← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 165

Sashe 82

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 4 min read

will never be, kin san abun dariyar? A kullum sai na yi ma mahaifiyata a addu'a, saboda Daddy ya fada min cewar ta mutu, kuma haka zan cigaba da yin addu'ar har a yanzu, domin har yanzu uwata a mace take, ta tafi kenan ba zata taba dawowa ba, ki bayyana gaskiya a yanzu saboda ki sake ruguza rayuwata, me yasa ba ki bar ni na cigaba da kallon mutumen da ya tsaya min a matsayin Ubana ba? Saboda ina son na farantawa kowa kamin na mutu, na tafi ana yabawa ba a bini da bakar addu'a ba, ina son an roki gafarar kowa Ameer? Har da mahaifina? Ba zaki taba samun wannan damar ba, ba zan taba yafe miki ba, kuma ba zan taba kallonki a matsayin uwata ba.. Mahaifinka yana kaunata Ameer, da ace yana raye da baka isa ka fada min wata magana marar dadi ba, ban aikata hakan dan bata ran kowa ba, idona a rufe lokacin bana ganin kowa sai mahaifinka rayuwarsa kawai nake son na ceto Yana kaunarki, amman ke baki kaunar ansa baki son jininsa, shiyasa kika zabi rabuwa da shi, why me? Miyasa baki siyar da Maleek ba? Kamar daga sama suka ji muryar Abiey yana amsa tambayar da Ameer yayi. Saboda Maleek ubansa mai arziki ne, Ameer kuma an siyar da cikinsa ne saboda a nemawa Ubansa magani Duk kallonsa suka yi, Ameer ya ji ina ma be zo duniya ba, da be ga wannan bakar ranar ba a rayuwarsa. Ya girgiza kai ya kalli Ummi yana murmushi. Na gane, tsiya kike gudu, shiyasa da kika samu wani mijin kika watsar da ni, kika tara wasu iyalin? Toh miyasa yanzu kika ruguza tawa rayuwar? Da ace da kika haife ni kashe ni kika yi da na huta ganin wannan ranar, kin cutar da ni ba ki cancanci a kira ki uwa ba, na ga soyayya da kauna daga gurin wadanda ba jinina ba, ya kike son na yi rayuwa a yanzu? Farincikin da nake ne yake kona miki rai? Ummi ta kasa cewa komai sai kuka take, ya mike tsaye rike da takardun ya nufi kofa har ta ya kusa fita ya juyo hawaye na masa zuba cikin ihu ya ce. Kin san zafin da a yake ji idan uwarsa bata sonsa? Da ma gidan marayu suka hai ni, siyarwar ita ta fi min zafi... Ya juya ya fice, kai kawai take iya girgiza masa domin kuka ya ci karfinta ta yarda bata ko iya magana. Abiey ya rikota ya nufo inda take ya rikata. Ya isa haka, and this is the last zuwan da yaron nan zai yi a gidan nan, domin ba zan dauki ya shigo har cikin gidana ya fadawa matata magana marar dadi ba Ummi ta kwanto jikin Abiey tana kuka ta dafe zuciyarta, Yesmin ma kuka take duk da kasancewar a yanzu ne ta fahimci abun da yake faruwa, Waira ma kuka take tana kallon Ummi. Me yasa bana da tunani, me yasa ban yi tunanin zuwan irin wannan ranar ba Abiey? Ameer zai iya shiga wani hali, ba zai yafe min ba na shiga uku.. Shi ne abun da ta iya furta tana kuka sosai kamar zata rusa akin. Zai yafe miki amman ba a nan kusa ba, dole sai kin jure kin zama jajirtacciya, and i promise you zan yi iya kokarin da zan yi na gyara mun gyara duk wani abu da kika bata Ta runtse ido tana girgiza kai, zuciyarta na wani irin zafi kamar an watsa mata tafasasshen talge a ciki. ____________________ Allah sarki Ameer ni dai duk ya fi ba ni tausayi, taya kana rayuwa da iyayenka rana daya ace ba iyayenka ba ne. Wayyo Allah, ku dauke zancen jindadi ko da wahala ake sha a tare wannan kallon da kake musu a matsayin iyaye canja shi ne abu ne mai wahala, and the most painful part yana zaton uwarsa ta mutu ashe tana raye a kusa da shi........ Ni daman can team DEEN ce yanzu ma ina bangaren ansa AMEER, gaskiya Zahra baki kyauta mana ba
Chapter 82 · 0% Book details