← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 165

Sashe 16

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

saboda tsananin tsabtarsa Ta juya ta kalli dakinta da yake ya mutse, ita kam sam bata ga wani abun kyama ko Allah wadai a dakin ba, ita dai yadda take rayuwarta a haka tana jin dadin rayuwarta sosai. At takfr hur verrr gulta jaget _Yayi tsabtarka?_ Ya fi ni sau dubu Ya fada yana kallonta, sai ta ya mutsa fuska domin Eid ma ganinsa take mai tsananin tsabta da idan zai ci abu sai ya wanke ga wanka a kullum idan kuma aka ce akwai wanda ya fi shi ai abun be burge ba. Bana son irin wadanan mutanen sam, amman fatar jikinsa ba irin wannan bace ko? Saboda tsabta Yayi murmushi mai sauti, ya kama hannunta ya dora saman goshinsa ya yana kallon kyakkyawar fuskarta dake dauke da datti, so yake kawai ta ga yadda suka yi rayuwa da mutumen na dan lokaci kadan domin ya san tana da wannan tsafin da idan ta dafa kan mutum tana iya ganin da jin abun da ya faru a rayuwarsa ta baya. Runtse ido ta yi sai ta fara arba da karar wani abu mai da bata taba jin irinsa ba, karar ta girmin kunnuwanta, hayaniyar da take ji ta yi yawa, dishe dishe ta fara ganin wani abu bata taba gani ba yana gudu wasu kalar na binsa a baya karar karfe da karfe suna gaduwa kamar za su tashi kwakwalwarta, da sauri ta dauke hannunta ta bude ido domin karar da take ji ta girmi kunnuwanta. Kara sosai Abun da nake baki labari kenan Mota, ita suke hawa a madadin dabobin mu Outar.... ota... Ta maimaita tana mamakin wace irin rayuwa ce wannan. A gurinta ya wuni har dare sannan ya kunna mata wutar tsafi ta haska mata dakin na adadin awawanin da zai yi kamin ya kwanta a daidai lokacin da wutar zata mutu. ...WANI GARI... _Na Khadeeja Candy_ Kai ta daga sama ta kalli Namra dake tsaye tana kallon duk abun da yake wakana a kasan murmushi kawai ta yi ta maida kanta kasa ta cigaba tafiyar ta har ta shigo cikin gidan, sai da ta duba ko'ina bata ga Ummi ba sannan ta hau sama ta duba dakin Ummi nan ma bata ciki, sai ta zagaya ta inda yar'uwarta take tsaye tana kallon harabar gidan, tun kamin ta karasa kusa da ita ta ce. Ummi bata dawo ba? Suna can gurin case din Kirana fa ta yi wai na dawo gida, ta ji abun da na yi miki Na fada mata komai ai, akan wani banzan saurayi zaki wulakanta ni Duk maganar da suke Namra bata juyo ta kalleta ba, ita kuma bata fasa murmushi da mamakin halin yar'uwarta ba. Kyakkyawa ne ko ba haka ba? Yana da masifar kyau Namra baki gani ba Kyaun ne matsalarki? Yana da kwarjini, yana da natsuwa yana jin kanshi, samarin dake jin kan su ba su cika kula mata ba, domin gani suke kowace mace ba tsararsu ba ce Magana take tana murmushi domin ji take kamar yana a gabanta tsaye tana kallonsa. Namra ta juyo ta kalleta. Ke wai tsaya ba dai shi kika bawa motarki ba? Mota kawai kika gani? Ke baki ga alamar zan iya ba shi rayuwata ba ma? Love is stupid.... Ta fada tana jan tsaki, tsabar haushi ma ya saka ta bar mata gurin, Nimra ta yi murmushi domin ita kadai ta san abun da take ji a game da Ameer. Bata sauko ba sai da ta hango Shigowar iyayenta tare da Yayanta Maleek da kuma Mahmood, kamin ya zagayo ta sauko har sun shigo cikin falon. Ummi an kama shi? Shi ne abun da ta fara tambaya, Hajiya Zahra ta yaye mayafinta ta zauna saman kujerar da ba a isa a saka a gidan wani karamin mai arziki ba tana fadin. Abban ku be bari na shiga ciki ba, a mota suka bar ni ban san ya aka yi ba, sai fada yake min wai miyasa na bi su Nimra na kallon Abiey ya dankaro mata harara. Daga yau kar mu sake fita akan wani issues irin wannan ki dauki mahaifiyarki ku bi bayanmu Nimra ta marairaice fuska try to act innocent. Ba laifina ba ne fa, ita ta ce sai mun kaita saboda hankalinta ba zai kwanta idan tana gidan nan ba Na fada miki dai, this should be the last, kuma an rufe case din nan daga yau kar na sake jin maganar mun yi solving da mahaifinsa Ummi ta kalleshi da sauri tare da mikewa tsaye Nimra da yar'uwarta ma haka, Mahmood da Maleek da suka san abun da ya faru ne kawai ba su yi mamaki ba, ba ma kamar Maleek da hakan yayi masa dadi. Saboda me? Shiyasa ka hana na shiga? Yaron ya fi karfin a hukunta shi ne? Taya mutum zai nemi kashe min yaro kuma kace kun sulhunta Ba sulhu nake so ba, hukunta shi nake son ayi idan ya saba yi ana kyaleshi to yanzu ya kai karshe Abiey be ce mata komai ba, ya wuce dakinta sai duk suka bishi da kallon mamaki, har sai da ya shige kofar da zata sada shi da bangarensa. Sannan Ummi ta juyo tana kallon Maleek. Waye yaron nan ne? Ya fi karfin kowa a garin nan ne? Waye Ubansa? Nimra ta dafata tana kokarin kwantar mata da hankali. Ummi, Abiey fa ya fiki son yaya tun da kika ga ya bar maganar nan abun ya fi karfinsa ne please calm down Yaron ba a san inda yake ba Ummi, DSS din da aka tura su kama shi sun ce ba su same shi a gidan ba, kuma step mother dinsa ta zo tana kuka ta yi ta ba mu hakuri, ta ce yanzu haka mahaifinsa ya koreshi ya karbe komai nasa saboda abun da ya aikata, kuma mahaifinsa yana can ya fadi ba lafiya Mahmood ne ya bata amsa, daman can bata sa ran samun wannan dogon bayanin daga bakin Maleek ba. Karya ne sun shirya hakan ne saboda su kare dansu Namra ta fada, a daidai lokacin da wani tunanin na dabam ya zowa yar'uwarta Nimra. Waye Ubansa? Ummi ta tambaya tana jin kamar ba zata iya kyale maganar nan hakan nan ta tafi ba. Maleek ya fara tafiya ya nufi kofar fita daga falon domin ya tsawalla dan tsayin da yayi a falon da kanennensa da kuma mahaifiyarsa. Sunan Yaron Ameer dan gidan Alhaji Bashir something Mr Bashir shi ma dan Kano ne Da wani irin karfi Ummi ta zabura sakamakon bugawar da zuciyarta ta yi cikin rashin shiri, sai ta ja numfashi da karfi. Nimra ta nufi Mahmood tana fadin. Ka san shi Mahmood? Kana da hotonsa? Na san shi, lemme see Ya ciro wayarsa ya shiga Instagram yayi searching Account dinsa, a nan yayi ta haduwa da fake account da sunan nasa, sai dai be damu da hakan ba domin abun da ya kai shi Application din neman hotonsa, hotunansa ya kama ya mikawa Nimra, ita ma faduwa gabanta yayi jikinta ya fara rawa kamar marar gaskiya. WAIRA POV. By the time din da Eid yake tsammanin ta yi bacci sai ya kashe wutar, ita kuma ganin wutar ta mutu ya saka ta tashi zaune ta fito daga cikin dakin, a bakin kofa ta zauna tana kallon sama, taurarin da suka yi ma samaniya ido suka fara burgeta kallonsu take sosai kamin ta fara kirgasu. Tun tana zaune har abun ya kai ga ta mike tsaye ta fito waje gaba daya yana juyawa idonta na sama kamar wanda aka cewa idan kika kalli kasa zaki mutu, bata ankara ba ta ji ta bugi mutum da sauri ta dawo da dubanta gabanta sai ta yi arba da wani saurayi da be wuce sa'ar Eid ba, dariya ta yi ta sauke kai kasa tana cewa yayi hakuri, shi ma dariyar yayi ya rike walkin dake kugunsa yana kallonta. Ba sai kin ba ni hakuri ba, laifina ne Laifina ne dai ban kalli gabana ba sai sama Ba ki yi bachi ba har yanzu me kike yi? Bana komai bachin ne be zo ba, kai miyasa baka yi bachi ba Ta tambaya yana saka yatsanta a baki tana watsa da yawun dake cikin bakinta. Daman na kan dade ban yi bachi ba Waira.... Kamar daga sama suka ji muryar Eid daga ita har shi juyowa suka yi suna kallon inda sautin muryar ke fitowa, Saurayin ya kalleta. Matsalar kenan Eid baya barin kowa ya rabe ki, ba ya barin kowa yayi magana da ke, shi yake tafiyar da ke Ita dai ban da kallonsa babu abun da take domin bata fahimci komai a cikin maganarsa ba, karaso Eid yayi gurin fuska babu annuri. Mu je ki kwanta Bana jin bachi Ta amsa kai tsaye sannan ta juya zata cigaba da tafiya, wani irin fisgota yayi ta dawo baya da karfi ya daka mata tsawa Muje ki kwanta A ka'idarta ba a mata fada, haka zalika ba a mata tsawa, sai kawai ta fisge hannunta ta yi tafiyarta wani gefen dabam, kallon Saurayin kawai Eid yayi ya bi bayan Waira, gurin wasu manyan duwatsu ta nufa ta zauna tana kallon wajen garin iska mai dadi na kadata. Kar wani ya sake miki magana ki amsa? Ta juyo da karfi kamar ta dake shi. Zan amsa ko yanxu wani yayi min magana sai na amsa, ba ruwanka da ni Kallonta kawai yayi be ce komai ba, ya juya ya fara tafiya, ba shi da halin hukunta wacan saurayin da ya haddasa masa ruruwar wuta a zuciyarsa, domin idan yayi masa wani abun dole za a gani idan aka yi tsafi, ya san kuma babu makawa dole ne sarki ya hukunta shi, Waira ce kadai ke da ikon ta illata wani ko ta kashe shi a kyaleta, sai dai ayi mata fada ko dan hukuncin da be taka kara ya karya ba. Jin kamar ba zai iya barinta a gurin ba ya saka ya dawo ya sake cewa ta tashi ta je ta kwanta. Ba zan kwanta ba, na fada maka babu ruwana da kai Matsawa yayi kusa da ita sosai ya dafa kafadarta, tana kokarin kai hannunta ta janye na shi hannu ta ji tafiyar wani abu mai kamar Maciji ya shiga cikinta yayi bayanta da
Chapter 16 · 0% Book details