← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 165

Sashe 119

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

shi ma be san sonta yake a lokacin ba, sai daga bayan nan, wannan dalilin ya saka na zurfafa a binciken danginta, Amman me yasa be fada min ba sai a yanzu da Ameer ya fada a fili? Bayan kuma ta dade a gidan nan? Ban sani ba, wata kila sun fada a lokaci daya ne, amman suna hankali da natsuwa irin ta Maleek mai tunani bana ganin zai yi hakan a yanzu da Ameer ya nuna yana son Waira, kuma ai Maleek ya fi shakuwa da ita, abun ya zama wani ace suna son mace daya Ummi ta kwanta jikin Abiey hawaye na sauko mata, farinciki ya jure mata ya zama bakinciki, domin ba zata raba Waira biyu ta ba wa kowa rabi ba, haka kuma ba zata iya bawa Ameer ta hanawa Maleek da be taba jin soyayyar kowa a zuciyarsa ba sai wannan karon. Ba kuma zata bawa Maleek ta hanawa anta Ameer da take ji da shi a yanzu ba, take tsananin kaunarsa bayan ta gama bayyana masa farincikinta da jindadin fada mata yana son Waira har ma ta fada masa zata shige masa gaba a komai, kuma shiri take bukata da shi a yanzu, so take ta bashi farincikin da bata samu damar tsayawa ta bashi a lokacin da yake karami. Maleek yana yawan cewa Ameer lalata Waira, saboda yana sonta ne ko kuma dai ya fadi haka a yanzu ne saboda kar Ameer ya aureta? Ya kike magana kamar baki san waye Maleek ba, ai shi ni ya gado bashi da wannan zuciyar ko kadan, ina zaton dai Ameer ya fahimci haka ne shiyasa yake kokarin ganin ya shiga tsakaninsa da Waira, kuma be kama ace suna jayayya akan abu daya ba, musamman Ameer da shi ne babba, wannan shi ya zo daga baya bayan ya gama cewa be san yarinyar ba, ba san inda ta fito ba, da ban rike ta na mata gata ba, wata kila da be ganta ya ce yana so ba a yanzu, hausawa sun ce so so ne amman son kai ya fi, kuma da arziki a gidan wasu kara gidanku Ranka ya dade dukansu yayana ne, zan fi kowa farinciki idan dukansu suka samu abun da suke so, amman a yanzu ban san wa zan dauka ba, farincikin ya zame min bakin hadari da na kasa hango haske a ciki Maleek ya Ameer kaunarta, kuma shi ya kamata ya aurenta zai fi sanin darajarta fiye da Ameer, wata kila shi kyauta ne kawai ya dauke shi, ina gudun kar maganar Maleek ta tabbata ya aureta na dan lokaci daga baya ya nemi rabuwa da ita, kin ga ya lalata mata rayuwa kawai, kuma Maleek ba zai jidadin kin bawa dan'uwansa shi kin hana shi ba, ni kaina ba zan lamunci haka ba, kin fi kowa sanin yadda nake goyon bayan yaya a komai Ta lumshe ido tana jin wani kalar abu marar dadi na neman karya mata zuciya. Amman zamu iya bata dama ta zabi wanda take so, duk kuwa da na san be zama lallai ta san wanda take so din ba Aa haka be kamata ya kasance a tsakanin yan'uwa ba, da ma da wani ne a waje amman ba yan'uwa da suke jini daya ba, me yasa abubuwa suke zuwa min a haka ne? Abubuwa suna zuwa min da yadda shawo kansu zai zama mai wahala a gareni, kullum zuciyata a cikin kunci take Ba tare da ta bude ido ba take fadar haka, sai dai haka be hana hawaye samun hanyar fita daga idonta ba. Babu wani abun kunci a nan, kawai mu yi addu'a kuma mu ja hankalin kowa a cikinsu, zan yi magana da Maleek na ga idan har zai zan iya canja nasa ra'ayi, na san abu ne mai wahala amman zan gwada, idan na yi nasara kin ga an huta, sai ya barwa Ameer Ummi ta bude idonta ta saki Abiey ta nufi hanyar fita tana jin zuciyarta kamar zata fashe. Maleek be cancanci a gabatar masa da wata a matsayin ya so ta ba, domin be taba nuna son wata ba, sai a yanzu, neman canja masa ra'ayi kuma zai iya sakawa ya dawo da rayuwarsa ta baya, ko kuma ya kara rashin fahimtar dake tsakaninsa da Ameer, wata kila kuma yayi ma Ummi guguwar fahimta zai ga abun kamar ta nuna fifiko akan Ameer ne sama da shi. Ba kuma zata iya tunkarar Ameer ta canja masa ra'ayi ba, yadda yake da wahalar tankwaruwa ma ta san abu ne mai wahala ya amince, kuma zai sake kallonta a wata muguwar uwa wadda ta kasa bashi farinciki a baya, kuma ta kasa sama masa shi a yanzu. Wai miyasa tuntuni bata kula da alakar dake tsakanin Maleek da Waira ba, da a yanzu haka duk bata kasance ba, da yanzu ta san yadda zata bullowa lamarin, zuwan Ameer ya dauke hankalinta daga komai har bata ganin wata alaka sai ta Ameer da Waira, shi kuma ya cancanci farinciki daga gurinta a yanzu, ta dayan bangaren kuma ta san Abiey fada kawai yake amman ba zai bar vangaren dansa ya zabi Ameer ba, wadda suke yi ma kallon makiyinsu saboda abun da ya faru da Nimra, ga kuma salsalar rashin jituwa dake tsakanin Deen da Abiey, Deen din ya tafi amman Abiey ya kasa jefar da wannan gabar da kiyayyar wata kila shi ya saka har yanzu bw taba tambayar lafiyar Ameer ko kuma zuwa duba shi a bangarenta, tun da Ameer ya sako kafa a gidan Abiey be taba maganarsa ba idan ma ta yi magana ba zai ce uffan ba har aci a sude. Wayyo Allah.... Ta fada tana jinginawa da corridor ta sulale kasa tana kuka marar sauti, gaba daya abun ya rikice mata, ta rasa na dauka ta rasa na zubarwa haka ma ta rasa yadda zata bullowa lamarin. WAIRA POV. Tana gama kallon Sallah a wayar Ummi sai ta aje wayar akan gadon Ummi, daman kamin Ummi ta fita dakin ta karbi wayarta ta shiga gurin da Ameer ya nuna mata, kuma a yau ta ji bata sha'awar kallon komai sai Sallah, daman yadda take ganin suna yi a gidan abun na burge, ta wani bangaren kuma tana kallon abu kamar wahala ne a gareta. Tana aje wayar ta nufi gurin da Ummi take aje a carpet dinta ta dauka, ta dauko dankwalin Ummi na atamfa dake kan gado ta riko carbi ta fito ta sauko kasa. Bata damu ta fuskanci alkiba ba, domin bata san miye haka ba, kuma bata taba ganin kowa yayi sallah a falon ba balle ta kula da inda ake kallo idan za'ayi sallah, dama a cikin dakin Ummi ta san inda zata tsaya ko ta shimfida yayi daidai da alkiba. A falo kam sai ta shimfida carpet din ya fuskanci gurin plasma ta nada dankwalin a kanta ta rufe gashinta, bata damu da yadda rigar jikinta bata sauko mata har kasa ba ta rufe ido tana tuna yadda macen da ta kalla take yi, da kuma yadda take yawan ganin Ummi tana yi da Nimra idan suna sallah, har fa motsa baki take ba dan ta san abun da ake fada ba, ita dai motsa baki kawai take saboda ta ga Ummi na yi, har lokacin kuma idonta a rufe yake. Tun daga sama Maleek ke kallonta yana saukowa a hankali ya iso inda take zaune tana zaman tahiya, bata san raka'a nawa ke magariba ko isha'i ba, dan haka ta kara ra'a uku bayan ta yi biyu. A lokacin da ta gama sai ta zauna ta yi sallama kamar yadda ta ga Ummi tana yi, duk abun da take Maleek na tsaye bayanta yana kallonta fuskarsa da murmushi, wani irin kimarta da girmata da kwarjinta ga haibarta suka cika masa zuciya. Jin kamshin turarensa ya saka ta juyo suna hada ido sai ta yi dariya ta rufe ido, sautin dariyar da yadda ta kalleshi ta rufe idon da ta yi suka ruda shi har ya nufi kujerar dake gefenta ya zauna yana mata wani irin kallo da shi ma be san yana yi ba. Sallah nake yi Ta fada ganin yana kallonta, sai dai hakan be saka ya dauke idonsa daga barin kallon ba sai ma jan hankalinsa da ta yi da sautin muryarta mai dadi sauraro ya zuba idonsa akan bakinta yana kallon yadda take motsa shi a hankali tana sake nanata masa Sallah ta yi. Sallah ce kawai Ameer ya fada min yadda ake yi, kuma na ganin a wayar Ummi, yau na ji ina son na yi shiyasa na yi, amman kai ma kana yin sallah? Ban taba gani ba Ya Maleek Still motsin bakinta yake kallo, kamin ya maida duban akan eyes dinta da dagon hancinta, wata kila sallah da ta yi ne ko kuma ya ga ta yi ne ya kara mata haiba da kyau a idonsa, har yake jin kamar bata taba burgeshi ba sai yau. Ganin yaki amsa mata sai kallonta yake ta saka ta kwanto da kanta tana leken fuskarsa. Ya Maleek Can cikin kwakwalwarsa yaji sautin kiran sunansa da ta yi da wata irin siga da yake jin kamar wani be taba kiran sunansa a yadda ya kamata da dadi ba irin yau, matsawa ta yi kusa da shi da gangan ta hura masa iska a cikin ido domin ta ga kallon da yake mata ta gani idan tana ganinta da gaske ko kuma binta ne kawai yake da kallon. Iskar bakinta na isa a fuskarsa kai tsaye ta zarce a idonsa ragowar ta ziyarki hancinsa kamshin bakinta ya daki hancinsa, slowly ya lumshe ido sai tattausan murmushi ya biyo baya. Ita ma murmushin ta yi ta matsa baya. Sorry Ya bude idon ya kalleta still murmushi yake mata kamar ba shi ba. Sorry for what? Na hura maka iska mana, to na ga ina ta fada maka sallah na yi amman baka ji ba, sai kallona kake yi Sallah da kika yi ne, abun da ya bani mamaki kuma ya faranta min rai na ji kin burge ni, shiyasa har na kasa dauke idona daga barin kallonki kin yi abu mao kyau Waira, baki taba burge ni ba irin yau Ta kai hannu ta taba zuciyarta dake
Chapter 119 · 0% Book details