Sashe 27
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta dade sai hakkinsa ya fita, ka saka masa ido kana zaune hakkinka zai ita matukar ya zalince ka Allah ba zai bar shi ba Ni ko ba a taba ni ba, kin san zan taba balle kuma an taba ni, bana bari ga Allah Ya amsa mata kai tsaye, numfashi ta sauke a hankali ta mike tsaye. A dauko maka wani abincin? Na koshi, a sama min flight din da zai tafi Abuja anjima zan kwanta yanzu idan babu kuma zan je da mota Ba zaka kwana a nan ba? No ina son na je na duba jikin Daddy hankalina ba zai kwanta ba sai na ganshi Hajiya Jamila ta shafa kansa, sannan ta fice cike da damuwar da ita kadai ta santa. Kwanta yayi saman lafiyayyen gadon abun ka da wanda ya marmarin bachi nan da nan bachin yayi gaba da shi. Mafarkinsa gaba daya akan yarinyar da tunaninta ke saka shi tashin zuciya da mai ne, ba mafarkin abun da ya faru a dajin yake ba, mafarki yake akan wata yarinyar da aka tsabtace ta sha ido da kwalliya, kamshi ta ko'ina ta ratso taron jama'ar da ake gabatar da Event din da be san na minene ba, ta iso gare shi, sai ya risina kamar mai jiran isowarta ta saddan kansa kasa alamar girmamawa a gareta ita kuma ta cire wani zare a hannunta ta daura masa a wuya ta yi mashi murmushi, sannan ta juya ta fice daga taron a zuwa wani dakin dake da icen tuffa ga kuma wani itacen na dogon yaro (Dalbejiya or Bedi) a tsaye. Can kuma mafarkinsa ya sake daukarsa zuwa gidansu Nimra, kuka ya hango tana yi tana fadar shi yayi kisa ba ita ba, hakan ya sake haddasa fada a tsakaninsa da mahaifinsa har ya sake korarsa a karo na biyu...! Firgigit ya farko daga bachin na rana ya yarfar da hannu ya shafe wuyansa, tsabar kyamar Waira da yake ko a mafarki ya ga ta taba shi kazanta yake ji, Even though ya san mafarki ne amman hakan be hana shi sake yin wani wankan ba, har mamaki yake in wanda haukar mafarki da kwashe kwashe shi miye hadinsa da kazama da har zai kawo masa ita a bachi, ba kawo ta ne kawai matsalar ba daura masa zaren dake hannunta da tayi a wuya shi ne matsalar domin jinsa yake kamar gaske. Tsaki yaja yana shafa turare a wuyansa, lallai ya yarda mummunan mafarki daga shaidan yake, domin idan ba shaidan ba ta ina za a ga wannan yarinyar kazama ta yi wanka ta yi kyau tsabtsab da ita har su kamshi, a yau kam ya tabbatar da mafarkin rana shirme ne. Sai da ya saka wasu tudafin sannan ya sake komawa bathroom din yayi alwala ya fito ya karbi key din motar Hajiya Jamila ya fice daga gidan, gida biyar ya wuce sannan ya isa inda masallacin unguwar yake, yin Sallah in time kuma cikin jam'i is one of his favorites, sai dai baya jerawa da mutane sai dai ya tsaya a gafe daya, idan kuma ya samu Masallaci ya cika sai yayi sallah a waje, Saboda kar jikinsa ya taba na wani indai ba abokansa ba, sai kuma mahaifinsa da mutanen da yasan suna tsabta a yadda yake so, haka Allah yayi shi akan kyamar mutane da yake har warinsu yake ji wani lokacin. Bayan an sallame ya fito ya dawo gida, a nan ya samu Hajiya Jamila na hada masa cake, bayan ta gama take fada masa ba za a samu flight zuwa Abuja da yamma nan ba, amman ta masa Booking din Private jet, kuma ya jidadin haka cake din kadan ya ci daman he's not that foodie abu kadan idan ya ci ya ishe shi wani lokacin ma Lemu kawai zai wuni a cikinsa. Karar tsayawar motar YaYan Hajiya Jamila ya tuna masa da sarewa, da sauri ya saka hannunsa aljihu yana lalabe kamar a ciki ya aje ta. Oh... Ya furta hakan yana jin wani sabon bakinciki. Lafiya? Sarewata na bari a motar yarinyar can Wallahi Mantuwa ka yi? Eh ban tuna ba sai yanzu Sai siyen wata kenan? Ba za a samu mai kyau irinta a yanzu ba, and akwai wanda ya saka min wani abu a sarewar nan wanda idan na busa take tafiya yadda nake so Zanjabil da yar'uwarta Hurriyya ne suka shigo falo, suna ganinshi suka yo kansa da gudu suna murna, sai dai bacin rasa sarewarsa ya saka be wani sake musu fuska sosai ba, tunaninsa na yadda zai dawo da barsa hannunsa ne, ya san zai sha fama amman haka zai dawo da ita ko da kuwa yakin duniya na uku ne zai afku. Khadeeja Candy Copyright 2023 ...WANI GARI... Khadeeja Candy_ Daddy na kokarin mikawa yarsa tea cup din dake hannunsa Momy ta turo kofar dakin ta shigo, tun daga yanayin annashuwar da ya gani a fuskarta ya san akwai labari mai dadi, domin samun saukinsa kawai be isa ya saka ta farinciki har haka ba. Kamin ta karaso inda yake zaune Ameer ya shigo dakin. Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar Daddy a take ya ji kamar ya warke daga ciwon da yake, cikin yanayi na damuwa da halin da Ameer yake ciki yake kallonsa har ya karaso kusa da shi, Kanwarsa ma kallon mamaki take masa domin babu wanda yayi tsammanin dawowarsa so soon haka, duk a tunaninsu sai mahaifinsa yaje nemansa. For the first time Ameer ya ji yana dan jin nauyin mahaifinsa har ya kasa hada ido da shi. Ina shirye shiryen zuwa nan ya Hajiya Jamila ta kira ni ta ce gata ita da yaranta sun raka Ameer Airport jirginsu zai sauka 5:30 na tura mota ta dauko shi Airport, ni naje daukarsa da kaina domin na san kai yake son gani Momy ce take labartawa Daddy haka tana murmushi, Ameer ya saka hannayensa aljihu. I'm just care about you, an fada min jikinka ya tashi Daddy yayi murmushin da shi kadai ya san na minene ya ma dansa mazauni a kusa da shi. Ba ma iya rabuwa da juna Ameer mutuwa ce kawai ke iya raba a da mahaifi, ba zaka iya rayu idan babu a tare da kai ba, haka nima bana jindadi komai idan baka kusa da ni, Allah ya maka albarka ya shirya ka Momy da Kanwarsa suka amsa da Ameen, shi kuma ya kara matsawa jikin Daddy kamar wani karamin yaro, they miss each other irin na uba da a, a asibitin ya raba dare sannan ya karbi key din Momy ya fita daga Asibitin, family house dinsu ya nufa yana yin horn aka bude masa ma keken gate din, ya kunna kai harabar ya faka motar ya fito ya fito ya shiga falon, kamshin gidansu na dabam balle kuma dakinsa da doka ce a saka masa turare sama da kala daya. What a blessing Ya furta yana jin yadda ya shaki iskar yanci a yanzu kamar wanda ya fito daga gidan yari. Kan gadonsa ya fadi kwance ya ware hannayensa yana jin marmarin macen da addinin musulunci be halal ta masa ba, abun bakinciki kuma babu wayarsa a kusa da shi, Sim din ma sai am masa welcome back domin ba zai iya komawa daukarsa ba he don't think ma idan ya koma zai samu liyin a gurin. Tashi yayi zaune ya nufi gurin da yake aje wayoyinsa ya dauki wanda and ya manta when last yayi amfani da ita ya kunna, sai dai ba shi da liyin da zai yi amfani da shi ya kirata a yanzu, domin liyi biyu yake amfani da su, kuma ya fasa wayar ya bar Sims din a can. Fitowa yayi dakinki ya sauko kasa falon ba kowa daman dare ya raba mutanen kirki duk sun yi bachi. A dole ya zauna akan kujera ya lumshe ya san idan yaje gidanta a yanzu ba lallai ta iya fitowa ta bude masa ba, kuma gashi sisters dinsa duk sun yi bachi balle ya ari Sim dinsu ya saka ya kirata, by this time kuma ya san kowa ya rufe shagonsa. Ba dan Allah ya hakura ba sai dan babu yadda zai yi sai karfe biyu da minti biyar ya tashi falon ya haura sama ya shiga dakinsa, wanka ne first abun da ya fara yi sannan ya saka kayan bachi ya kwanta. Hankali kwance bachi ya dauke shi be farka ba sai da Asuba, gidansu ya shan banban da wasu sauran gidajen da suke Abuja, domin akwai karamin Masallaci a na su gidan ba kamar gidajen sauran masu kudin ba. Da shi aka yi jam'in Sallah Asuba sai dai bangarensa da dabam da yake tsayawa yayi Sallah. Dakinsa ya sake dawowa ya kwanta sai a yanzu yana tunanin ko ya Nimra zata yi idan har yarinyar da ya dauko aka ce ta mutu a motarta? At least ya rage zafi domin ya san zai jefata a matsala, be zama lallai mahaifinta da Maleek da ta hada kai da shi ya bari a hukuntata ba, kamar yadda ya san mahaifinsa ba zai yarda ya bar shi ya amsa sunan kiran kai ba, ko da ta fadi cewar shi ta bawa motar a dole ita za a dorawa laifi, balle kuma shi a yanzu ya shirya karyatata idan har tace shi ta bawa motar. Kamar an tsikare shi ya tashi ya cire tufafin jikinsa ya shiga yayi wanka ya shirya akansa sai kamshi yake ta ko'ina, key da ya shigo da sho ya sake dauka ya fita, Babu wanda ya san da fitarsa a gidan sai masu aikin da suka farka tun da Asuba suka fara aikinsu Momy bata dawo ba saboda kwana da ta yi Asibitin kanensa kuma duk bachi suke. Motarta ya shiga sanin halinsa ya saka masu gadin suka bude masa gate tun kamin ya iso. Tafiyar awa daya yayi sannan ya isa wani madaidaicin Gida da aka kawata da kayan alatu, tsayawa yayi da motarsa yana kallon yarinyar dake kokarin rufe gate din da ke nuna alamar motar da ta wuce ta gabansa a gidan ta fito, ita ma tsayawa ta yi rike da kofar tana kallonsa hanjin cikinta na kadawa domin ta ga fuskar ko waye duk da kasancewar ba da motar da ta