Sashe 10
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin motar ya wanke idonsa ya kurkure bakinsa sannan ya saka hannu ya lalabo wayarsa ya kunna kamar jiran yake a kunne wayar sai ga kiran mahaifiyarsa Hajiya Zahra ya shigo a take. Hello Maleek kana ina? Ina kake? Me ya same ka? Yayi shiru kamar mai tunanin abun da zai fada, ya daga gorar ruwan ya cika bakinsa ya hade. Miya faru? Kamar ya me ya faru? Tun jiya baka dawo gida ba kuma wayoyinka a kashe ko'ina na bincika ba a ganka ba Yeah... Ya fada yana tuna abun da ya faru, jiya yana tare da abokansa ya fara jin bachi, ya shiga motarsa har wani saurayi ya zo ya taimaka masa.... Kamar walkiya haka komai ya dawo masa a akwakwalwa lokaci daya ya tuna komai da sauri ya jefar da ruwan dake hannunsa. Who's that guy? Ya tambaya a yayinda wayar take a kunnesa. Waye? Ummi ta yi zaton sa ita yake, sai ya kashe wayar ya shiga motarsa cikin wani irin bachin rai da bakin ciki marar misaltuwa, kam yayi ma motar key kira ya sake shigowa a wayarsa, daga Abiey har na Kannensa da abokansa be daga ko daya ba, tukin kawai yake yana tuna yadda saurayin yayi kissing dinsa kamar a mafarki. Ransa be kara baci ba har sai da ya isa gidansu yana faka motarsa mahaifiyarsa da kanensa suka fito da sauri sannan mahaifinsa dake bayansu, kallo daya yayi musu ya fahimcin suna cikin tashin hankalin rashinsa musamman ma mahaifiyarsa da har lokacin kuka take, ta matsa kusa da shi sosai kamar ta rumgume shi sai dai babu dama domin danta baya son haka. Maleek ina ka shiga? Ka daga mana hankali miyasa ka kashe wayarka? Kamin ya amsa tambayar Ummi Mahmood ya jefo masa tasa tambayar. Ina ka shiga Maleek? Jiya babu wanda yayi bachi a gidan nan kuma an bincika ko'ina ba a ganka ba Ya dauke idonsa daga kallon kanensa ya kalli Abiey da shi ma tambayar yake masa. Ina ka shiga Maleek? Ya amsa kiran wayar da Abdull yake masa. Abdull ina gida Ya sauke wayar ba tare da ya jira abun da abokinsa zai tambaya ba. Sannan ya kalli mahaifiyarsa dake ta zubar da hawaye tausayinta ya kama shi. Ummi lafiyata kalau Ina ka shiga? Ban sani ba, na fito daga inda muke zama zan dawo gida na kwanta sai bachi ya dauke ni Cikin kallon rashin fahimta Abiey ya ce. Shigo ciki A tare suka dunguma gaba daya suka shiga cikin falon, kowa ya samu guri ya zauna sai kallon Maleek suke da idonsa suke da ja har lokacin ga wani ciwon kai da yake jin yana son saka shi gaba. Ya fara shimfida musu labari tun daga fitarsa gida har zuwa isarsa Q-town da abubuwan da suka faru be boye komai ba ciki har da kissing dinsa da Guy yayi. Maybe wani abu aka saka maka a drinks din Mahmood ya fada Maleek ya kalleshi yana daga masa kai. Ni ma abun da nake tunani kenan, kuma shi ma wannan saurayin turo shi aka yi Wa zai maka wannan? Wannan kuma sai na natsu ko kuma wani za'ayi ma aka yi kuskure Ko dai abokin da kuka samu matsala da shi ne? Abiey ya tambayar yana kallon wayar Maleek dake ringing. Karka daga wayar nan, bari mu gama magana Maleek ya aje wayar gefe ya shafa kansa. Ba na jin zai yi haka Wani lokacin wanda baka tunani shi zai aikata maka abu, wata kila kai baka dauki abun da zafi ba amman shi ya dauka kuma gashi har ka ce wani yayi kissing dinka wannan abun ba a saba da shi ba, kuma baka san manufarsa ta yin haka ba Cewar Namra cike da damuwa. Siyasa ai ba zamu kyale ko waye ba, musamman yadda ya tashi hankalinmu a gidan nan jiya, a inda ya kaika ya aje wani abu zai iya samunka a can din ma, kuma duk wanda zai maka wannan abun zai iya silar rasa rayuwarka, dole mu gane ko waye wannan tun daga kan drink din da ka sha Abiey ya fada with serious face, Maleek ya kalleshi cikin yanayin dake nuna baya son iyayens su shiga cikin lamarin domin yana jin kamar Ameer ba zai iya masa haka ba, duk kuwa da kasancewar wani bangare na zuciyarsa na raya masa shi din ne. Abiey wannan a tsakaninmu ne? Hajiya Zahra ta daka matsa tsawa. Wani irin a tsakaninku? A tsakaninku wani zai maka haka? Wannan shi yake nuna friends dinka ba mutanen kirki ba ne, su waye ma friends din duk ba mu sani ba, basa zuwa gidan nan sai dai ka je can kana haduwa da su wani guri Abiey ya saka hannunsa ya ciro wayarsa dake aljihun jallabiyarsa yayi dialing. Duk masu aikin gurin sai an dauresu sai sun fadi wanda ya saka su Abiey kar aja abun nan da nisa kar aje inda ba a so Cewar Maleek domin ya fi son a bar maganar a hannunsa. Ba za a bari ba, Maleek kuma sai an hukunta yaron nan ko dan gidan uban waye, domin zai iya kashe ka ma Ummi ta fada cikin bacin rai, Nimra ta ce. And the most annoying part ma Yaya baya iya zama ya fadawa kowa damuwarsa sai dai ya bar abu na cinsa Allah kadai ya san abun da ya faru a tsakaninsu amman be fada ba, gashi abu har ya fara wuce gona da iri Kallonta kawai Maleek yayi ya mike tsaye ya nufi hanyar stairs. Ja ka a duba lafiyarka, whats if yayi poisoning dinka? Ya juyo ya kalli mahaifiyarsa dake maganar. Zan je, wanka zan yi na yi sallah tun jiya ban yi magariba ba Sannan ya juya ya hau sama yana jin yadda Abiey yake yi ma abokinsa bayanin yadda ansa ya dawo. Ba zan sake bari ya rabi friends dinsa ba, ba mu san su waye yake abota da su ba, ji yadda suka saka shi ko sallah be yi ba, dole ne a hukunta ko waye.... Wannan karon ma Hajiya Zahra ce take maganar cikin fushi tana jin kamar ace wanda ya aikatawa anta haka yana a gabanta. ...WANI GARI... _Na Khadeeja Candy_ WAIRA POV. Tun daga lokacin da sarki yayi mata gargadi sai ta rika ware kanta dabam, daman can bata da abokan wasa sai dai tana dan shiga cikin mutane a yanzu kuma ko fita gida bata yi sai dole, Eid din ma da take sakewa da shi sai ta daina, sai dai hakan be saka ya kyale ta hakan be canja komai daga alakarsu idan bata fita ba shi zai zo ya same ta har cikin gidan, wani lokacin zai mata hira ranar da aljanun kwarai suke kanta sai ta amsa masa su yi ta hira yana bata labaran duniyar da ta sha banban da tata, wani lokacin kuma har ya gama abun da zai yi ya tafi ba zata ce masa komai ba. Sai dai tana jidadin idan yana labarta yadda wasu abubuwan suke a wasu garuruwan kuma yana fahimtar hakan a fuskarta domin ya fi kowa sanin halinta, abun da zai faranta mata ko ya bakanta mata rai. Karar jirgin saman da ya ji ya saka shi riko hannunta ya fito da ita daga cikin dakin da take ya nuna mata jirgin saman, ba a yau ta fara ganinsa ko jin kararsa ba, sai dai yau ne rana ya farko da ya taba labarta mata cewar mutane ne a ciki, kuma tsuntsun yana daukar mutane da yawa har da kayansu, kana ya misalta mata yadda girmansa yake a kasa, ta bude baki sosai tana fiddo idonta waje. Kuma mutum ne yake tukawa? Ta tambaya tana saka hannunta ta tare ranar dake haska fuskarta. Mutum ke tukawa, yana da sauri fiye da tsuntsu Ta dawo da dubanta gurin fuskarsa tana murmushi. A ina yake sauka? Shi ma ya sauko da kansa kasa yana kallonta domin yayi mata tsawo sosai. A can garuruwansu, sun tanadar masa muhalli mai girma sosai wandanda za su hau sai an tantance su suke hawa, kuma sai sun biya kudi Ta sake juyawa tana kallon inda jirgin ya bi amman ko alamarsa babu. Me suke bautawa su? Miyasa komai na su ya banbanta da mu? Saboda sun yarda sun karbi sauyin da duniya ta zo da shi, wanda mu muka kasa haka, na nesa da mu suna da addininai kala kala na kusa kuma na san ana kiransu Musulmai Ya amsa mata yana kallonta irin kallon nan dake tafiya da ruhin mai yinsa. Ina ma ace an baki damar fita wajen gari, da na bawa idanuwanki abinci, na zaga dake duniya ki ga wata rayuwar data banbanta da taki sai dai an iyakance miki iya cikin garin nan, fitarki a garin nan zai saka ki manta hanya dawowa, hakan kuma na nufi rasa rayuwarki gaba daya Ta sauke kanta kasa ta fara tafiya. Miyasa rayuwarsu take burgeka? Rayuwarsu tana da kyau, wani abu na su yana burgewa ke ma da zaki leka ki gwada zama a cikinsu da kin jidadin rayuwar Bata sake ce masa komai ba har suka isa gurin da dade bata zauna ba saboda gargadin da Sarki yayi mata, zaunawa ta yi a gurin shi kuma ya tsaya yana kallon itatuwan da suka kawata gurin ga ruwan dake gudana gwanin sha'awa. Wasu kan kawata cikin gidajensu da irin wannan ruwan Ta yamutsa fuska. Saboda su yi wanka? Ya amsa da kai yana murmushi, a take ta ji ta tsani mutanen domin mutane masu yawan wanka ko son tsabta basa burgeta. Bana son zama a cikinsu Zaunawa yayi a gurin yana kallon ruwan da take kallo. Akwai wanda na taba haduwa da shi, a rana zai yi wanka kamar sau biyar ko sau goma saboda tsabta Kuma baya jin wahala? Baya ji kuma baya gajiya Ya juyo ya kalleta sai ya kama hannunta ya rike. Waira baki taba jin marmarin wani abu da kika rasa ba? Da manyan idanuwanta ta kalleshi tana kokarin fahimta tambayarsa, sai ya saka yatsansa ya daki hancinta. Taya mutum zai yi marmarin wani abu da da be san da wanzuwarsa ba? Ya kallonta yake wannan karon kallon tausayi yake mata, ta tashi babu iyaye kuma tana rayuwa ita kadai