Sashe 154
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta fada masa abun da take nufi ba, wata kila tana tsoro ne ko kuma tana jin kunya. Eh haka ne, dole ne sai an sake daura muku aure na musulunci, yanzu dai idan na fahimta Maleek kike so kenan? Abun ka da wanda ba bahaushen mutum ba sai ta daga kai tsaye tana kuka. Eh amman zai iya min fada, shi baya so na nindai ba zan auri Ameer ba, Ya Maleek nake so Ta kwana gidan sauki, daina kuka yarinya zan yi magana da shi idan ya amince shikenan idan kuma be amince ba shi ma ba zan masa dole ba kamar yadda ke ma ban miki dole ba Ta amsa da kai sannan Abiey ya mike tsaye ya nufi bangarensa, tsoron kar Maleek ya dawo ya same ta a falon ma ya saka ta shige dakin Namra ta kwanta kwanan dole, amman bachi ya ki daukarta sai ta da dare ya raba. Washe garin Abiey ya labartawa Maleek abun da ya faru tsakaninsa da Nuwaira bayan na gama fadawa Daddy yadda suka yi a waya, Maleek sai ya rasa me zai yi farinciki ta fadi shi take so, ko bakincikin dan'uwansa Ameer ya rasa? Domin ya lura Ameer yana son Nuwaira sosai sai dai ba su isa su yi mata dole ta so abun da bata ra'ayi ba. Amman Ameer zai ji wani iri idan ya ji, zai shiga damuwa Ina kyautata zaton zai fahimta, kuma idan har ya sauya a yadda ni da kai muke gani zai yarda ya karbi wannan kaddarar ne Amman Abiey abun is some how ta ya zai kalleta a matsayin matata? Ta yadda zaka kalleta a matsayin matarsa da ace abun da yake nema ya samu, idan baka ra'ayinta kai ma ba zan maka dole ba kamar yadda ban mata dole ba, zaka iya gabatar da wadda kake so sai mu bincka iyayenta da tarbiyarta kamin lokaci ya kure mana Zan yi tunani akai Abiey, a bani kwana biyu Daga haka ya mike tsaye ya fice daga falon, ji yayi baya bukatar ganin kowa sai Nuwaira a lokacin dan haka ya nufi bangaren Ummi, yana shigowa ta ganshi sai ta saki kular hannunta ta juya zata bar falon da gudu, cikin hanzari da jarumtaka ya sha gabanta sai ta duke ta rufe kanta, tunanin take zai mata fada ne ko ya fada mata magana marar dadi akan abun da ta yi, domin bata da masaniyar yana sonta ko akasin haka all what she knows is ita dai tana sonsa. Dukawa yayi gabanta ya kalleta gabansa na bugawa da mugun karfi, har lokacin kuma ya kasa faricikin ya kasa bakinciki kuma ya kasa ganin laifinta haka ma yana ganin babu hujjar da zata saka ya zargeta da kin Ameer. Me ye na rufe idon? Fada zaka min? Saboda kin san abun da kika yi baki kyauta ba ko? Ni dai kawai na fadi abun da yake zuciyata ne Ta amsa da muryar dake nuna alamar tana daf da fashewa da kuka, har lokacin kuma bata yarda ta dago ta kalleshi ba. And now murmushi ne a fuskarsa sometimes tana abu kamar wata yar 6 years. Me yasa baki son Ameer? Ni dai kawai bana son shi da aure? Sai wa? Ta ki yarda ta amsa masa, har ya gaji da jira ya mike tsaye ya rumgume hannayensa yana kallonta. Ba fada zan miki ba tashi tsaye Ta ki ta mike tsayen kuma ta ki ta dago kan, har sai da ya gaji da tsayuwa ya fice daga falon, yana maida kofar ya rufe sai ya jingina da kofar ya lumshe ido yana murmushi... AMEER POV. Zagaye zagaye Daddy yayi ta masa sannan ya fada masa gaskiyar abun da Abiey ya fada masa na irin amsar da suka samu daga gurin Nuwaira. Ameer yayi murmushin da hausawa ke cewa ya fi kuka ciwo ya hade wani abu da ya tsaya masa a makoshi. Daman na saka ran haka, domin na lura da yadda take mu'alama da ni babu so a ciki Wata kila lokaci take bukatar a bata... Aa Daddy, da ace kudi yana siye rago kyau na san zaka iya siya min, idan har bata son aurena bana son na aureta a dole kuma iyakar son gaskiya da zan nuna mata a yanzu shi ne na barta ta auri wanda take so, ko da kuwa bera ne, indai hakan zai saka ta farinciki ni ba ni da matsala zan jur har na saba, sometimes dole ne mu karbi kaddara, Humairah tana yawan fada min haka, kuma ni ma ya zamin ishara wata ma rai ta rasa saboda ni, ni me yasa ba zan iya hakuri ba? I have to accept this Daddy Duk kokarin da yayi na danne zuciyarsa sai da hawayen bakinciki suka zubo a idonsa. Haka ne, wani lokacin kana ganin abu sai kuma ya zama ba alheri ba ne a gareka, Allah ya saussauta maka Ameer, zan yi magana da Abiey ya daga maka kafa har ka warke daga wannan ciwon kamin ka samu sukunin son wata a ranka Ba zan taba warkewa ba daddy har a bada, kuma ba zan bari hakan yayi tasiri gurin hana ni cika burin Ummi ba, wannan ne lokacin da zan amsa sunana na cikeken musulmi mai yarda da kaddara Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Ameer cike da tausayi. Allah zai maka mafita soon Ameer In Shaa Allah Ya tashi ya fice daga falon. Dakinsa ya shiga ya kwanta sai ya ji gadon baya masa dadi, ya tashi zaune zaman ma babu dadi, a take ya fara safa da marwa yana son yayi kuka ya kasa domin abun ya fi karfin kuka a gunsa, sai dai mamaki kawai yake da dariya wani gefen kuma yayi murmushi. Da ya ji kamar ba zai iya da zaman gidan ba ne ya saka ya fice daga gidan ya nufin gidan kakarsa, a nan kam ya samu sukunin yin kuka bayan ya budewa Humairah zuciyarsa. Dole ce kawai ta saka ya shiga gidan Abiey da daren ranar domin ya gama shirinsa na tafiya ziyarar Ummi, kuma yana son tafiya yayi ma Abiey Namra Mahmood da Maleek sallama har ma da Nuwaira. Daya bayan daya ya biyu yana sallama da kowa, Abiey ya dade yana masa nasiha kuma ya nuna masa babu hannu ko laifin kowa a ciki, bayan ya gama karanta masa muhimmanci yarda da kaddara, hakan da Abiey yayi masa ya saka shi jin sanyi domin be saka tsammanin Abiey zai zaunar da shi ya masa nasiha mai ratsa zuciya haka ba, bayan duk abun da ya faru a tsakaninsu sai a yanzu yake tsantsar nadama da bakinciki abun da ya aikatawa Nimra, a yanzu ya fi gane yayi kuskure fiye da baya. Bayan ya fito ya shiga dakin Mahmood ya gaisa da shi kuma yayi masa bankwana tafiyar da zai yi ya shiga dakin Namra a nan ne hankalinsa ya tashi a lokacin da yayi arba da Nuwaira abun ka da mai karfin hali kuma sai kallonsa take, sai yayi mata murmushi ya ce. Zan tafi gurin Ummi gobe kina da sakon da za a kai mata? Ta kalli Namra sai ta kasa cewa komai. I'm sorry for loving you Nuwaira, i was afraid of leave you, amman yanzu na fahimci we are not mean for each other, ina miki fatan alheri kuma ina miki addu'ar Allah yasa wanda kike so ya rike ki amana ya so ki fiye da ni, ban cancanki ba Nuwaira a gane hakan a yanzu, kin cancanci auren tsabtatacen mutum wanda kika so saboda samun farincikinki, baki cancani mutum mai son kai da rufe ido ga bukatun wasu ba irina, duk haka kuma zan miki godiya domin zuwanki a rayuwata ya canja rayuwata ya koya min darasi da karatun da ban san da shi ba a baya Hawaye ya sauko idonta maganarsa na taba ta, sai dai ita dai ta san har ga Allah bata jin son Ameer da aure, ko da kuwa zata rasa Maleek ne, ba Ameer ba har Eid da yake dan'uwanta bata jin zata iya aurensa, haka ma bata jin tana yi ma Sulem dinta irin wannan son, Maleek kawai wanda yayi nasarar cike wannan ramen a zuciyarta. Bana nufin cutarwa dan Allah ka fahimta Sai ya mata murmushi ya girgiza mata kai. Noo please don't cry idan ban fahimce ba waye zai fahimce ki? I know what you mean Ya kalli Namra dake rike da system. Zan wuce gurin Ummi gobe ayi mana gafara ban san ta rai ba Ameer dan Allah karka hukunta kanka karka dorawa kanka laifi akan abun da ya faru, dukan mu muna kuskure, please don't feel bad akan abun da ya faru, i wish i could do something You're such a wonderful Sister, thank you sai na dawo Ya juya ya fice daga dakin, sosai tausayinsa ya kama Namra. Ta juya ta kalli Nuwaira dake kuka. Ina ma ban dawo ba, na bata ran mutane a nan na saka wasu a damuwa Ummi ma ba zata ji dadin haka ba, me yasa zan zaba a tsakanin yan'uwa? Namra ta aje system din hannunta ta nufi inda Nuwaira take tsaye ta rumgumeta. Baki da laifi ke ma, Ameer ba shi da laifi haka ma Maleek, so baya duba kusanci ko tazara, haka baya duba alaka da yan'uwanta baya duba arziki da talauci, na tabbatar da ace Ya Maleek ne ya rasa ki zai iya rasa ransa ma Nuwaira ta dago ta kalleta. Ya Maleek din? Kwarai Nuwaira yana sonki fiye da yadda kike tunani, sai dai yana da wani irin kawaici da karfin hali, yana da halin girma da kokarin na danna abun da yake ji a ransa Amman be taba fada min yana so ba Yana duba alakarki da Ameer ne, amman a yanzu komai ya zo karshe dole ne kowa ya karbi kaddarasa kuma ya yarda da gaskiya Nuwaira ta maida kanta a kirjin Namra ta kwantar tana tunanin Maleek din. Gaba da rikicewa Maleek yayi a lokacin da Ameer ya sauko kasa, sai ya dan juya baya yana taba kayan dake dinning din, kunyar kallon Ameer yake kuma yana jin kamar be kyautawa Ameer din ba. Ameer na ganin haka ya isa gurinsa ya saka hannu