Sashe 139
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
babu wanda ya saka tufafin da suka suturta jikinsu kamar yadda shi yayi ko kuma Nuwaira. Tun daga kan gine ginen garin zuwa abubuwan amfaninsu gaba daya Maleek be taba ganinsu ba, domin bw rayu a kauye ba balle ya san wasu abubuwa, haka ma ba dan da ba ne balle ya ce ya taba ganin yadda rayuwar baya take. Sai dai wani abun da ya bashi mamaki ganinsu tsab tsab ba kamar yadda ya fara atba da Nuwaira ba da kazanta, yayi zaton zai tararda kusan rabin garin da kazanta amman be ga haka ba. Duk gurin da suka ratsa kallonsu ake wasu na mamakin dawowar Nuwaira tare da wani, bayan an yi shelar ta gudu, wasu kuma na mamakin yadda ta sauya tufafin jikinta take tare da wanda ya aaka tufafin da suka banbanta da na su, ga kuma fatar jikinta dake sheki farinta ta fita fess kamar wadda aka sauyawa mata. A madadin ta bi hanyar gidan Sarki sai ta zabi dauke hanyar da dakinta yake, bangaren da take rayuwa a gurin da ta girma, kuma gurin da ta gudu ta bari, tna tafiya tana tunanin yadda rayuwa zata kasance mata ita da Maleek domin abu ne mai wahala ace Sarki ya yafe mata ita kanta da take yar garin balle kuma Maleek da ya karya dokar garin bayab yayi hayayya d Eid, idan ma sarkin ya yafe mata to zai tabbatar da mata da kudirinsa na bata sarauta ne, abun da take ta fargaba tun farkon tashinta, saboda ta san idan ta haihu mutuwa zata yi kamar yadda aka kashe iyayenta bayan haihuwarta, kuma addinin da ta sauya a yanzu ba zata iya aje shi ba, tufafin ba zata daina sakawa ba, haka ma abincin garin Garuk bata jin zata iya cinsa a yanzu, rayuwa a dakin kasa da babu wuta babu ac babu kujera babu babban gado, babu mai damuwa da tashinta ko bachinta anya zata iya a yanzu? Ina ne? Tambayar Maleek ce ta dawo da ita daga dogon tunanin da ya kwashe ta har ta iso gurin ba tare da ta sani ba. Gaba dakin ya kara lalacewa wani bangare na dakin ya rufga ciki, datti ciki ya karu daga ciki har wajen dakin kamar gurin zuba shara haka yake, sharar ma ta kazamai masu bari bola ba tare da sun tsabta ce ba. A nan na yi rayuwa, a cikin dakin nan na girma a nan makwancina yake, ci da sha na duk a nan suke abincina yayan itatuwa ne, zakaru da beraye ne abokaina Kusan mutuwar tsaye yayi yana kallonta, how come zata ce masa ta yi rayuwa a nan? Nuwaira ko dabobi ba za su iya rayuwa a nan ba balle mutum, ina danginki suke? A nan muna kalar rayuwar da ba irin ta ku ba, babu mai damuwa da danginsa, idan ka zabawa kanka yadda kake so rayuwa babu mai ce maka domin me? Ba a takura maka ka canja baka takura rayuwar wani ka ce sai ya canja. Shiyasa nake mamakin rayuwarku kuma na yi mamakin yadda Ummi ta karbi ta nuna min soyayya da kauna ta rumgume ni ta ana min dadin uwa Ya busar da iskar bakinsa a hankali be tana jin tausayin Nuwaira irin wannan karon ba, duk yadda yake tsammanin zai samu garinsu da rayuwarta abun ya wuce tunaninsa. Kuma a haka kike son dawowa? A haka kike son cigaba da zama a garin nan? Kalli yadda gurin nan yake Ta kalleshi tana hawayen tausayin kanta. To ya zan yi, ina da wani zabin ne? Amman yanzu kika gama ce min an idan wani ya zabi yadda yake son rayuwa babu mai hana shi Ba a ba mu wannan damar ba, mu ba a yarda mu aura daga wasu ko kuma wasu su aura daga garemu ba, ba yarje mana mu zauna a wani gurin mu yi rayuwa ta dindin bayan garin nan ba, sai idab wani laifin ka aikata aka koreka daga garin, balle kuma ni da idon kowa yake kaina Wannan ba gurin rayuwa ba ne Nuwaira, Sarkinku ya danne muku hakki da yawa, kokarin bin tafarkin iyaye da Kakanin ya hallaka rayuwarku, duk wanda zai so ki rayu a nan ba masoyinki ba ne, babu wanda zai iya rayuwa a nan Ni a nan zan rayu rayuwa a nan ya zame min dole, ba ni da wani zabi bayan wannan ba kowa yake sa'a da dacen rayuwa kamar ku ba Ya kai hannunsa ya saka yatsansa biyu tsakanin hancinsa ya cire hawayen da suka cika idonsa. Na ga hakan nima a yanzu, and Nuwaira you deserve a better life ya kamata ki yi magana ta fahimta da Sarkinku ki fada masa kin canja addini a yanzu kuma kina so ki yi rayuwa a wajen garin nan wata kila zai fahimta ya daga miki kafa Kashe ni zai yi ba a yarda wani ya canja addinin ba, wata kila kai ma ba za su barka ba kuma idan wani abun ya same ka sanadina Ummi ba zata yafe min ba, be kamata sanadiya wani abu ya same iyalinta ba Maleek ya nufi wani dutse ya cire talkaminsa ya dora akai ya zauna sai kallon dakin Nuwaira yake, even zama na kwana daya tunanin yadda za su yi shi a gurin yake, me za su ci? Da sha. Hijabinta ta cire ta daure a kugunta ta juya zata fita daga gurin sai yayi saurin mikewa tsaye ya saka talkaminsa ya bi bayanta, tafiya mai nisa suka yi sannan suka isa wani gida, bata cewa mutanen gidan komai ba ta shiga sai kalle kalle take har ta hango gurin da aka aje abun sha ta dauko ta fito ta dawo inda dakinta yake ta fara gyarawa and Maleek have no other choice but to help her, dan haka ya cire rigar shaddar dake jikinsa ya rataya a wani kamin ice dake gurin ya nade wandonsa ya sake jikin suka fara gyara gurin. AMEER POV. Safa da Marwa kawai yake a harabar gidan ya rasa abun da zai yi sai ware hannaye yake kamar mai shirin fada. Fiyya ta fito da gudu ta nufi inda yake An kira wayarka Tsayawa yayi guri daya har sai da ta iso ta miko masa wayar. Yana ganin sunan Humairah ya girgiza kai. Is she your girlfriend too? Tana tambaya tana sosa kai. An taba girlfriend biyu at the same time? Handsome man like you yana yi ai She's my cousin and you know it Yeah kawai tunanina ya bari wani abu ne, na ga tana sake maka sosai Shakuwa ce mun san juna da ita tun kamin hakan ya faru shiyasa yanzu sai muka samu fahimta daya, zuciyata Waira kawai take so for now Owkkkk ina dayan cousin din nan wannan mai share mutane? Ameer ya dan yi shiru alamar tunani. Sai ta tuna masa Wannan da kuka yi fada That's friend of yours sa kuka yi fada before Oh Maleek Yeah he's hot amman yana da girman kai sosai idan am masa magana ba ya respond Kin taba masa magana ne? Eh amman be amsa ba, but he's handsome yana da kyau Ameer ya daga mata gira daya sai ta rufe ido tana dariya ta nufi hanyar part dinsu. Da kallo ya bita yana murmushi sannan ya yi dialing number Humairah domin kiranta na biyu ya shigo ya yanke. Ringing daya ta yi piciking. Hello Hello How are you? Ya tada kansa ya kalli sama. Not fine? I don't know ko dan Waira bata kusa da ni ne, ko kuma ina tsoron rasata ne ban sani ba, but I'm not fine jikina yana min wani iri Ameer I'm sorry ni ban fada maka magana a wacan ranar saboda na yi maka baki ba, kuma ba fata nake maka ba it just that bana ji dadin yadda idonka yake rufewa ka aikata abubuwan da zuciyarka take so ba tare da tunani ba Hey disturber ba laifinki ba ne, kawai kin fadi abubuwan da suka zo bakinki ne ba tare da tunanin haka zai faru ba right i know ba zaki so wani bad abu ya same ni ba haka ne Eh Ameer kullum fata na gari nake maka kullum burina ka zama mutumen kirki abun alfahari ne Na sani, kuma na fara dauka hanya but still akan Waira ina jin.... Sai kuma yayi shiru shi dai Allah ne shaidarsa yana sonta irin son va zai iya karantawa kowa ba. I know saboda na canja wasu hallayarka Ameer kuma na jidadin haka, and ina maka addu'a Allah ya zaba maka abun da zai fi zama alheri a rayuwarka kamar yadda nake rokawa kaina, and Ameer ina son na roke ka wani abu zaka yi min? Fadi duk abun da kike so Humairah zan miki, babu wani abun da da zaki bukata ban miki ba, you're more a sister to me ina jinki kina da muhalli mai girma a zuciyata Ta yi dariya tana jindadin. Ni ma na yi tunanin haka, shiyasa tun farkon haduwar mu na kasa tsoronka kamar yadda kowa yake yi, kuma na kasa daina fada maka gaskiya Shi ma dariyar yayi yana tuna some parts of rigimansu. Da ace zan kaiki kara kotu zaki biya kudi da yawa, saboda ke kadai ce mace da take takura min a back then, and you're the only girl da zata kalli ido ta fada min magana son ranta kuma na kasa yin komai kina da wannan power har yanzu I wish i have many powers over you Come on fada min me kike son rokona? Alfarma zan nema kuma ina son ka yi miki alkawari, na san kana son Waira so mai tsanani amman please ka yi min alkawari ba zaka tana barin sonta ya saka ka aikata abun da zai cutar da wani ba, ko da kuwa kaine, and please kar sonta ya lalata alakarka da kowa kuma kar sonta ya hana ka bawa Ummi kulawa da nuna mata kauna ko yi mata biyayya I won't i promise you, but abu daya ne ba zan iya miki alkawari ba shi ne hana kaina zuwa gurin da zan ganta, domin a yanzu ma da ban ganta ba na damu sosai Me yasa zuciyarka zata damu da wadda bata damu