← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 165

Sashe 115

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

domin ita ta rasa yar'uwa bata da abokin shawara a yanzu Ya kamata ta girmamani then Zan yi magana da ita, amman kai ma ya kamata ka girmama na gaba da kai, misali Abiey ko da ace ka girme shi ya kamata ace ka girmamashi saboda yana aurena, amman da rana daya baka taba zuwa ka gaishe shi ba, na ga ko ba komai ya girmeka ai kuma ya haifi kamar ka, sannan yana aurena Ameer ya hade yawu. Shi ma be taba kwatanta zuwa ya dubani ba a bangarenki, tun da na zo gidan nan ban taba ganinsa a bangaren nan ba, be shigo ya tambaye ya nake ba, idan Maleek ne ko Mahmood zai masa haka? Hajiya ta fada min komai akan Abiey irin kiyayyar da ya nunawa mahaifina, hakan ma sai ya saka na kara yi miki uzuri wata kila yana daga cikin mutanen da suke cilasta miki rabuwa da ni, Hajiya ta fada min Abiey baya son mahaifina ko kadan, wata kila kiyayyar mahaifina ce ta shafe ni nima ya tsane ni Ummi ta masa duba irin na mai rauni ta girgiza kai tare da kai hannu ta shafa fuskarsa. Ba zan ce Hajiya ta maka karya ba, amman iya sanina tsabani da rashin fahimtar dake tsakanin Abiey da mahaifinka irin wadda aka saba samu ce gurin samarin dake takarar neman aure, babu abun da zai saka Abiey ya tsane ka, idan har Mr Bashir zai kaunace ka alhalin be hada komai da kai ba, to ko Abiey ya fi dacewa yayi maka wannan kaunar saboda yana auren mahaifiyarka Ameer ya mike tsaye. Ummi kar mu bar Humairah tana ta jira Ummi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta mike tsaye suka fice daga dakin, ita ta sauko kasa shi kuma ya nufi dakin Waira, domin tun da ya shigo be ji motsinta ba kuma ya san ba time din zuwa makaranta ba ne balle yace ta tafi school haka ma idan ba ta school bata zuwa ko'ina. Slowly ya murda kofar ya tura, tana zaune akan stool tana kallon kanta a madubi ta juyo ta kalli kofar ganin Ameer ne ya saka ta murmushi. Shi ma murmushin yake yana takawa a hankali har ya isa inda take ya jingina da madubin. Fuskarki bata bukatar kwalliya Waira, Allah yayi miki hallitar da zata wadace ki ta gamsar da duk wani namiji mai kallonki Ta kai hannu tana gyara gashin kanta dake cushe cikin jar hular sanyi da Maleek ya bata. Rigar nan nake dubawa da hula ta min kyau ko? Ya kalli rigar jacket din ta mata kyau sosai even though ta mata yawa, balle kuma hular da ke yi duk wani farin mutum kyau. Sun miki kyau, Ummi ta siya miki? Ta rika rigar ta kai masa a hanci. Kamshin waye yake yi? Perfume din yayi masa kama da wanda ya taba ji, but ba zai iya fadar wake kamshin irin perfume din kai tsaye ba. Ya Maleek mana, shi ya ba ni rigar da saka min hula saboda na ji sanyi, Ummi tace naje na kaiwa duk wanda na gani a falo yayi min assignment sai na kai masa shi ne ya ba ni Cikin zumudi da jindadi marar misaltuwa take fadawa Ameer haka, ita dai yau kam Maleek ya burge ta kuma ya biyata duk wani kallo na mugunta da take masa yau ya kau a idonta saboda ya bata riga ta saka, ara mata yayi ko kuma bata yayi duk bata da tabbacin ko daya, sai dai tana jin cewar ya nuna mata kulawa hakan kuma ya saka ta farinciki. Kamar an yi ruwa an dauke haka murmushi yayi batan dabo a fuskar Ameer. I'm just joking rigar bata miki kyau ba, wannan ma kayan maza ne ba na mata ba, kuma sun miki yawa be kamata ki saka ba, sannan kuma bana son ganin komai a jikinki ko a maganar matukar ya shafi wani namijin ba ni ba Yana maganar yana kicin-kicin cire mata rigar, ita dai hular tuni ya cireta ya jefar. Sai ta kamashi da kokawa tana son hana shi cire nata jacket din. Ni ina son abuna haka karka cire min Haba Ameer yana min kyau na gani, ina son kayan mazan haka, ya nuna min kulawa ne kawai fa, duk wani abun kyautatawa da Ya Maleek zai min ina so i like it Cak Ameer ya tsaya daga kokarin rabata da rigar da yake ya dauke hannayensa, ba dan kukan da take kawai ba har saboda furucin da ta yi masa a yanzu. Ita kuma bata fada da wata manufa ba sai dan abun da ta fahimta kuma ta dade tana jira, wato ranar da Maleek zai daina hantararta da yi mata fada. Ba laifinki ba ne, na gane idan na yi wasa daga like it sai like him then love him, ina shuka wani zai girbe okay... Ya fada a ransa sannan ya juya ba tare da ya ce mata komai ba ya fice daga dakin, ita kuma ta tashi tana kuka ta nufi inda ya jefar da hular ta dauka tuna lokacin da ya cire nata zoben da Shuraim ya bata, shi kawai baya son ya ga an bata kyau. Yanayin yadda ya fito daga dakinta ya sauko kasa ya zauna a kusa da Humairah is something else, domin babu annuri a fuskarsa, ya hade rai kamar wanda aka yi ma bushara da bakin labari, zuciyarsa sai sake-sake take masa idan ta kwance masa wacan ta saka masa wannan. Duk wata hira da Ummi take da Humairah hankalinsa baya gurin, shi ya matsu ma Humairah ta yi sallama ya sanar da Ummi abun da yake ransa, domin ba zai iya jira sai gobe ko jibi ba, kawai ba zai iya jinkiri da jira ba, ba kuma ba zai iya hakuri da abun da Maleek yake masa na shiga hanci da kududdufi ba, ta ya zai kula Waira abun da ba muruminsa ba. Daga Ummi har Humairah sun kula da yanayinsa ba ma kamar Ummi da idan ransaya bace ko ta ga damuwa a fuskarsa take jin kamar an cire mata duk wani jindadi na duniya. Ummi ta saka Hanne ta kawo ma Humairah abinci sannan ta dauki wayarta ta kira Namra ta sauko suka gaisa, kana ta shiga dakinta ta yi mata goma na arzki daga kan perfume body spray da atamfa mai kyau, Namra kuma ta bata Veils har biyu saboda Ummi ta yi mata maganar ta bata wani abu a kokarin Ummi na ganin kowa ya kawar da abun da ke zuciyarsa. Ummi ta fito har balcony ta rakota tare da Namra da Ummi ta yi mata dole. Humairah ta bude mota ta shiga kamin ta rufe Ameer ya kalleta ya ce. Bari na kira Waira ku ga juna, ita ce kadai ba ku gaisa ba Namra ta taba baki kamar zata ja tsaki sai kuma ta juya ta shige ciki saboda gudun bata ran Ummi. Ummi muje ciki akwai maganar da nake son na yi da ke kamin na tafi, Maybe ba zan kwana a gidan nan ba yau saboda Daddy yace yana son na yi dinner a can shi ma yana da maganar da zai yi da ni Ummi ta amsa masa. Okay Sannan ta kalli Humairah ta ce. Allah ya kiyaye Humairah na gode sosai ki gaida gida Gida zai ji Ummi, ni ce da godiya Allah ya saka miki da alheri ya yaye miki damuwarki Ameer da Ummi suka hada baki gurin amsawa da Ameen. Sannan Ummi ta juyo suka shigo cikin falon, ganin Hanne na zaune a falon ya saka Ummi ta zarce dakinta kai tsaye yana biye da ita har suka hau sama. Idonsa sai ya koma gurin dakin Waira zuciyarsa ta raya masa yanzu tana can tana kuka ko kuma tana jin haushinsa. After sun shiga dakin Ummi ta zauna shi ma ya zauna sai shiru ya biyi baya, ita tana sauraren abun da zai fito daga bakinsa shi kuma ya samu kansa da jin nauyin furta mata kurinsa kai tsaye, wannan ne karon farko da yake jin haka, bayan kuma ya shigo da zimmar furta mata komai kai tsaye. Wata kila saboda tana ita ne ko kuma saboda Waira ce da ta banbanta da sauran mata a gurinsa, ya'allah kuma saboda wannan ne karon farko da zai gabatar da wata mace a matsayin wacce yake so da aure, amman zai iya ikirarin kunya ko jin nauyi akan komai ba halinsa ba ne. A dan zaman da yayi a gida da kuma experience irin na uwa mai a maza da mata ya saka Ummi fahimtar yana jin nauyi ko shakkar furta mata abun da yayi niya ne, lura da ta yi da yadda ya rike hannunsa yana matsawa kuma ya kasa daga kai ya kalleta. Hakan ya sakata tasowa daga inda take zaune ta dawo saman kujerar da yake ta zauna ta fuskance shi. Ameer maganar tana da nauyi ne ko hatsari? Ko kuma tana da kunya ne? Wani abu zaka bukata? Ko kuma wani abu zaka gabatar? Kar tunanin yadda zan karbi abun ya saka ka yin nauyi ko jin kunya gabatar da bukatarka, fada duk abun da kake so a duniyar nan matukar be tsabawa Allah ba, na maka alkawari zan maka shi, wannan duty na na uwa, wata kila da nan ma zaka yarda ina kaunarka sosai, ko wani ka kashe ko wani abu ka aikata karka ji nauyi ko tsoro fuskance ka fada min saboda ni Mahaifiyya ce, uwa kuma mai tausayin a ce kuma mai kaunarsu, balle kuma ni da nake da kai a matsayin a, dole zan sama maka mafita a duk inda take Kalamanta sun karfafa masa guiwa kuma sun masa dadi, ta haka ne ya dago ya dubeta duba na tsanaki yana murmushi. Ummi Sai kuma yayi shiru ya sake maida kansa kasa. Ummi... Daman... Ya kasa dago kai, ganin hakan ya saka ita ta kai hannu ta riko fuskarta ta dago ya kalleta Fada min me kake so Ameer duk abun da kake so zan maka shi a duniyar nan karka ji nauyin komai Ya rausayar da kai. Ummi akan Waira ne Ummi ta gyara zamanta irin na ina saurarenka. Ummi Daddy ya dade yana min maganar aure,
Chapter 115 · 0% Book details