dabam alphabet dabam na daya ba ne Ka kira haka nan Ko na kira ba zai yi ba look here kin ga babu inda S take a nan duk numbers ne Ya nuna mata wayarsa, sai ta taba 5. Gata nan, ita ce ta canja ka kira haka nan zai yi Ya fita gurin ya shiga gurin kira ya nuna mata numbers din mutane. Kin ga yadda numbers suke kowa da kalar tasa kuma suna da yawa Ka saka 5 da yawa 5 dabam S da am ba a banbance muku ba a makaranta? Kuma 5 din har guda nawa zan saka? Da yawa Okay Ya saka 5 din kusan guda ashiri sannan ya kira ya saka mata a speaker, ta ji ana the number you try to call is not exist, sai ta fashe da kuka. Ka cika da yawa, ka saka kamar na su Ya rage ya saka daidai ya sake kira the same thing. Idan mun shiga ki ce Ummi ta kira shi ni wayata ta lalace bata kira kin ce ai abun da take cewa Okay, ni meye number na? Gudun rigimarta ya saka dole ya bata number. Ta share hawaynta da rigar jikinta sannan ta shiga falon, shi kuma ya juya ya shiga motar daman yana da gurin zuwa bata bari sun tafi ba tace ya kawo ta gida. Idonta be sauka a ko'ina sai akan Tea da ta bari dazun, kamin ta kalli dinning room tunawa da a nan ta bar Maleek a lokacin da suka fita, ba ta yi zaton Ummi ta dawo ba dan haka bata haura sama ba sai ta zauna a kasan kujerun da suke nan ta bude wani chocolate din tana ci, tana daf da cinyewa zomonta ya zo gurinta da gudu ya fara shinshina jikinta. Tana ganin haka ta tashi ta shiga Kitchen ta kunna tap ta wanke hannunta sannan ta dauki cup ta aje ta zuba ruwan zafi ta saka Lipton kamar yadda ta ga Ummi tana mata, sugar da sauran kayan hada tea da suke kitchen din sun mata tsawo domin suna a cikin cabinets ne, ita kuma ba wani tsayi ne da ita sosai ba idan ma zata ce ta dauko sai idan zata hau wani abun