Sashe 19
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
fiye da kowa karki tashi hankalin yayana...! Yana kaiwa nan ya kabe rigarsa ya fice daga dakin a fusace har yana sakin kofar da karfi. Kalaman da yayi mata a yanzu sun kara tabbatar mata da cewar Ameer din ta ne, sai dai ya shata mata layin da bata isa ta tsallaka ba, kamar yadda ta yi ma kanta kataga tsakaninta da shi da bata isa ta rusata a yanzu ba. Ba tayi mamakin kalaman mijinta ba domin ta san ba shi da makiyi kamar Deen, hakan ya saka a duk lokacin da ta nuna damuwa akan Ameer sai ransa ya bace ya ce saboda yana an Deen ne, a kullum ikirarinsa bata son Maleek saboda jininsa ne sai Ameer da yake an makiyinsa. Gaskiya ne, Ameer ba ana ba ne a yanzu, an wasu ne, yana da family da iyaye yana da rayuwarsa ta dabam Da zuciyarta take magana tana kokarin ganin ta kawar da tunaninsa a ranta ta cire shi daga zuciyarta, ko ba komai yanzu dai ta san yana a guri mai kyau kamar yadda take buri, ta san Mr Bashir ya ba shi gata da kulawa kamar yadda yayi mata alkawari tun da har ya hana police su kama shi saboda abun da ya aikatawa anta Maleek, ya girma a yanzu ya zama babban Saurayi rayuwar baya ba ita ce a yanzu ba, ya kamata ta manta da komai. Hakan ya saka ta tashi ta shiga bandaki ta wanke fuskarta ta fito ta zauna bakin gadonta dafe da zuciyarta, har yanzu bata daina jin wannan mashin da ya tsoki kahon zuciyarta ba, a yanzu kam ta yarda ta rasa Ameer har a bada, sai dai idan ta tuna bata bashi kulawa yadda ya kamata ba, sai ta ji wani iri a ranta, ga cutarwa da ta yi ma iyayen Deen na raba su da an Deen tilo da zai iya zame musu sanyin ido. Hakki ba zai bar ni ba, na cutar da yaron nan na cutar da kananinsa na cutar da kaina, miyasa ban yarda na karbi hukunci tun a wacan lokacin ba? Ta fashe da kuka sosai tana tsananin nadamar abun da ta aikata, ina ma ace da halin gyara da ta gyara komai a yanzu, yanzu ta kara tabbatar da hakkin ne yake bibiyarta shiyasa Maleek baya kaunar matsowa kusa da ita, kuma baya son ko muryar mata ya ji, ita kuma ta kasa manta abun da ta aikata hakan ya hana ta farinciki. Mikewa ta yi tsaye ta dauki wayarta ta yi clearly din searching din da Namra ta yi mata na Ameer, a kokarin na engaged din kanta da wani abu ya saka ya canja tufafin jikinta zuwa wasu marar nauyi ta sauko falo, Mahmood kawai ta samu zaune yana lasa wayarsa, dagowa yayi yana kallonta har lokacin idonta be cire kumburi ba. Abiey yace mana Bachi kike Yanzu na farka Ta fada tana kokarin ta yi murmushi amman ta kasa, haka ta wuce Kitchen suna da masu aiki, sai dai ta sabawa kanta ita take girkawa mijinta abun da zai ci da kanta, hakan ya saka ta fara shirye shiryen girka masa abin da ya fi kauna saboda ta san ransa ya bace, sai dai me tana kai hannu ta bude fridge sai ta fashe da kuka. AMEER POV. Be isa Katsina ba sai 11pm na dare sai da ya fara tsara dajikan garin ya fara tunanin me ma zai kawo shi garin? Miyasa ya zo nan? To ina zan je idan ba nan ba? Ta tambayi kansa domin ya san barin kasar a yanzu ba abu ne mai sauki a gare shi ba, idan ma ya bar kasar duk inda zai je zai samu kansa cikin bacin rai ne da damuwa. Ya cika bakinsa da iska ya busar tare da kai hannu ya dauki wayar Nimra da sakonta na uku ya shigo domin jin lafiyarsa tsoron kiransa take kar ransa ya kara baci wata kila be huce ba har yanzu. Kai tsaye ya aika mata da kira ringing daya ta daga kamar daman can jiran kiransa ake, sai dai yayi mamakin jin wata muryar wacce ta girmi ta Nimra ta daga wayar tare da sallama, da gangan yaki amsa sallamar domin ya san ba Nimra ba ce, kuma shi tun da ba wanda yake son waya da ita ce ta daga ba be ga amfanin yin magana ba, sai kawai ya kashe wayar. After like 3 minutes Nimra ta kira shi sai ya daga ya saka ta a speaker. Ka kira na je na daukowa Ummi abu, ka isa Lafiya? Yayi shiru kamar ba zai amsa mata ba. Ina na je? Ban sani ba, amman ina fata r kana wani guri mai aminci Ya faka motar gefen titi ya sauke gilashin Motar yana kallon titi. Ina KT in the middle of the road i think Nimra dake zaune a dakinta ta mike tsaye cike da damuwa. I know be kamata ma saka kaina a cikin matsalarka ba, Amman da zaka yi hakuri ka dawo gida ina tunanin zai fi domin a yanzu zaka jefa kanka a cikin wata matsalar ne kawai kuma.. Sai kuma ta yi shiru.. Mahaifinka yana bukatar ka Ameer Ya juyo ya kalli wayar kamar ance masa ita ce a gabansa. How do you know my father? Taya kika san shi? Abiey mu yayi magana da step mother dinka Ke ki fito fili ki yi min magana yadda zan fahimta, what do you know about me? Bata son ta fada masa cewar ita din kanwar abokin hamayyarsa ne duk kuwa da ta san dole zai sani, sai dai tana ganin kamar be dace ta yi hakan a yanzu ba. I'm talking to you Ya daka mata tsawa kamar tana gabansa, a dole ta fada masa abun da ya faru da yadda aka yi ta gane cewar shi din ne ciki har da hotonsa da Mahmood ya nuna musu. Wow... So Maleek duk shi yayi planning wannan? Shiyasa kike ba ni shawarar yadda zan yi masa? Shi yake fada miki ko? Ta girgiza kai da sauri. No no no Wallahi ba shi yayi ba, ba shi ya saka ni ba, taya zan baka shawarar yadda zaka yi masa haka? Wallahi ban san akwai alaka tsakaninku ba sai dazun ka yarda da ni Ameer Idan na yarda dake duniyarki zata gyaru ne? I don't trust you karki sake kirana, and mark my words ke ma sai na koya miki darasi kamar yadda zan koyawa an'uwanki Rasa ta yi ta inda zata kamo zaren balle har ta fara sakar yadda za 'ayi ya yarda da ita. Mahaifinka yana bukatarka Ameer He's Unconscious, Step Mother dinka tace be ma san an kai shi Asibiti ba Yanke watar yayi ya bude motar ya fito yana jin wani bakinciki na karuwa a ransa, Ameer wani irin murdaden mutum ne da bashi da fahimta cikin sauki, abu kadan ya bata masa rai. Ji yake gaba daya Maleek ya gama da shi. _Da gaske mahaifinka na asibiti Ameer ba karya nake maka ba, kuma ka yarda da ni ban yi komai saboda na bata maka ba, dan'uwana ma be san muna da alaka ba_ Ta aiko masa da sako, yana gama karanta sakon ya koma cikin motar ya danna a wata hanyar da ke gefen inda ya faka motar, daman can be san tsoro ba tun yana karami baya shakkar kows bata shakkar komai, musamman idan ransa ya bace babu abun da ba zai iya aikata ba, Ameer irin mutanen nan ne da idan ran su ya bace hankalinsu ke gushewa su aikata komai sai dai daga baya ayi nadama, tun yana karami haka ya tashi ko mutuwa aka aje sai ya taba ta sai dai ya mutu, idan kuma aka ce idan yaje can zai mutu ko wani abun ya same shi to sai yaje sai dai komai zai faru ya faru. Ba ma kamar yau da yake jin kamar ya kashe kansa, miyasa ya yarda da yarinyar da be sani ba, why ya kulla alaka da kanwar makiyinsa? Duk wannan plan din Maleek ne haka zuciyarsa ke raya masa, be taba sani shi din wawa ba ne dai yau. Gudu yake sosai cikin jar kasar da babu titi sai kura da turda dake tashi saboda gudun da yake komai ya ci karo da shi bugewa yake babu ruwansa da bata motar da zai yi ko kuma ya jiwa wani ciwo, yo a gari ma Ameer ai gudu yake da mota yana kade mutane balle kuma a wannan dajin na Allah da babu kowa a hanyar. Karshe gudu ya kai motar har sai da ya kai karshen hanyar sai ya tsara ta inda ransa yayi masa dadi domin ba hanya da ke bullewa cikin gari ba, da gangan yayi ta buga motar a jikin wasu manyan duwatsu da ya samu daker da wahala motar ta karaso gurin, sai da ya tabbatar ya lalata gaban motar sannan ya bude ya fito ya jefar da wayar a cikin daji. He rather die here da ya sake amfani da wani abun da ya shafi Maleek. Hudun yayi masa yawa domin ya lalata na Motar kuma ya jefar da wayar a inda be saka ran ganinta ko da ya duba, tsaye a gurin yana kara jin tsanar Maleek a ransa musamman idan ya tuna shi yana can kwance a guri mai kyau tare da iyayensa shi kuma ya hada shi da nasa iyayen kuma ya bashi da inda ya fi jindadin kwanciya. Ya dade yana tunanin yadda zai yi ya rama abun da Maleek yayi masa kamin ya bude motar ya dauko Carpet dinsa da ya siya ya saka hannu aljihu ya ciro ATM din Nimra ya karya shi, ya cire kudin data bashi ya saka a motar ya rufe motar. Da taimakon farin wata dake haska dajin mai kama da tarkon mutuwa ya karasa gurin fakon dake gabansa mai kamar an share ya shinfida ya kwanta a gurin ba Aljannu ba ko Uban gidan aljannu ne a gurin sai ya kwanta ko ma kashe shi suka yi shi daman mutuwar yake nema, yadda ka san wani dan shaye shaye haka yake zama idan ransa ya bace. Kasa bachi yayi hakan ya saka shi tashi ya zaune