Sashe 74
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
wayar da yarinyar nan ta bari da wasika amman ban samu dama ba saboda kun fita hankali a tashe Wace yarinya? Abiey ya tambaya domin shi be san abun da ke faruwa ba ma. Yarinyar da ta so dazun akan cewar ita kawar Nimra ce tana son ta ganta wai wayar Nimra ma tana hannunta, toh na zo na kira wayarka a tambayi Nimra ko ta san da zuwanta ko kuma akwai wanda ya santa a gidan, gudun kar mu barta ta shiga wani abu ya faru bayan dokar da ka saka mana cewar kar mu sake barin Nimra ta fita, toh fitowar da aka yi da ita cikin rashin lafiya sai yarinyar ta saki wayar da takardar hannunta ta gudu, mun bita sai dai ba mu samu nasarar kamata ba saboda ta shiga wata motar kuma mai tukin yaja da gudu sun tafi, sai dai muna son fadada bincike idan ka ba mu dama Abiey ya mika hannu ya karbi wayar da takardar with curious face. Maleek ma da mamakin guduwar ya ja motar suka shiga compound din gidan, Juwairiyyya ce ta fara fita, Abiey ya warwar takardar ya fara karantawa bayan ya gama duba wayar da ya tabbatar ta yarsa ce. I'm sorry Nimra, ban dauka abun zai kai ga haka ba, ina tunanin kiran wayata da kika ba zai gamsar da ke ba kamar ganin wannan sakon nawa a rubuce, na rubuto ne saboda na kara tabbatar miki kuma na jadda miki cewar ni ban tana jin kaunarki ko digo daya a zuciyata ba, na san zaki min kallon maci amana, amman yayanki ya fara ai ni kawai fansa na dauka, kuma ki gode Allah ban taba mu'amala dake ba, wata kila da sai abun yafi taba ki, i wish you all the best, i kila da wanda zai nuna miki so kuma wanda zaki fada sonsa a nan gaba Ameer Sunansa ne daga karshe tare da sa hannunsa, Abiey na gama karantawa ya mikewa Maleek yana jin wata sabuwar tsanar Ameer a ransa. Maleek ya karba ya karanta. Me kake tunani idan ta karanta wannan sakon? Yaron nan so yake kawai ya kasheta Ta sani ai, Ummi ta fada mana haka dazun kamin ka zo, kuma tace shi yayi silar da aka kaita asibiti, daman na fada mata ai bata yarda ba ne, amman ni na san waye Ameer, ba zai taba sonta ba ko dan tana kanwata, sai dai yayi amfani da ita ya cin ma wata manufa Abiey yaja dogon tsaki ya bude motar ya fita ya nufi sashensa. Maleek ya juya gafensa da zimmar bude gambun motar ya hango Waira dake tsaye nesa da motar rike da dan zomonta tana kallon motarsu, jiran take waye zai fito mazaunin direban ko Ummi ce, domin ita kadai take son gani. Samun kansa yayi da tsayawa kallonsa kasancewar bakin gilashi ne na waje baya iya ganin na ciki, sai dai na ciki ya ga na waje, idonta yayi sumtum kamar an dafa shi saboda kukan da ta ci na tafiyar Shuraim. Ganin kamar ba za a fito ya saka ta laraso gurin motar ta saka hannunta daya ta dafa zata leka ciki sai ya sauke gilashin motar, ta kalleshi ya kalleta ido cikin ido, ba tare da tace komai ba ta juya. Waira Ya kira sunanta da tattausan lafazi, ta juyo tana kallonsa sai ta fashe da kuka. Toh me na ce miki kuma na kuka? Ka ce Waira Ta fada tana kuka hawaye na mata zuba kamar bata san zafinsu ba. Hannu ya mika ya ciro tissue a motar Abiey ya mika mata bata tare da ya ce komai ba, sai ta saka hannu ta karba ta share hawayen, sannan ta juya ta koma gurin da ake mata lessons dinta. Sai a sannan ya bude mota ya sauko ya shiga cikin gidan. A kujerarta ta zauna tana share hawayenta har lokacin. Dattijon dake mata darasin ya ce. Kin tafi ki gani ko Ummi ce? Ta daga kai Ummi tana can asibiti gurin Nimra Me ya same ta? Ta tambaya cike da son sani, domin ita dai tun da Maleek yayi mata tsawa dazun saboda tafiyar su Shuraim sai ta boya a kitchen tana kuka duk abun da ya faru bata sani ba. Saboda rabata da aka yi da wanda take so Amman miyasa Ummi ba zata bari ta aureshi ba Baki san Ummi ta haife shi? Na sani Na gani ai Ta ina? Sai ta yi shiru bata son ta fada masa yadda aka yi ta sani saboda kar ya mata fahimta dabam, domin ta lura nan ba kamar garinsu ba ne da suke girmama tsafi. Dariya yayi ya matso kusa da ita A addininsu idan mace da namiji suka sha Nono daya ba a aure, ko da kuwa uwar su daban daban Amman miyasa addininsu yake da zafi? Kai ma ai addininsu kake yi Ta tambaya domin ita dai bata ga illar haka ba, saboda sun sha nono daya ace ba za ayi musu aure ba bayan ba uwa daya ta haife su ba. Ya daga mata kai yana murmushi. Addininmu daya mana, amman ina fatar ba zaki jefar da na ki addinin ba ki dauki na mu, kuma ki daina kuka har idonki ya kumbura haka Kallonsa take kamar mai tunani ko mai son gano wani abu. Ganin hakan ya saka shiikewa tsaye ya isa gurin blackboard din suke rubuta ya cigaba da yi mata darasi. AMEER POV. Sai da suka yi nisa sosai sannan ya rage gudun da yake ya kalli Humaira dake gafen motar tana kukan da babu hawaye. Sai ki fada min gudun me nake wai? Toh ba kamani za su yi ba, yarinyar nan na ganta a fito da ita da alama ma mutuwa ta yi, ai na san ina tsayawa za su kamani kashina ya bushe, Ameer ka ci amanar yarinyar nan kuma nima ka ci amanata, yanzu sun rike fuskata ko a wani gurin suka gan ni za su gane ni Amman ke kin raina wayon mutane saboda wannan kika saka na taka mota ina da gudu kamar mun yi sata? Fitar min a mota Malama Wallahi ba zan fita ba sai ka kai ni gidanmu, kuma ba zan yafe maka halin da ka jefa ni ba, kai dai haduwa da kai masifa ne babu alheri sam Kuma rabuwa da ni bala'i ba, ina wayar? Tana can na saki mana har da takardar na bar su a can, ni ba ta raina nake ba, Kuma Wallahi yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali kila ma ta mutu, ni ba ruwana da alakarku amman yanzu ka dauke ni ka saka ni cikin masifa, gashi iyayena talakawa babu ruwansu ka ja min matsala Me aka ce ya samu yarinyar? Ni ina zan sani wai, kaddara ce kawai ta hada ni da kai, gashi ka zame min kaya, Allah kadai ya san iya abun da ka yi ma wannan yarinyar ita ba, bakin mugu Ya taka turki yayo slow down ya faka ya fita ya zafaya ya bude gambun motarta. Fita, ba zaki zauna min a mota kuma ki zage ni ba Ba zan fita nan ba Wallahi ban san abun da zai sake samuna ba, Ameer ka sakawa kanka imani ta tausayi haba, sai ka rika treating mutane kamar su basa da zuciya da jini kamar kai Wannan karon hawaye ne ya zubo mata. Ina kallo kana rubutawa mata cewar fake love kake mata fa, haka ake yi kwanan baya a gabana ka saka iyayenta kuka kuma ka saka tana zuwa nan kana taba ta ashe ma kai ba da gaske kake sonta ba, ina ta mata hannunka mai sanda ta gane amman bata gane ba Gaskiya na fada mata ai, miye laifina a haka? Bayan ka gama cutar da ita, ni Wallahi da ace mahaifiyarka ce sai na maka dan banzan duka, kuma sai na kai kararka gurin police na nuna min wukar da ka yi Ko yanzu ai zaki iya marar kunyar yarinya Marar kunyar yara dai Ta rama tare da kai hannu ta jango gambun motar ta rufe ta bar shi nan tsaye. Shi har mamakin yadda ta iya rashin kunya kuma take iya tsayawa ta fada masa magana son ranta yake. Zagaya ya shiga side din direba yaja motar har suka isa inda yake kyautata zaton unguwarsu ce domin ya ganta a gurin sau biyu kuma ta jadada masa a lokacin da ta kai shi cikin gidansu. Ya faka be ce mata komai ba ita ma bata ce masa ba. Bude motar ta yi ta fita sai da ta yi nisa sannan ta juyo cikin daga murya ta ce. Allah ya isa, mugun kawai, bakin mugu Gudun kar ya biyota da mota ya saka ta cire talkamimta ta ranta a ana kare. Ta gishin gaban motar yake kallonta har ta shige kwanar sannan ya ja motar ya juya kanta yana fadin. Wannan ta fi tunanina, idonta a tsaye suke bata tsoron kowa Yaja motarsa ya fice daga unguwar, sai dai har ya isa gida tunanin halin da Nimra take ciki yake, babu abun da yayi masa dadi kamar rashin tarar da mahaifinsa a gidan da yayi saboda ya san zai masa maganar wukar da aka ce ya dauka dazun. Tunani kala kala ne a ransa na yadda zai yi ya san halin da Nimra take ciki, sai yayi kamar ya kira number data kira shi da ita sai ya ji ba zai iya ba domin ba san wayar a hannun waye take ba. Cam dabara ta fado masa ya kira abokinsa Abdull, Abdull na dauka ya gabatar masa da bukatar ta son sanin inda Nimra take. Ni ban ma san abun da ke faruwa ba ai Na dauka ko Maleek din ne yake dubata ai I don't think so kasan Maleek baya duba mata ai, ko da kuwa yan gidansu ne Dan Allah bincika min lafiyarta da inda aka kwantar da ita yanzu please Hope dai ba wani abun zaka yi ba Wai Abdull kun mai da dan ta'addane ko minene? Abdull yayi dariya ya kashe wayar. Ameer ya jefar da wayar saman gadonsa ya cire rigarsa ya wandon ba tare da tunanin ko gudun kar wani ya shigo dakin nasa ba ya nufi bandakin haihuwar