← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 165

Sashe 7

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin dalilin da ya saka bata da kawaye kuma kananan yara basa matsawa kusa da ita. Na sha fada miki ki daina wannan halin Su suka ja ni Karya kike yi, ba za su ja ki haka nan kawai ba A karo na biyu ta buge masa hannu saboda ya karyatata, sai ya sake rike kafadarta gam. Muje Sarki yana son ganinki Ya saki kafadar ya rika hannunta ya ja kamar wata kuya yana gaba tana baya har suka isa cikin fadar, tsananin girmamawa da ganin kimar sarki ko yayan mulki a garin ba a hada ido da su sai idan ta kama dole, idan za a gaishesu kuma sai an risina. Eid ya gaishe da sarkin dake zaune tare da jama'arsa sannan Waira ta risina ita ma ta kwashi gaisuwa, Sarkin dake cike da far'a da murnar bikin da aka yi ya kalli Waira da idonta ke kasa hannunta ke rike cikin na Eid yayi murmushi. Ranar yau rana ce mai girma da muhimmanci a garemu, be kamata ace kin kuntatawa wani ba, ba wannan ne karo na farko da aka kawo min kararki ba, amman wannan ne karo na farko da ya kamata na gargade ki, kuma ya yafe miki, kar ki yarda a sake kawo kararki akan kin zalinci wani, zan yafe miki iya na yau kawai saboda albarkar ranar yau da kuma kasancewar ban taba gargadin ki ba sai a yau, ke ta dabam ce a cikin yara sa'aninki Waira, matsayinki da na su ba iri daya ba ne, kina jiran wani matsayi da su har su mutu ba za su iya hawansa ba, ya kamata ki banbanta kanki da sauran yara Ta risinar da kanta kamar yadda ta san na amsawa Shugaba idan yana magana. Na gode Hannun sarki ya daga mata, sannan ya kalli Eid ya ce. Wannan ya zama karo na karshe da zaka rike hannunta a gaban idona Shi ma ya amsawa sarki da kai. Za'a kiyaye Sannan ya saki hannun nata ya juyo ya fito sai ta biyo bayansa, a yanzu kuma fushi take da shi saboda shi ya kawo ta gaban Sarkin, har aka mata gargadi abun da ba a taba yi mata ba, suna fitowa ta sauya hanya ta nufi inda dakinsu yake, tana shiga ta shige dakinta ta kwanta daga bakin kofa tana kallon waje, fuska murtuk babu annuri, zakarun da suke gidan suka taso suka tare a bakin kofar suna kallonta, tana ganin haka ta san abun da suke bukata, sai ta tashi ta bude inda take aje musu abunci ta dauko ta zuba musu su ka ci, ta bude wani karamin rame ta dauko beranta ta dawo bakin kofar ta zauna tana shafa shi, a gurin ta yi ta zama har hudu yayi sannan ta tashi ta koma kan shimfidarta ta kwanta ba tare da ta kunna fitilar aci balbal da ta saba kunnawa ba. Kamar wata gawa tun da ta kwanta bata farka ba sai da hasken rana ya keto dakin, sannan ta tashi zaune tana murza ido, ta dade a zaune sannan ta tashi ta fita ta yi fitsari, ba musulma bace balle ta san wanke fuska da yin alwala ayi sallah, ba mai tsabta ba ce balle ta san wanke baki da hannu kamin aci wani abu, tana dawowa dakin ta nufi inda ta saba aje ayabar ta sai ta samu an huda ta kasa an ci ayabar an ja wata a zubar, a fusace ta juyo ta kalli beranta dake kwance akan gado yana sharbar bachi ta watsa masa wata uwar harara. Gurin da ta saba aje bulala ta dukan beran da zakarun da suka mata laifi ta nufa ta dauko ta labta masa daya, da gudu ya shige cikin katifar ta kada yana tsuwa kamar wani karamin tsuntsun, haka take a duk lokacin da suka mata laifi sai ta zanesu da bulala haka kuma baya hana anjima ko gobe su sake yin barna. Zaunawa ta yi a gurin ta fara kuka domin fushin da take na jiya ta farka da shi a yau wannan ya saka na ayyana a ranta ba zata fita ko'ina ba balle ace ta yi laifi, gashi bera ya cinye ayabar data aje, ya lalata sauran. MALEEK POV. Yana jin lokacin da aka kwankwasa kofar dakin, amman ya kasa amsawa sai juyi yake akan gado gaba daya yau ya farka jikinsa babu dadi kamar wani mai laulayi. Ya kusan minti talatin saman gadon yana ta juyi sannan ya sauko ya shiga bathroom yayi wanka da ruwan zafi mai zafi sosai wai ko zai jidadin jikinsa ya fito ya shirya kansa sannan ya bude kofar dakin ya fita, kamin ya karasa saukowa ya aikawa mahaifiyarsa da gaisuwa domin baya son karasawa kusa da dinning dinta ma saboda kanensa da suke gurin, a ko wace safiya idan za a karya a tare da juna to ana rabawa ne ita ta yi breakfast dinta tare da yan matanta Twins Nimra da Namra shi da kanensa Mahmood su karya a dinning din Babansu. Can kasan makoshinta ta amsa masa ta kawarda kai daga barin kallonsa ta cigaba da cin abincinta, a yanzu kokari take ta sabawa kanta da sabuwar dabi'ar yaye Maleek a zuciyarta, so take ta saba da halayensa da dabi'unsa so that ta samu peace of mind, ta samu natsuwa ta cire shi da damuwarsa a ranta. Sai da ya fice daga falon ya shiga bangaren mahaifinsa sannnan Nimra ta tashi tsaye ta dauki jakarta dake gefenta. Ummi na tafi kar nayi latti To a dawo lafiya Hajiya Zahra ta fada ba tare da ta kalleta ba, fuskarta da muryarta suka kasa boye damuwarta, Nimra ta zagaya ta dayan side din mahaifiyarta take ta yi hugging dinta ta sumbanci gefen fuskarta. Ummi we love you dan Allah ki daina damuwa Ummi ta dago ta kalleshi da murmushi a fuskarka, sai ta ji abun da ke tsaye a tsakanin kirjinta da zuciyarta yana sauka kasa kamar suncewar tayar motar. Na gode Allah daya ba ni ku, Allah muku albarka ya ba ku mazaje na gari A tare suka hada baki suka amsa da Ameen, sannan Nimra ta fice daga falon tana ta sauri kar ta yi latti. Maleek yaja kujera ya zauna yana murmushi ganin kanensa Mahmood da Mahaifinsa suna dariya. Ni na fada maka wannan ka bari idan aka siyo wannan dan wasan ka ga yadda zai gyara muku team Mahmood ya girgiza kai shi har yanzu be yardar team dinsa ya kasa ba. Babu wani gyara da zai mana, daman matsalar mu wannan couch din ne kuma yanzu mun sauya shi Ai idan kana neman team din banza idan ka kai ga Man U ka saka aya, ku Manchester United daga manyanku har kanana ba ku iya komai ba sar shirme, gashi ba ku iya cire kudi su siye manyan yan wasa, idan kana son team mai kyau Malam je Arsenal Cewar Maleek Abiey ya saka dariya, ba team din Arsenal yake ba amman yana supporting dinsu domin sun san abun da suke yi ba kamar Manchester United ba. Kuma Arsenal din idan aka cire manyan yan wasanku biyu sauran ba za su iya yin komai da kansu ba Haka suka yi ta gardama akan kwallo da yan kwallo kai ka rantse da Allah su kadai a gidan domin muryarsu kawai ake jin tana tashi a bangaren, ba su ba ba Mahaifinsu ba domin tsohon dan kwallon kwando ne, ya san in and out na wasanin da yawa na duniya. A take laulayi da dan bacin ran da Maleek yake ji ya washe fess daman haka yake so ya zauna yayi ayi hirar abun da ya shafi maza tare da maza yan'uwansa, ya kan ji sakewa da sukunin zuciya da nishadi kamar kar a rabu, mahaifinsa kuma ya fi kowa fahimtar abun da yake so wannan ya saka yake kokarin faranta ransa. AMEER POV. Me ya hada ka da Balarabe? Ya aje spoon din da yake cin abinci da shi ya kalli Momy ko be tambaya ba ya san ita ta fada, domin ita kadai ta san abin da ya faru kare da karau a gaban idonta aka yi komai. Tambayarka na ke Daddy ya fada rai a bace, sai kanensa suka kalli Ameer, ba za su ce basu saba gani ba sai dai ya zama kamar bakon abu ne a gurinsu Daddy yayi ma Ameer fada ko ya nuna masa bacin ransa akan wani abun ko da kuwa ran nasa be masa dadi ba. Aiki na saka shi yayi min shirme Shi ne zaka daga hannu ka mari babban mutum kamar Malam Balarabe? Ameer ya masa kallon mamaki domin a gurinsa ba wani abun ba ne. Daddy a karkashinmu yake Shi ya baka damar ka wulakanta shi? Daddy ya kalli Safna. Je ki kira Malam Balarabe Safna ta mike tsaye domin cika umarnin mahaifinta, Ameer ya bita ta kallo kamin ya juyo ya kalli mahaifinsa kamar yayi magana sai kuma ya saka hannu ya dauki spoon dinsa ya cigaba da cin abincin, Baba Balarabe ya shigo bakinsa kumshe da sallama, Daddy da Momy suka amsa masa ban da Ameer dake kara jin haushinsa har a yanzu. Ranka ya dade gani Daddy ya kalli Ameer fuska babu alamun wasa ya ce. Ba shi hakuri Not just him even Momy da kanensa sai da suka kalli Daddy with shock balle kuma da aka bawa umarnin. Hakuri Daddy for what? For marinsa da ka yi Baba Balarabe yayi fararat ya ce. Babu komai Alhaji, ai komai ya wuce tun jiya, hakurin da ka ba ni ma ya wadatar Daddy ya daga masa. Babu ruwanka a wannan maganar, Ameer umarni nake baka ka bashi hakuri na ce Wasu takwayen numfashi ne suka fito da gudu daga cikin Ameer suka fita ta hancinsa suka suka shiga da gudu kai kace wani yakin duniya ake a jikinsa, ba komai ba sai bacin rai. Baya son ya kunyata Daddy a dole ya bude bakin da halshe ke hadewa da hakori ya ce. Ka yi hakuri Daddy ya daka masa tsawa rai a bace. Say his name and ask for his forgiveness Ameer ya kalli Daddy yana jin kamar ba a taba wulakanta shi a duniya ba irin yau. Ka yi hakuri Balarabe Baba Balarabe
Chapter 7 · 0% Book details