← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 165

Sashe 17

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

sauri kamar mai neman gurin boya haka ta rika jin abun na mata yawo har sai da ya zagaye jikinta ko'ina sannan ta ji yayi kasan cikinta. Da wani irin karfi da bata san tana da shi ba ta tura Eid ta fara dukansa babu kakkautawa. Me ka saka min a jiki me ka yi min? Eid me ka yi min me ye wannan abun nake ji? Hannayenta ya rike ya juyar da ita ya matseta a jikinta sosai ta bayanta har sai da ta natsu sannan ya sake ta. Kin san ba zan cutar da ke ba ko? Bata taba jin tsanarsa a ranta irin yau ba, gaba daya ya gama canja mata tsarin daren yau da take jinsa da nishadi, ya jagula mata lissafi ya bata mata rai. Wani irin huci take kamar zaki tana masa wata hararar da shi kanshi ya san sai ta dauki lokaci kamin ya su shirya. A gurin ta bar shi tsaye ta dawo dakinta ta kwanta tana ta jin haushinsa a ranta, shi kuma ya kasa tafiya ya kyaleta sai ya dawo bakin kofar dakin ya zauna ba tare da ta san yana gurin ba, sai da ya tabbatar da ta yi bachi sannan ya leka dakin, da idonsa ya haska fuskarta, bakinta a cige yake ta rumgume hannayena irin na masu fadan nan. Wani abu mai kama da ulba ya fito daga kafafuwanta Eid yayi tsaye yana kallonsa har ya fice daga dakin, sannan ya koma ya zauna kamar mai gadinta, be bar gurin ba sai da sanyin safiyar asuba ya fara sauka. Waira kuma bata farka ba sai da rana ta hasko dakin nata da wata bolar zuba shara ta masu kudi ya fita. Ba musulma ba ce balle alwala da sallah ya zama abu na farko da zata fara yi, ba mai tsabta bace balle wankr baki ko wanka ya zame mata dole, haka ta fara lalaben abun da zata ci, babu komai a cikin akushin dake dakin, ganin bata samu komai ba ta nufi gurin da zakarunta suke ta leka ramen bera ta dora hannunta a bakin ramen, da gudu bera uku suka hau hannunta, sai ta saka daya a cikin gashinta dayan kuma a cikin aljihun walkinta na dama, daya daya rage ta saka shi a na hagu sannan ta fita kafarta babu talkami daman can bata da su gaba daya ko ma akwai bata damuwa ta saka, wata mahaukaciyar rayuwa take da babu mai burin yin irinta. Waje ta fito gaba daya ta murza idonta so that ko da akwai kwantsa ta fita ba tare da ta wanke ba, gurin da ta saba zuwa ta ci yayan itatuwa ta nufa kamin ta karasa ta hango mutane sun doso inda take da sauri irin na wadanda aka bawa umarni, ganin haka ya saka taja ta tsaya domin mutanen na gidan Sarki ne dakarunsa ne ba gama garin mutane ba, ko ba a fada mata ba ta san laifi ta yi domin ba kasai Sarkin zai sa a kirata ko zo masa da ita ta sunan su gaisa ba sai idan ta yi laifi. Fada ta yi kira, Sarki yace a zo da ke Bata ce musu uffan ba, ta kai ta taba hannunsa in 5 seconds ta ga abun da ya faru a fada kamar a gabanta aka yi komai. Ban kashe shi ba Mu yan aike ne kawai Dayan ya amsa mata, sai ta yi baya baya alamar ba zata je ba, domin zuciyarta bata raya mata komai sai cewar ita ma kasheta za'ayi kamar yadda ta ga gawar saurayin da yayi mata magana jiya a fada matacce. Kai ta girgiza musu alamar ba zata je ba, su kam daman can musu da jayayya ba na su ba ne sai abun da Sarki ya fada, sai suka juya domin sanar da Sarkin yunkurin Waira na cewa ba zata je ba kamar yadda ta yi musu alama. Waira na ganin sun bace sai ta juya ta fara gudu zuwa bayan gari can gurin manyan duwatsun da Eid ya taba kaita, tana gudu tana kuka har ta isa, sai da ta isa ta boya bayan wani dutse tana tuno abun da ya faru jiya, sai ta sake fashewa da kuka, a rayuwarta babu abun da ta tsana kamar mutuwa, domin ta san duk wanda ya tafi be dawo ba, kuma ta san halin Sarki da tsananin hukunci kuma ba ya yafewa kowa musamman idan zalinci ne aka yi. Mikewa ta yi tsaye ta fara tafiya tana sauka ta gafen garin tun tana yi a hankali har ta fara sauri tana hadawa da gudun, duk da ita da kyamar ruwanta sai gata ta saka kafarta ta gafen da ruwan be da yawa ta tsallaka ta fara ratsa dajin dake gurin tana gudu, har da faduwa take ta tashi ta jefa kafarta can ta cire ta saka a nan bata damu da ciwon da ta ji a kafa ba ita dai burinta ta bar garin gaba daya.... EID POV. Eid dake tsaye cikin fadar yana jiran Dakarun Sarki su dawo tare da Waira da Sarkin ya ce a zo da ita ko ta halin yaya bayan sun shaida masa abun da ta fada. Ya daga kafarsa da ya ji tana masa mugun zafi alamar jin ciwo ko taka wani abu, yana dubawa sai ya ga jini. A take hankalinsa yayi matukar tashi. Waira... Ya furta numfashinsa na karo da juna, juyawa yayi da sauri domin zuciyarsa na raya masa dakarun sun ji mata ciwo a kokarinsu na kawota, sai tukunyar layun mai cike da kayan tsafi dake fadar ta fado ta fashe, ba shi ba gaba daya yan fadar mikewa suka yi tsaye har Sarki suna kallon tukunyar domin fashewar tukunyar na nufin wani babban lamari. A take Sarkin ya saka a fara bincike abun da ya faru, tsohuwar dake gaban tukunyar ta mike tsaye da sauri ta fara guda da halshe da ya rabe biyu kamar macijiya, ko'ina na fuskarta wuri ne aka yi mata ado da shi ba kuma ado irin na kwalliya ba, ado ne na tsafi domin sai da aka tsafe wurin sannan ta saka su a fuskarta. Yau dandanon azabar rai ta tabbata ga mai butulcewa Sarki, mai gudu ya bar garin tsafi, mai yunkurin karya dokokin garin Garuk, yaryaryar...... Karkarkar.... Farfarfar Waira ta gudu kafarta ta taka wata kasar da ba ta garin nan ba, hancinta ya shaki iskar da ba ta garin Garuk ba, lelelelelelelelelelelelelelelele hasara ta tabbata ga tsatson Kusan.... Tsohuwar na maganar Eid na jin zuciyarsa na rawa kamar zata fado tsabar tsoro da zuwan labarin ba ga tatatan, a take ya ji yawun bakinsa sun kafe kansa ya fara tsawa, kamin ya ji kamar bakinsa ta bugu wani abu, sai jini ya samu hanya. Hannu ya kai ya taba bakin ya duba sai ya ga jini, ya juya da sauri sai Sarki ya daka masa tsawa. Waira ta tsallake iyaka, babu wanda zai je ya dawo da ita, babu wanda zai taro ta, wannan doka ce, ita zata dawo da kafarta Sai da suka fadi kasa kamar za su masa sujada domin girmama umarninsa da nuna tsantsanr biyaya a gareshi, ban da Eid dake tsaye yana kallonsa domin ya san hukuncin da Sarki ya shar'anta idan har ta bar garin kasheta za'ayi. AMEER POV. Ko da aka yi azahar ya bar garin Abuja, gudu yake kamar wanda baya son ransa, yana overtaking any how irin shi ya shiryawa mutuwa a yanzu saboda mahaifinsa ya bata masa rai. Sai da ya isa Kano sannan ya rage gudun da yake, ya shiga wani Shagon siyar da kaya dake bakin hanya, yana dubawa ko zai samu tufafin da za su masa, wani kallo tsana yake yi ma tufafin domin ba a'adarsa ba ce saka tufafi mai karamin kudi, duk wani abu da karamin mai arziki ko talaka zai iya sakawa sai ya ji cewar ba sa'arsa ba ne. Hakan nan dai ya daure ya siya kayan da suka ci kudin da ya kai 20k riga da wando, sannan ya fito ya shiga wani Babban shago ya siye biscuits da lemu sai ruwan da ya san za su ishe shi har ya isa inda zuciyarsa zata raya masa. Ina zan samu Carpet a nan? Ya tambaya daker domin mutane haushi suke ba shi, wani yayi masa kwatacen inda zai samu carpet dai ya nufi can ya siye karamin Carpet domin ba su da na sallah, shi kuma be ji zai iya sallah da na Nimra da ya gani a motar ba, domin be dan waye yayi sallah da shi ba. Cikin garin Kano ya shiga ya sauka a wani babban Hotel da dollars yayi amfani ya kama daki, bayan ya bada key din motar Nimra da sunan a bada masu wankin mota na Hotel din su wanke masa ita saboda kyamar ta take tun da ya kamo hanya, duk kuwa da kasancewar be ga wani abun kazanta a ciki ba, sai dai taba sitiyarin da Nimra ta yi shi kuma ya bata yana jin kyamar kansa domin be san iya abun da ta taba ba kamin ta tuka motar bayan ita be sani ba ko wani ya tuka motar ma. Yana shiga tufafin jikinsa ya fara cirewa ya shiga be yarda ya taba tawul din dake Hotel din ba, shi dama be tana amfani da kayan kowa ba sai na shi, idan zai yi tafiya be san wahalar neman komai ba sai dai a hada masa, har Hotel ko gidan da zai zauna nema masa ake, haka ya shiga dakin wanka yadda zai kai hannunsa ya taba shower ma wani abun kallo ne, domin kyamar komai yake na Hotel saboda sanin da yayi kowa zai iya zuwa ya kama dakin ciki har da kare da akuya da tinkiya ko jaki. Miyasa Daddy zai min haka Ya fada yana jin duniyar ta juye masa gaba daya saman ya dawo kasa, kasan kuma ya koma sama, yamma ta zama kudi arewa ta zama yamma, ransa be kara baci ba sai da ya shiga wankan ya tuna be siyo soap ba, wani mugun tsaki yaja ya ji kamar ya fashe komai dake cikin bathroom din, a dole ruwa kawai ya watsa ya wanke jikinsa yayi alwala ya
Chapter 17 · 0% Book details