← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 165

Sashe 140

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

da kai ba? Why Ameer? Idan tana sonka ba zata boye maka ba, kuma ba zata tafi ta barka ba Tafiyar kamar ta cilas ce Amman me yasa bata fada maka tana kaunarka ba kafin ta tafi? Ita ba karamar yarinya ce kamar wadda aka haifa yau ba, tana wayo Ameer fada min ya aka yi ka san bata sonka? Saboda ta fada min bata min son aure, amman da zata tafi ta tsaya tana kallona not knowing ina ganinta kuma ta yi kuka sosai Wata kila tana ganin rashin kyauta a abun da ta furta maka ne, kukan mace ko far'ar ta ba shi yake nuna soyayyarta ba, ka yi addu'a Allah ya tabbatar maka da duk abun da ya fi zama alheri nima kuma zan taya ka Ina kan yi kuma zan dage Thank you, ina rokon Allah ya kula min da kai ya yaye maka damuwarka ni ma kuma ya yaye min tawa cikin ruwan sanyi. Ya jikin Ummi? Ameen Ya Allah, jikinta yana nan a yadda yake Abiey ma yayi min maganar fita da ita waje kuma yana son a tafi tare da ni Wow da gaske Ameer? Abiey ya yi maka magana da kanshi? Yeah ni ma na yi mamaki Please ka ba shi duk wani hadin kan da yake bukata, kuma ka ga tafiya a tare da kai jinyar Ummi zai baka damar kebewa da mahaifiyarka, zaka kara saninta ka rabe ta ita ma kuma ta zauna da kai hakan zai kara mata kwarin guiwar tafiya ko'ina ne Shi ma haka ya ce, kina tunani irin na manya Humairah that's why i like you I like you too, daman i just call na ji ya ka tashi how you're feeling Na farka da tunani da kewa but kiranki ya saka na ji sarai thank you for the care zan shigo anjima na duba kaka kuma na duba abubuwan da babu Okay na rubuta komai idan ka zo zamu tafi tare mu siyo Okay bye Ya sauke wayar yana jin relief ba kamar dazun ba da rasa ma me zai yi, main door ya nufa yana kiran line Ummi domin gurinta yake son fara zuwa after taking a shower. MALEEK POV. Kusan rabin aikin dakin shi yayi domin aiki na karfi kamar dauke abubuwa a fitar daga dakin, shara ce kawai Nuwaira ta yi sai dauke kakanan abubuwa, babu komai a dakin yanzu har berayinta saboda babu mai ba su abinci tuni suka sani inda dare yayi musu, wadanda suka gudu tare da ita kuma ta bar su a dajin da maciji ya cijeta. Ita take dauko ruwa a koramarsu tana kawowa yana yayafawa kasar dakin domin ba sumitin ba ne balle ma ayi maganar tile, ana shara kura na tashi haka dai har suka gama tsabta ce dakin. Maleek ya nufo inda take tsaye tana kallon dakin ya ce. Babu katifa akan me zaki kwana? Ta juya ta nuna masa wani raggar katifar ka a da ya jefar a waje ta ce Da akan wacan nake kwana So wacan katifa ce? Eh ta ka a ce ba irin ta ku ba Oh.. Da me kike rufa? Ta nuna masa tsuman da ya jefar, sai kawai ya saka dariya kamar ba shi ba, shi dai mamaki yake ace haka take rayuwa. The most dirty girl in the world Ta dan bata fuska. I mean can baya ba a yanzu ba Ta yi dariya Kai ma kalli kanka ka yi datti ai Ban tana shara ba a rayuwata sai yau, ban taba gyara dakina ba, amman gani ina gyara naki, and ni daman na yi tunanin tafiyar ba ta kwana daya ba ce shiyasa na zo da wasu tufafin a mota ina da extra kaya a mota, katifar ma da na san haka zamu tarar da dakin ai sai mu yi guzuri Wannan karon ita ma dariya take. Sai mu dauko katifa mu taho da ita? How Yes ko ma ta yaya ne dai sai mun zo da ita a mota Ta fashe da dariya, dariyar ta saka shi dariya kadan, sai ta kalleshi yadda dariyar ta yi masa kyau sautinta ki fita da dadi da mazanta. Ya Maleek ashe kana dariya? Sai ya daina fitar da sautin dariyar domin shi ma be san tana fita haka ba, and ya manta when last ma yayi dariya mai sauti da saka zuciyarsa nishadi irin yau since yana tare da abokansa tun suna in group, sai kuma a lokacin da yake kebewa da Abiey da Mahmood suna hira, a nan idan abun dariya ya tashi yana yin dariya idan babu mata ko Ummi ko kuma kannensa a kusa. I guess ina yi, gashi dai yanzu kin gani Amman baka taba yi a gidanku ba Gashi ina yi a garinsu Nuwaira ai Magana yake kamar ba shi ba, every sentence every word da nishadi da annashuwa suke fita a bakinsa. Tana kallonsa sai kawai suka fashe da dariya at the same time kamar wasu mahaukata. What are we laughing? Ya tambaya yana kokarin maida dariyarsa murmushi, sai kallon Nuwaira yake da har lokacin dariya take har da hawaye. You're so beautiful Ya fada a ransa, a zahiri kuma kallonta kawai yake yana murmushi har ta gama dariyar. Wani abun da Nuwaira bata yi tsammanin za a barsu, su aikata ba shi ne shigowa da wasu abubuwan da ta yi guzurinsu tun a garin Abuja, Maleek ya dauko jakarta kayansa ita kuma ta dauko wasu daga cikin abubuwan da zata iya, suka dauko wasu abubuwan ci da Ummi ta bata domin samun abun kaiwa a bakin salati. Duk wani motsi na su yana kan idon jama'ar garin suna kallonsu kamar sun samu tv, musamman ma wadanda ba su taba gwada barin garin ba suna ganin komai na su bakon lamari, wadanda suka saba bawa idanuwansu abinci kam hakan ba bakon abu ba ne a gurinsu. One of those laces da aka bata ta bude ta shimfida a kasa, Maleek ya leka bandakinta ya fito yana jin kamar zai yi amai domin be saba shiga irin wannan bandakin ba, kuma be jin zai iya shiga nata ma. Babu wani guri da zan iya yin wanka? Zaka iya yi a cikin korama? Ta tambaye shi bayan dogon nazari da tunanin inda zai yi daidai da rayuwarsa. Maybe bana son canja wasu tufafin ban yi wanka ba na yi datti da yawa Muje na nuna maka Shi ya fara fitowa daga cikin dakin sannan ta biyo bayansa sai da suka tafiya ta tsaya ta dube shi. Ya Maleek ko dai ka hakura da wanka har ka koma gida? Why? Don't tell me zaki koma ma rayuwarki ta baya No ina jin tsoron kar Eid ko sarki su yi maka wani abu na cutarwa Zan yi addu'a kamin na shiga, kuma na yi addu'a kamin na fito babu abun da zai same ni Amman... No amman baki ga yadda nake rayuwa ba? Ha hankalina kwance? Ta daga masa kai cikin damuwa. Muje Ta cigaba da tafiyar ba dan ranta ya so ba, shi kam kalle kalle kawai yake har suka isa gurin wasu abubuwan suna burge shi, domin an kawata su sosai ga itatuwa ko'ina suka bi, uwa uba ma da suka isa koramar yadda ruwa ke saukowa daga kan duwatsu suna zuba gwanin burgewa. Cire dankwalinki Ba kuna cewa ba kyau mace ta bayyana gashin kanta da jikinta ba? Kamawa ta yi ai cire wani abu zan nuna miki Ta cire dankwalin hakan ya bawa yalwatacce gashin kanta da ya sha gyara damar saukowa bayanta. Juya Bata iya yi Maleek musu tun asali hakan ya saka ta juya bayanta. Sai ya saka dankwalinta ya daure mata ido gam yadda ba zata iya ganin komai ba. Ya Maleek minene? Bana son ki kalleni ne Ya cire rigar vest din dake jikinsa ya daure hannayenta ta baya. Ki tsaya a nan sai na fito Ba tsirara yayi ba rashin riga a jikinsa da kuma short din ya bari a jikinsa be baya son Nuwaira ta kalleshi a haka. Sai da yayi addu'a sannan ya shiga gefen koramar ya tsaya yana wanke jikinsa. Tana tsaye a gurin da ya barta gabanta na faduwa ganin take kamarba zai gama wankan lafiya ba, zuciyarta na ta raya mata Eid zai iya masa wani abu. Ya Maleek baka gama ba? Na gama... Ya rada mata daidai saitin kunneta, kamin ya kwance mata hannunta ya bude mata ido har ta matsu. Ta dafe zuciyarta tana kallonsa sama da kasa, ya wanka jikinsa fes ya canja tufafi a yanzu jean ne a jikinsa da T-shirt. Muje A tare suka jera suna tafiya, ita kam sai hakura ta yi da wanka domin ita ma ta ji ba zata iya shiga bandakin ba, kuma bata son ta yi nisa da Maleek jikinta kawai ta wanke ta fita daga dakin har sai da ta canja tufafi sannan ya dawo. Idan za su yi Sallah sai da ya duba agogo ya gane lokacin yin Sallah yayi domin babu masallaci a kusa da garin ma balle kuma garin, a cikin kayan kwalan da makulashen da Ummi ta yi mata guzuri suka ci, dan ruwan gorar da yayi musu saura ya sha rabi ya bata rabin ta shanye. After sun gabatar da Sallah Isha'i ya dauko wayarsa yana ta dubawa rashin shigar kira ya fara damunsa domin ya san hankalin iyayensa zai tashi. Ya kamata ka tafi gobe Ba tafiyar ce damuwata ba, rashin samun network ne damuwata, ba zan tafi na barki ba ba tare da na yi magana da sarkinku ba, kuma Nuwaira ko da na yi magana da shi i just feeling like ba zan iya barinki a irin wannan rayuwar ba Ban san abun da suke ma shiri ba, amman wani be taba karya dokokin garin nan kuma aka kai wannan lokacin Sarki be saka an kama shi ba, ko kuma a hukunta shi, amman ni har yanzu be aiko min ba, kuma Eid be dawo ba, ina ta jin tsoro Ya Maleek kar su cutar da kai Ya jingine wayarsa domin ta haska dakin da babu komai a cikinsa sai duhu, without saying anything, ya yarda addu'a zata yi masa aiki kuma yana tare da kariyar Ubangiji but deep down inside him
Chapter 140 · 0% Book details