Sashe 12
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta zo ya hada ka da abokinka? Ko kuma abun da ka aikatawa abokinka? Momy ma kallon Daddyn take tashin hankalin da ta gani a fuskarsa ya daga mata hankali sosai, ta dade ta sanin cewar Ameer yana gwada aron hannu sai dai ba damar ta fadawa mahaifinsa gudun kar ta hada su ko kuma yayi zaton tana yi ma ansa sheri ne. Daddy ya nuna kansa. Kwarin idonka ya kai ka kalleni ka fada min cewar kana da budurwa sheke aya? Dukanin arzikin da na baka na nufin ka lalace ba, amman kullum sai ka saka ni ciwon zuciya, a kullum ina nuna maka abun da kake be dace ba amman ka kasa fahimtar hakan, tun kana dauko kanana har ka fara dauko mana magana Ameer ya mike tsaye yana kokarin danne bacin ransa. Daddy wannan abun da na aikata har ya kai ka fada min magana marar dadi kamar wannan? Simple abu? Ashe wani ba zai iya taba ni na gudu bayanka na buya ba Zaka iya only idan kana sa gaskiya, bana son zalinci bana son cin mutunci da rainin wayo, ka wuce mu tafi gurin CP yanzu nan, kuma karka kuskura amsa cewar ka aikata laifin nan Daddy ya fada yana nuna shi da yatsa, domin ya san karamin halinsa ya amsa laifin a gaban kowa a kokarinsa na nunawa duniya cewar shi baya tsoron kowa ko kuma babu mai iya hukunta shi. Ameer ya kalli Daddy kamar yace wani abu sai kuma ya juya ya fice daga falon rai a bace. Motar da ya shigo ya sake shiga yayi mata key Daddy na jin karar tashin motar ya san ansa ba zai bi umarninsa na zuwa inda ya bukata, wani kulikulin bakinciki ne ya taso masa har sai da ya fadi kan kujera zaune. Ba mu yi ma iyayenmu haka ba, kullum muna gudun bacin ransu, tarin dukiya da yawan gata be saka mun lalace ba Momy ta matso kusa da shi tana kokarin kwantar masa da hankali. Zamani ne ya zo, wasu abubuwan da baka tana ji ko gani ko zato ba za su faru, wani abun jarabawa ce dole sai ka yi hakuri zaka iya ci, dan Allah karka saka komai a ranka, shi ma na san anjima kadan zai sauka ya gane kuskurensa Daddy ya lumshe ido ba tare da yace komai ba. Yanzu ka samu kashe wannan wutar, da alama shi ma yaron da ya tsokano dan manya ne shiyasa har CP ya aiko maka da police har cikin gida, idan ba haka ba ba zaka san ma an kashe case din ba Ya amsa mata kai yana jin yadda zuciyarsa take masa mugun ciwon, irin ciwon da ta saba yi masa tun kamin ya samu Ameer. A gurin da ya koyawa kansa zama ya nufa, ya isa gurin a lokacin da wata zuciyar ta jika da jiransa, gaban motar Nimra ya faka motarsa sannan ya fito motar ya nufo inda Nimra take jingine da motarta fuskarta ba yabo ba fallasa ba kamar yadda ya saba yi ganinta da far'a ba. Tsaye yayi ya kasa ce mata komai, he need someone to talk to amman ba ya jin zai iya fara yi mata magana sai dai ita ta yi masa. Tun safe nake a nan Ta fada tana kallon harabar cikin wani yanayi da ya fi kama da na damuwa. A gogon hannunsa ya kalla 12pm da mintuna ya gani, ya saka hannayen nasa aljihu yana wani shan kamshi. Why? Ta kalleshi a karon farko. Daman na saba zama a nan, saboda guri ne da babu hayani sosai, kuma babu mutane da motoci idan kuka kake son yi zaka yi kuka babu mai ce maka domin me? Idan kuma nishadi zaka yi duk zaka iya yi a nan, na saba na kan zo wani lokacin da kawatau zauna a nan mu ci wani abu ko mu yi hira, kamar yadda ka tararda muna ci abincin a farkon zuwanka gurin nan Ya daga kai yana karewa gurin kallo. Mi ke damunki? Ban sani ba, tsoron rasa mahaifiyata ne ko kuma damuwar da an'uwana ya shiga ne? Na matukar son family na, musamman mahaifiyarmu ko kadan bana son na ganta a cikin damuwa, damuwarta tana haifar min da tashin hankali, wani lokacin sai na rika jin kamar zan iya rasata idan na rasata ya zan rayu? Ummi tana yawam shiga damuwar da bata fadawa kowa, tashin hankalin da na gani a cikin idonta a jiya saboda yaya da kuma halin da yayana ya shiga ya saka na tashi ina jin wani yanayi na dabam A karon farko ya jingina jikin motarta ba tare da tunanin kar tufafinsa su kwashi datti ba kamar yadda ya saba jin tana cikin damuwa ya saka ta sa damuwar nisantar ruhinsa. Akwai ta inda zan iya taimakawa? Murmushi ta yi. No... Karka damu komai ya wuce a yanzu, fada min ya kare da abokinka? Kamar baki cikin yanayin da ya kamata mu yi wannan hirar, but na yi nasara kuma ina daf da sake yin wata nasarar, but yau din ma an sake mata min saboda shi Waya bata maka rai? Daddy na Karka damu da sannu zamu ga bayansa da yardar Allah, duk makiyin da ya saka mu gaba sai mun ga bayansa Ya daga mata gira Yeah... Tare da yin murmushi mai sauti kamar ba shi ba, ita ma ta yi murmushin tare da busar da numfashi. ...WANI GARI... _Na Khadeeja Candy_ BARKA DA SALLAH Allah ya maimaita mana ya karbi ibadun mu, Ameen. MALEEK POV. Maleek ya hade carpet din da yayi sallah da shi ya mike tsaye ya juyo ya kalli Mahaifiyarsa dake cikin shirinta na fita. Ummi da zaki taimaka ki fita a maganar nan, tsakanina da friends dina ne? Friends...? Ummi ta tambaya tana matsowa kusa da shi da wani irin mugun kallo. Maleek har kana da karfin halin sake kiran mugayen mutanen nan friends dinka? Maleek kasan abun da abota take nufi? Abota na nufin mutanen da za su tsaya da kai a lokacin da kowa ya guje ka, ku fadi tashi ku tashi tare, ba mutumen da zai cutar da kai ko a hada kai da shi a cutar da kai ba, kamin na haife ka na yi wata awa wanda na gudu da cikina na farko na tafi garinsu na boya, kuma ta bani mafaka a lokacin da nake tsananin bukatar mafakar, na ji ciwo na kwanta asibiti ta kwanta tare da ni da yi jinya ta har na samu sauki, idan na fada mata sirri na ce bana son kowa ya ji ba zata fada ba, wannan ake kira abota, ba mai cutar da kai ba... Cikin fada take masa maganar, sai ya jefar da carpet din saman gadonsa ya kalleta. Ummi kin taba haihuwa kamin ni? A take sai ta ji kamar ta kwancewa kanta zane a kasuwa, tsoron kalar amsar da zata bawa danta Maleek ya maye gurbin bacin ranta. Cikinka nake nufi..... Ta furta murya na rawa tare da dauke idonta daga barin kallonsa ta juya ta fice daga dakin. Iskar bakinsa ya juya fuskarsa gurin wayarsa dake ringing. Dawood Ya fada sannan ya karasa ya dauki wayar ya danna picking. Hello Maleek ya ne kana lafiya Ya fada kansa Lfy Kalau for now Muna tare da Abdull zamu zo gidanku yanzu nan No karku zo yanzu, Ummi fada take zan kira ka later Be jira cewar Dawood ba ya sauke wayar ya nufo kofar dakin ya bude ya fito, tsaye yayi a stairs din yana kallon mahaifiyarsa dake zaune Namra na rumgume da ita tana kuka. Matsalata da ku karamin abu sai ku mayar da shi babba, miye abun kuka a nan kuma? Nimra dake tsaye rike da keys din da alamar shigowarta kenan ta watsa masa harara kamar wani sa'anta. Ba komai ba ne? A saka maka abun da zai iya zama sanadiyar lalacewar rayuwarka ko ma rasa ran gaba daya? Sannan ka ce ba komai ba ne? Ba laifinka ba ne mu muka da mu da kai Ta risina kusa da Ummi ta rika hannunta. Ummi dan Allah ki daina zubar da hawayenki a banza, ki daina damuwa da Maleek dan girman Allah, ta so mu je ciki Ummi ta mike tsaye Nimra na rike da hannunta ta juyo a hankali ta fara takawa, Maleek kuma ya fara saukowa tare da kawarda fuskarsa daga barin kallon kukan da mahaifiyarsa take yi. Hajiya ta lumshe ido ta hade yawu wannan karon ba kuka take na abun da aka yi ma Maleek ba, kukan marmarin danta Ameer take, ko a wane hali yake ciki a yanzu? Waya yake kula da shi a yanzu? Su waye abokansa? Wacece uwar rikonsa? Tana bashi kulawa kamar yadda danta yake samu? Har yanzu Mr Bashir yana kaunarsa kamar da ko kuma ya sauya? Yana ma raye ko ya mutu? Ummi... Kamar wacce ta farko daga dogon bachi haka ta bude ido da sauri ta kalli Nimra dake rike da ita, sai ta sake fashewa da kuka ta kwantar da kanta jikin Nimra. Ba zan taba zama lafiya ba Nimra, ba zan sake samun farinciki domin na siyar da shi da dadewa, shiyasa kullum da kalar kalubalen dake fuskantar yayana ko kuma ni Ummi me kike fada haka ne? This too shall pass, ki daina saka kanki a damuwa please, idan kina saka damuwa a ranki muma sai ki saka mu shiga wani hali, muna bukatar rayuwarki Ummi Ta kalleta sai ta yi murmushi cikin hawaye, daf da zata kai hannu ta share hawayen Abiey ya shigo falon yana fada kamar zai tashin falon. Sai ga waye uban yaron nan a Abuja, sai na ga abun da yake takama da shi a garin nan, sai an daure min shi a ceil Ummi ta kara hanzarin kai hannu ta share hawayenta, karaso kusa da shi tana tambayar abun da ya faru, Maleek ma kallonsa yake kamar yadda Nimra ma take yi. Miya faru? CP ne ya kira ni, wai yaron baya garin nan, amman mahaifin yaron ya bada hakuri, daga shi har yaron babu wanda ya je gurin, ni za a nuna isa? A taba min yaro kuma ace za a taka ni? Maleek yayi tabe baki abun mamaki ba