Sashe 98
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
Waira ke yarinya ba ki san komai ba Ta tari numfashinsa. Na san komai, na san komai tun kamin Ummi ta fada min na san komai Ya kalleta Taya? Wannan dan iskan Maleek ya fada min ko? Ni bana hira da Maleek, he hate me shi ma kuma ni na fada masa, na sani ne ssboda ina iya sanin abun da ya faru da mutum This time around dariya yayi. Waira kina tunanin kin fini wayo? Kina iya sanin abun da zai faru miyasa kike tambaya waya koya min busa? Be zama lallai ka sani ba, amman idan na rumgume ka zan iya sani Then what are you waiting for? Stop the car Ya samu guri ya faka gefen titi sai ta bude gefenta ta fita ta zagaya inda yake ta bude masa. Fito Samun kansa yayi da bin umarninta ya fito daga motar, sai ta rumgumeshi ta rufe ido, saman kanta yake kallo hannayensa na zube a muhallinsu, ta kai minti talatin tana rumgume da shi, shi be gaji ba kuma be saka hannu ya rumgume ta ba ko yace ta sake shi, duk kuwa da irin abun da yake ji. Ta dago ta kalleshi da kamar tsoro. Eid ya koya maka? Ta daga mata kai, ba dan yarda tana iya ganin past life din mutum ba. A garin da ka je karatu? Kana yawan busar sarewa amman baka iya mai kyau kamar nasa ba Maybe kin san shi, shi ya fada miki cewar ya koya min Be fada min ba, amman na san shi, shi an'uwa ne, na san da cewar shi kadai ya iya busar shiyasa nake mamakin yadda naji kana busawar Na ji wannan sai kuma me? Yau ka kade wata tsohuwar ka kaita asibiti A motata akwai jini maybe kin ga jinin ne, cewa tsohuwa ce kuma wannan kin canka ne kawai, look Waira ke da Ummi ba za ku iya wasa da kwakwalwata ba Ya juya zai shiga sai ta ce. Ranar da Ummi ta fada maka ita ce mahaifiyarka, ka tafi gurin wata mata Humaira, ka fada mata damuwarka. Jiya kanwarka Fiyya ta shiga akinka ta yi magana da kai, kamin ka zo nan daga office kake. Kana shirya yadda zaka bar garin nan ka koma wata duniyar da babu wanda ya sanka ka zauna, ranar da Nimra ta mutu ka zo nan da dare, sa safe ma ka zo, da kai aka kaita makabarta, kuma shi ne zuwanka na farko, wannan shi ne karo na farko da wata ta yi hatsari ka tsaya ka dauketa ka kaita asibiti kuma har ka sakata a motarka, kamin ka zo nan kaje gurin wanki mota, sai ka yi tunanin za su yi zargin ka kashe wani sai ka fasa bada wanki ka zo da motar a haka, kana son ka tambaye ya aka yi na zama haka ya aka yi na iya hausa, ka taba ganina a school bus a lokacin da baka gane ni ce ba, ni kuma ban ganka ba..... Haka ta rika zayyano masa abubuwan da suka faru da bata sani ba, da kuma wadanda ya san be yi maganarsu da kowa ba sai kansa. Tana fara maganar ya juyo yana kallonta da tsananin mamaki har ta kai aya. Ya aka yi kika san haka? Wannan shi ne sirrina da ban taba fadawa kowa ba, ina ganin rayuwar da ta faru, ta haka ne na gane Ummi tana dauke da cutar leukemia, ba tare da ta fadawa kowa ba, ta haka na gano yadda take ta boye soyayyarka a zuciyarta, na gano damuwarta na son rayuwa da kai ni na fadawa Iyalanta tana dauke da cutar da take stage 3 Duba kike yi? Bana duba, al'adar garinmu kowa yana irin baiwarsa ta tsafi ne, sai dai ni tawa ta sha banban da saura, saboda ana jiran na kai wasu shekaru ne a ba ni sarauta ta sarauniyar matsafa da garin, sai kuma gashi na gudu saboda an zarge ni da kashe kashe wani, alhalin ban aikata ba? Me yasa ba ayi amfani da tsafin an gano ba ke kika aikata ba? Ban tsaya jiran a gano ba, na gudu saboda bana son sarautar kuma a dokar da aka saka min idan na gudu kashe ni za'ayi Hawaye ya sauko idonta. Ina iyayenki suke? ba ni da iyaye, duka sun mutu, ni kadai nake rayuwa a cikin wani daki, tare da beraye da zakaru, ban san wani abu dadi bachi ba sai da na zo nan, ban wani ya kira da ya ba sai da Ummi ta kira ni, ban san gatan da dadin dake cikin wanka kullum ba sai a wannan duniyar, ban san saka wani tufafin a kullum ba sai a nan, tun ana yi min da karfi, har na fara yi da kaina saboda na saba, a yanzu ko wane dare sai na yi wanka na wanke baki nake kwantawa, tsabanin can da ban san wani abu tsabta ba, ni da iyayena suka mutu sun tafi sun bar ni a cikin wata kazamar rayuwa, ni ce bana son tsabta bana son wanka saboda ina ganin hakan shi ya fi min, kuma ni zan iya mutuwa a kowane lokaci saboda na san ba za su kyale mu ba, ni da Ummi duk mutuwa muke jira, ita tana son ta gyara komai kamin ta tafi, tana son ta rabe ka ka kyautata maka, ni kuma bana son komai sai dai na san bana son mutuwa Be san lokacin da ya rumgume ta ba, ya lumashe ido hawaye suka zubo masa. Sai ta fashe da kuka sosai. I can take you back, zan maida ke inda na dauko ki, zaki nuna min hanyar garinku, zamu tafi tare mu roki yafiyarsu Ba zan gane hanya ba, sun bata da komai a kaina, wanda ba dan garin ba, ba zai shiga garin ba, ba za su yafe ba, ba za su saurari kowa ba, ba zaka iya ba Zan iya Waira i will do this Ya sumbanci saman kanta. Ni dai ina son, kamin na mutu ka zauna lafiya da Ummi, ita tana sona sosai, ita ce ta zama min uwa, a gurinta na san abun da a take ji idan uwarta tana raye, ta ba ni duk wani jindadi bata kyamata tun ina da kazanta, ina son ka yi rayuwa da ita lafiya, ina son na ga haka kamin na mutu ko kuma ita ta mutu, ina son farincikinta, Ameer ko wani dare na gani tana kuka saboda kai, tana kaunarka sosai tana son kasancewa da kai, kana da iyaye ai kai Ameer ba zaka taba sanin dadinsu ba har sai basu da rayuwa, na yi mamarin nawa, idan ina son ganinsu sai da na rumgume danginsu na ga hoton fuskarsu na ga rayuwarsu i miss them Ya dagota daga jikinsa ya sake hannunsa biyu ya share hawayenta. Ba zaki mutu ba, babu abun da zai same ki, na saka taimakonki a lokacin da ganki a daji, yanzu ba zan ki taimakonki ba Ta daga kanta tana kallonsa. I won't hurt anyone anymore, domin ban san ta inda zan fara neman gafara ba i regret what i did to Nimra i wash... Then don't hurt your mother, karka dawo ita ma kana nadama a lokacin da bata nan, we're all making mistakes, kowa yana yin kuskure muna yin ba daidai ba to miyasa idan wasu sun yi ba daidai ba ba zamu yafe musu ba? Yayi murmushi yaja kumatunta. You're so brilliant Ta yi murmushi tana kallon cikin idonsa da blue eyes dinta. Zaka yafe mata? Yayi shiru. To zaka so ka zauna da mu? Wannan kam a take ya amsa mata. No no Please bana son ka bar ni, ni bana da dangi a yanzu kai ku, mutumen da nake so rasa su nake, kuma ka ga ni ba dadewa zan yi ba idan na mutu sai ka tafiyarka Wayo kike min Waira you're just building a room for Ummi I'm building a room for all of us, ina son mu yi rayuwa a gida aya, kamar iyali daya a gidan nan Nimra ce kawai take so na sai Ummi da Mahmood, Ya Maleek baya so na, Abiey ma baya so na, na rasa Eid, da Sulem i don't want to lose you too You wouldn't, idan kina so zaki iya magana da Ummi ki dawo gidanmu da zama Me yasa kai ba zaka zauna a gidan Ummi ba? Why do you hate her Saboda ba zan iya zama karkashin inuwa aya da Maleek ba, ba zan iya zama a gidan mahaifinsa ba Ta kama hannunsa. Please Ya rike hannun nata yana murzawa a hankali. Kamar daga sama suka ji muryar Maleek. Ke Waira Ta zabura ta juya da sauri tana kallon inda muryarsa ke fitowa, Ameer kam ko dago kai be yi ba balle ya kalleshi kuma ya ki ya saki hannunta duk kuwa da irin kokarin da take tana son kwace hannun. Ummi ta bude mota ta fito ta biyo bayan Maleek da ya nufo inda Ameer da Waira suke tsaye. Maleek Maleek bari na yi magana da shi Shi ne abun da take fada tana kokarin rikowa shi domin ta lura da yadda ransa yayi matukar baci. Daman na raya a zuciyata kai ka dauke ta, tun da muka je makarantar aka ce mana wani ya zo ya tafi da ita, na raya kai ne sai gashi ina duba details din abun kuma sai na ga kai din ne Ameer ya saki hannun Waira ya kalli Ameer fuska kamar bakin hadari. Me ye a abun kunya? Biyo yarinyar da ka tsana har makaranta da sunan daukarta, ko kuma tare abokinka a hanya kana fada masa maganar banza a lokacin da mahaifiyarka take kokarin hanaka? Thank you ka ce Mahaifiyata ashe ka san bata cancanci zama uwar kazamin yaro irinka ba Sai kuma gashi ta haife ni, ya ranka? Fessss haihuwarka kawai ta yi bata amsa sunan mahaifiyarka ba Ummi ta dakawa Maleek tsawa. Maleek ina ganinka kamar mai hankali? How could you say those words to your own brother? Ameer yayi murmushi yana kalleta. Karki damu, Maleek be taba zama an'uwana ba and he wouldn't be, he is just a friend shi ma kuma a can da Ameer ya maida