← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 165

Sashe 100

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

akwai abun da kuke bukata ki sanar da ni Okay Da ok kawai ta amsa mahaifiyarta ta dora da godiya da addu'a, shi kuma ya juya ya fice bayan yayi ma tsohuwar fatar samun sauki. A lokacin da yake kokarin bude motarsa ya shiga ya ji muryar Humairah bayansa. How are you Ameer? Ya juyo ya kalleta. I'm fine Ban ga haka a fuskarka ba I will be fine Ta rumgume hannayenta. Ka yi magana da ita? No maybe tonight idan zan kai jakar Waira Who's Waira? Ya daga kansa yana kallon harabar gurin. Wata yarinya ce mai kyau fuska da kyakkyawar zuciya, ta iya kyautata lafazi, gata da jan hankali, abar tausayi ce kuma abar so, abar kulawa full-option ta hada komai, and someone has never been in her heart I'm sorry Ameer. It since like ka yi saurin warkewa daga abun da ka yi ma Nimra. With due respect Ameer baka canja ba Ya matso kusa da ita. I canja Humairah kuma zan canja, shiyasa nake son na kyautatawa mata i won't break her heart, ba zan bari wani ya cutar da ita ba, she's the kind of girl I'm looking for, not just her zan kyautatawa kowa gwargwadon ikona, domin na fahimci ni ma alfarma nake ci Ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani abu marar dadi ya tsaya mata a makoshi. Who's knows who my family is? Wace kalar rayuwa suke? Su waye su? Mutanen kirki ne ko na banza wace kalar rayuwa mahaifina yayi ban zani ba, kamar yadda Waira ma bata san waye mahaifinta ba, banbancinta da ni, ni ina da Daddy da Ummi a yanzu, ita kuma bata da kowa if you want to change you should start from within.... Ina fata kuma ina kyautata zaton mahaifinka mutumen kirki ne wish you all the best Ta karasa tana murmushin karfin hali. Thank you Ya amsa sannan ya saka key din ya bude motar ya shiga. Tana tsaye a gurin har ya bar asibitin. A hanya ya tsaya yayi sallah sannan ya kama hanyar gida. Yana isa ya cire jakar Waira ya saka a wata motar ya mikawa mai kula da motocin gidan key motar da ya dawo da ita. Ka wanke ta da kyau akwai jini a ciki, na kade wata mata ne muka kaita asibiti Jiki na rawa mutumen ya saka hannu biyu ya karba, yana mamakin yadda Ameer yake masa bayanin abun da ya faru, abun da be saba ba, ko da mutum zai bude ya gani a motar ba zai fada masa ga abun da ya aikata ba, shi a gidan babu mai jindadinsa dukansu suna zaune ne kawai saboda Mr Bashir yana kyautata musu kuma yana musu albashi mai tsoka. Ya shiga cikin falon cikin wani yanayi mai wuyar fassara, Mummy dake tsaye rike da remote ta kalleshi. Ameer ka dawo Ya kalleta, a lokacin da yake an iskan gari bata isa ta yi magana ya amsa mata ba sai ya ga dama, har ganin yake kamar sa'ido take masa tana masa munafurci a gurin Daddy, amman yanzu wannan duk ta kau. Ya wuce sai kuma ya juya. Na kade wata mata by mistake amman na kaita asibiti, please ina son ki saka masu aikin gidan nan su zuba mata abinci, zan yi ma musa text din inda take da kudin da za a bata sai yaje ya kai musu Subhanallahi amman dai baka ji ciwo ba ko? Ya amsa mata da kai. Matar da sauki? Da sauki ina tunanin karaya ce Allah ya sauwake, ya tsare gaba please Ameer ya kamata ka rika kula idan kana tuki, kuma ka rika sassautawa zuciyarka Sai da yayi kamar ya tsaya yi mata bayanin ba da gangan ya kade ya ba, it's not his fault sai kuma ya juya kawai ya nufi stairs. .Around 9:11pm Waira tana zaune kan carpet tare da pen dinta, liffatinta na lessons na gabanta ta dora jakar a kan kujera. Baby rabbit dinta ta dora kan littafin tana zanawa kamar an sakata. Namra na zaune kam 3 seater tana lasar wayarta. Maleek kuma na zaune a dayan side din falon rike da mug hannunsa daya kuma rike da wayarsa, sai ko kadan hankalinsa ba shi a gurin wayar ya tafi gurin abokiyar fadansa Waira dake zane, ba ya iya hangen zanen da take, but he found himself looking at her, ko wane motsi da nata yana kan idonsa. If ba dan kar na yi karya ba da sai na ce har yadda yake fita da shigar numfashinta yana kallon yake yana kan idonsa. If wani zai tambaye me yasa yake kallonta ba zai iya fada ba, maybe ko dan ita ce mace ta farko data fara bude masa ido har yake son kallonta ko zama kusa da yan'uwanta, zai kuma fi yarda idan aka ce saboda kyaunta ne domin tana da kyau daidai yadda ko ita ta tsara kanta iyakar abun da zata yi kenan. Everything about her is unique her hair, dress, her talk the shagwaba part and even her talk yana jin fadi muryarta when she's talking about something. Yana ganin Ummi ta fito daga kitchen sai yayi saurin dauke idonsa daga barin kallonta ya maida dubansa kan wayarsa. Ummi ta dire mata copy tea Wai haka aka ce ku yi a makaranta? Kina wahalar da wannan zomon ace sai an dora shi kan takardar sannan a zana waya ce ku zana zomo Waira ta kalleta with her cute laugh ta ce. Babu wanda ya ce na yi Ummi, kawai ina son na zana ne Kin sa miyasa mai lessons dinki be zo ba yau? Aa be ce komai ba da zai tafi Ko maybe ba shi da lafiya ne? Waira ta bude baki zata yi magana kenan aka murda kofar falon, Ummi ta juyo ta kalli kofar Maleek kuma ya dago kansa ya kalli kofar, Waira ta maida dubanta a inda suke kallo. Ameer ne ya shigo cikin shiga ta kananan kaya sai kamshi yake kamar sabon ango, hannunsa rike da school bag din Waira. Mamakin zuwansa ya hana Ummi amsa sallamar da yayi, Maleek kam daman shi ba zai amsa masa ba, balle kuma Namra da sai a lokacin ta dago ta kalleshi. Waira ta washe hakora kamar bakauye ya zo birni, Hanne ce kawai ta amsa masa sallama domin bata wayance shi da kyau ba. Maleek ma mamakin zuwansa yake duk kuwa da yana kallon dalilinsa na zuwa wato jakar Waira dake rike a hannunsa, sai dai abun da ya fi daure masa kai shi ne yadda Ameer yake kokarin kula Waira yarinyar da ko a mafarki aka ce masa Ameer zai yi haka ba zai yarda ba. Ba a maraba da zuwana ne? Ya fada ganin yadda kowa yayi tsaye yana kallonsa kamar sun samu tv. Sai a lokacin Ummi ta dawo hayyacinta tunaninta ya dawo jikinta. Of course you're welcome, kai da gidan mahaifiyarka Ameer Ta fada idonta na cika da hawaye even though ta san ba zuwansa ne ya kawo ta amman a haka murna take anta ya shigo gidanta, sallamar da yayi kawai ta isa ta saka ta fahimtar da lalama ya shigo gidan nan. Please dan Allah ka zauna Kujerar da ta nuna masa dabam kujerar da ya zauna dabam, ta nuna masa dayar kujerar dake kusa da inda Waira ta dora jakarta, shi kuma sai ya zauna a kujerar da ke kusa da Waira. Da sauri Waira ta saki abun da take ta tashi tsaye ta zauna kusa da shi kamar zata shige jikinsa. Jakata ka kawo? Ya daga mata kai try to smile, kallonta kawai yake kana gani kasan ta gama dauke masa hankali, domin ko kadan be lura da sauran mutanen da suke falon ba, balle har ya san da zamansu. Welcome Ta fada tana jindadi sosai, not just for Ummi, tana son ta ganta kusa da mutanen da take kauna kuma ta sani, he the second person da take jin sakewa da shi bayan Shuraim. How are you? Fine Ummi ta nufi kitchen da sauri jikinta har rawa yake, bata dade ba ta fito rike da tray dake dauke da ruwa da kuma lemu da kuma tea a dayan gefen, bata karasa inda yake zaune ba sai ta kira sunan Waira gabanta na faduwa a ranta tana addu'ar ya karba ya sha. Waira karbi ki bawa yayanki, wata kila ni idan na bashi ba zai sha ba Ameer ya dago da ya kalleta sai ya ga maganar da Waira ta fada masa na ciwonsa kamar rubuce a fuskarsa, ita kuma ta sauke kai kasa kamar mai jin kunya. Waira ta mike tsaye ta isa gurin Ummi ta karbo tray ta nufi Ameer da shi kamin ga aje kasa ya saka hannu ya karba. Ummi bata san me kake so ba, ta zuba maka tea ga juice ga kuma ruwa Ya ji babu dadi ace mahaifiyarsa tana raye amman bata san kalar abincin da yake so ba, amman ya danne saboda ya farantawa Waira, domin be zo gidan dan ya daga hankalin kowa ba. Ya san ruwa daga kamfani aka yi, kamar yadda lemun ma daga siyo, tea ne abun da zai iya shaidar ta hada masa da hannunsa, dan yana ya dauki cup din tea din ya aje tray ya rike tea yana kallon Waira dake fada masa ita da biscuit ko cake take shan nata kamar ta manta Maleek yana falon. Akwai dadi idan ka hada Yayi murmushi kadan. Akwai dinki a jakarki Ta bude jakar ta fiddo cake din ta bude. Kai ka ci da yawa Ya daga mata kai. Yayi dadi ne sosai Ka tafi da shi duka za a sake min wani Ya girgiza mata kai. I will take tea Namra ta mike a fusace ta fice daga falon domin ko kadan bata son kallon Ameer, Maleek sai yaki yake da numfashinsa domin jin yake wani abu na masa yawo tsakanin makoshi da zuciyarsa ba dan kai yayi ruining happy face din Ummi ba, babu abunda zi hana shi iss gurin ya tsinakawa Waira mari kuma ya kori Ameer. Ameer ya dade rike da cup din tea din yana ta magana da Waira kamar daga shi sai ita ne a falon, Ummi kam idonta na kamshi tana jiran
Chapter 100 · 0% Book details