Sashe 91
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
natsuwa har sai na zo na duba shi Duk da haka dai, ni da shi duka muna karkashin kulawar Mai gidan ne, be kamata na yanke hukunci ba tare da saninsa ba, ko da kuwa baya kusa balle ma yana cikin gidan saboda yau weekend ne, bari na kira shi ku yi magana tukuna Ummi ta amsa mata da kai, zuciyarta na raya mata Mr Bashir ba zai bari ta ga Ameer ba. Mommy ta tashi ta nufi wata kofar sai kuma ta juyo ta kalli Ummi. Ke ce matar da aka ce kin ce Ameer anki ne? Ba ance ba ne, Ameer ana ne zan iya tutuya da fadar hakan a gaban kowa Ummi ta amsa mata kai tsaye ba tare da ka kalleta ba. Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta fice daga falon. Bayan ficewar Mommy Ummi ta dora jakarta a kan kujera tana ta sake sake a ranta. Ummi ta yi zaman da kai minti ashirin a falon sannan ta ji muryar Mr Bashir kamar daga sama. Ban yi zaton na karya daya daga cikin alkawuran da na daukar miki ba, me zai saka ki bada kyautar da zaki dawo daga baya ki tambaya Ummi ta juyo tana kallon Mr Bashir da ya tunkarota fuskarsa dauke da damuwa, duk yadda ya shirya yin fada da Zahra da yi mata barazana da duk wani abun bacin rai sai ya ji lagunsa ya karye a lokacin da kalli fuskarta, kwarjininta ya cika idonsa har ya ji kamar yana gudun bata mata rai. Ni ban yi zaton zan tambaya ba, fadar gaskiya ko kuma bayyana ta baya nufin canja komai daga alakarku da Ameer, kawai dai ina son na yi duty na a matsayina na uwarsa, ina son na gyara komai kamar yadda na bata Mr Bashir ya kalli Mommy bayan ya zauna. Ba mu guri Ta mike tsaye ta haye sama, sai da Daddy ya tabbatar ta shige dakinta sannan ya kalli Zahra ya ce. Wani ya taba kai miki gulmar Ameer ya rasa wani na gata ko kewa daga uwa? Ta girgiza kai. Aa na kasa jurewa ne, fiye da yadda ka kasa jurewa a yanzu da kake ganin kamar zan rabaka da shi ne, kai kenan balle kuma ni da nake uwa? A ko wane dare ina kwana da kaunar Ameer a raina da kewarsa, na baka amanarsa ne saboda ma gamsu zaka kula da shi, bayan na yi hakan kuma zuciyata ta kasa natsuwa da abun da na aikata, na cutar da wasu domin ba ni kadai nake da hakki da Ameer ba, tsoron hukuncin da zai biyo baya da kuma kurciya a wacan lokacin na cewar idan suka san na siyar musu da jika, kuma ina ganin kiyayyar ana a cikin idon mijin da nake aure a wacan lokaci shiya karya min guiwar duk wani buri da nake da shi, kai ma zai taba mutumcinka shiyasa na bar komai ya tafi kamar yadda muka tsara, ban yi zaton Allah zai sake dawo da Ameer a kusa da inda zan ganshi ba, sai gashi ya kulla alaka da an'uwansa kuma ya zaunar da mu a gari daya, na furta masa hakan ne a lokacin da hankali ya gushe saboda abun da ya aikatawa yarinyar da na yi riko kuma na shayar da ita da nono na, wanda sanin kanka babu aure a tsakaninsu, duk abun da ba mu sani ba, Ameer daman ba son ta yake ba, kawai ya shirya hakan ne saboda ya dauki fansa na gabar dake tsakaninsa da Maleek, sai kuma aka yi daidai da ajali, ya fada mata gaskiya a lokacin da zuciyarta ta kasa dauka har sai da zuciyarta ta buga aka kwantar da ita asibiti, kuma rai yayi halinsa mai ajiya ya karba jiya aka yi sadakan ukun Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Shi ne abun da yake ta fita a bakin Daddy ya cire hular kansa ya dafe kansa, Ummi ta sauke kanta kasa tana hawaye. Da ace Ameer ya aureta, ko sun aikata wani kuskuren laifin waye? A yanzu ma da ta rasu laifin waye? Kai ma uba ne ka bude zuciyarta ka kalli yadda zaka ji idan hakan ya faru da kai, Maleek da Ameer gaba suke da junansu bayan kuma su yan'uwan juna ne, idan na fadi na mutu a yau wace amsa zan bawa Allah? Na aikata abun da na aikata ne saboda ina tunanin mahaifinsa zai rayu, na aikata saboda ba ni da mafita, talauci ne silar komai a yanzu kuma ba arzikinka nake so ba, so nake na gyara komai ina da wasu yayan kuma mai arziki nake aure a yanzu idan har saboda kudi ne to me zai saka na yo haka? Me na rasa? Ina ta kokarin kaucewa amman kaddara ta rubuta haka, shiyasa har Nimra ta gabatar mana da Ameer a maysayin wanda take son aure, bayan shi yar'uwarta Namra kuma ta gabatar mana da an likitan da yayi min hanyar ganin Hajiya Jamila wato yayanta a matsayin wanda take son aure, me ka gani shim ke kamata mu bawa kaddara damar rubuta abun da ta tsara akan mu ba? Idan na kauce wannan to abun nawa ya zama son kai, dan Allah ka ba ni dama ni ma na wanzu a rayuwar Ameer ya kalleni a uwa kamar yadda yake kallonka a mahaifi Ummi ta karasa tana saukowa daga kan kujera ta zube kasa kamar zata roke shi. Sai yayi saurin mikewa tsaye ya girgiza kai. Ameer be yi lalacewar da uwar da ta haife shi zata duka ta roki wani abu ba, idan har wani zai tsuguna ya roki wata alfarma to ni ya dace na duka na yi miki godiya kuma ya roki Alfarmar ki bar Ameer ya cigaba da zama a matsayin ana, dan Allah koma ki zauna Ummi ta tashi ta zauna kan kujerar, Mr Bashir ya zauna a karo na biyu yana kallon fuskarta tausayinta shimfide a fuskarsa. Allah ya mata rahma, hakika ban tarbiyar da Ameer da wata kalar tarbiyar makamanciyar wannan ba, sai dai rayuwa da kuma jarrabawa babu ta inda bata zuwa, ni kaina halayen Ameer sun jefa ni a cikin damuwa kala kala, sai dai be kara min komai ba sai kaunarsa, a da ina ganin kamar kin yi hakan ne saboda ki yake ni, sai dai a yanzu na fahimci ba mu isa mu yi ma Allah wayo ba, kuma Ameer deserve to know the truth, My condolences Ameen Ummi ta amsa tana share hawayenta. Sai dai idan zai yiyu ki yi hakuri ganin Ameer ba zai samu a yanzu ba, ba dan ina nufi gina wani abu a tsakaninku ba, domin kin min komai kin rufa min asiri a lokacin da makiya za su min dariya, gaskiya kika fada bayyanar cewar Ameer ba ana ba ne a yanzu babu wanda zai ji sai idan mun so ya sani, amman a wacan lokacin da hakan ya faru da na sha kunya da kunci matuka, kin min kyautar a sukutun da ya hana ni kewar rashin haihuwa, ko a haka kadai kin cancanci na yi miki komai a yanzu, kin aikata abun da kika aikata saboda ki ceto rayuwar mijinka na farko, sai dai hakan ya gagara saboda rai baya tsayawa dan wata rai, kuma kin hakura kika danne abun da kike ji ranki saboda farincikin mijin da kike aure a yanzu, maddallah da ke Zahra hakika ke mata ce ta gari Ummi ta sauke ajiyar zuciya tana sanyi a ranta na saurin fahimtarta da Mr Bashir yayi domin ba ta yi tsammanin zata same shi haka cikin ruwan sanyi ba. Na gode, amman me yasa ba zaka bar ni na ga Ameer ba? Saboda ni mahaifinsa be, duk wani abu da zai jefa Ameer a damuwa bana sonsa, kwanansa biyu babu lafiya, abincin kirki baya iya ci, ko aiki baya fita kuma ina tunanin duk saboda faruwar wannan abun ne ya haifar masa da damuwa, yau ne muka samu ya dan sake har ya fita harabar gida yana dan hutawa, ina tsoron kar ganinki ya dawo masa da damuwa ko ya haifar masa da wata matsalar domin har yanzu be gama fahimtar rayuwar da kika bijiro masa da ita ba Ummi ta yi shiru, bata son takurawa domin ita ma din kamar shi take bata son damuwar Ameer idan har ganinta zai haifar masa da damuwa yo zata iya hakura. Daman dai na zo na duba lafiyarsa ne, ssboda zuciyata ta kwadaitu da son ganinsa, tun da na ji lafiyarsa Alhamdulillah wannan ma kadai abun farinciki ne a gurina Ta mike tsaye ta dauki jakarta. Ka taimaka min gurin shawo kan yaron nan dan Allah, ya yafe min abun da na yi masa Ba zamu iya cilasta shi ba, amman a hannu zai fahimta mu bashi lokaci Ta amsa masa kai sannan ta ce. Na barka lafiya Binta yayi da kallo har ta fice sannan ya girgiza kai ya sauke ajiyar zuciya. AMEER POV. Tun a safiyar da ya raka gawar Nimra makabarta ya dawo gida zazzabi ya rufe shi, be sake lafiya ba sai yau shi ma kuma ba wadatarsa ta yi ba, ya dai samu kuzari ba kamar kwana biyu da yake wuni da zama a daki ba, har sai da Daddy ya kira Family Doctor su ya duba shi ya rubuta magani aka siyo masa ya sha, abinci sai Mommy ta matsa masa ya ke dan ci, ko kuma Daddy ya saka a kira shi bangarensa su ci abincin a tare duk yadda Daddy yake jans ada hirar duniya saboda ya sake ya kasa yin haka, idan kuma ya dauko masa zancen Ummi sai kawai ya tashi ya fice ya bar Daddy. Sai dai ya tashi jikinsa da dan sauki bama kamar da yamma nan da ya sha energy drink. Kewar Nimra da tunanin rayuwarsa da yayi ta baya kamin komai ya lalace ya saka shi fitowa yana ta yawo a compound din gidan, kamin daga karshe ya tare a garden da yar sarewarsa yana busar dake deba masa kewa da kadaici. Vest ce a jikinsa sai Jean baki da talkamin da suka fi kama da silifas. A tsaye yake yana busar a tsakanin ruwa swimming pool da kujerun da aka ware