← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 165

Sashe 155

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

biyu ya dafa shi yana murmushi. You got lucky, babu wanda ya fada min amman a yanzu na fahimci kai ta ce tana so kenan Maleek ya juyo ya kalleshi cikin karfin hali, zai yi magana Ameer ya tari numfashinsa. Please don't say anything, Wallahi ban ga laifinka ba, yarinyar nan ta cancanceka, kuma kai sadaukarwa ka yi da zuciya daya, sai Allah ya saka maka, na san zaka rike amana fiye da ni kuma ina mai tabbatar maka hakan ba zai taba alakarmu ba blood is thicker than water Maleek ya rugume shi yana jin babu dadi, if ba dan neman ya faranta ran Nuwairar ba da shi ma zai iya hakura da ita, domin ba ya jin zai iya samun farinciki ga bakinciki dan'uwansa. Ameer ya sake shi suka yi sallama sannan ya fice. Gidan Hajiya ya nufo a falo ya same ta bayan ya gama yi mata sallama ta sanar masa Humairah tana dakinta fever ya rufeta, cikin sauri ya shiga dakin sai ya same ta kwance a kan gadonta idonta a rufe ta lulluba da blanket. Gefen gadon ya zauna ya kira sunansa sai ta bude idonta a hankali. Me ya same ki? Hawaye ne ya sauko idonta. Ina ta tunanin abun da zan maka na dauke damuwar nan dake tare da kai a yanzu Ameer, gashi gobe zaka tafi zan yi kewarka sosai Yayi murmushi. Ki yi min addu'a kawai kuma tafiya ai zamu yi waya, zamu yi video call ma Ta tashi zaune. Zan je na yi magana da Nuwaira kamin ka dawo maybe ni zata fahimce ni No na rufe babinta a yanzu Humairah, ba mu iya cilasta wasu su so mu, ya kamata mu koyi haka? Ba ma iya juya zuciyar wani garemu Haka ne, da zamu iya da mun juyo da zuciyar wasu izuwa garemu, dole ne mu karbi kaddara Yeah, kuma daman can kin yi min baki idan an rasa mai so na ba zai na dawo ki san yadda zaki yi da ni ba Cikin zolaya yayi mata maganar amman a take ta ji an zare mata duk wani ciwo da take ji, sai ta sauko da kafafuwanta ta sauke idonta kasa tana murmushi. Shi kuma ya mike tsaye yayi mata sallama ya fice daga dakin. A cikin mota ya zauna yayi ta kukansa kamin ya isa gidan Daddy domin duk wani abu da yake yana jurewa ne kawai saboda ya sabawa kansa amman deep down ya san yana cikin damuwa. A dare kasa kwana yayi ya raya dare da nafila yana rokon Allah ya cire masa son Nuwaira a ransa gana daya domin yanzu ya fahimci ba kaddarasa ba ce. Bayan sallah asuba ya samu kwantawa bachi minti talatin ya tashi ya shirya domin jirgi da zai bi da wuri zai tashi. 8 daidai Mommy ta shigo dakin ta dora masa da nata kalar nasihar ta karfafa masa guiwa har ma ta dora da cewar. Ni dai daman can saboda babu damar zaba maka mata ne, amman Daddynka Humairah ya ci burin ka aura, mun tattauna da shi ya nuna min haka tun a baya ma saboda yana ganin kamar zaku dace kuma hakan zai faranta ran Hajiya, ya gyara alakarta da Ummi, sai dai nuna masa kana son Nuwaira a ya saka dole ya aje maganarta a gefe, kuma tun da har ka ga Allah be baka ita ba to ba alheri ba ce a gareka, sai ka gode Allah kuma ka roki Allah ya baka mace ta gari In Shaa Allah Mommy na gode, daman Humairah ce yarinyar da Daddy ya so ya gabatar min a matsayin matar aure? Ita ce Yayi shiru be sake cewa komai ba har ta fice daga daki. Memorial Sloan Kettering Cancer Center United Kingdom. Misalin karfe 10 na dare jirginsu ya sauka a airport, zakuwa da son ganin Ummi ya hana shi sauka a gidan Daddy dake garin, kai tsaye ya dauki taxi zuwa asibiti, daki daki ya bi dokinsu sannan suka ba shi damar shiga dakin da Ummi take. Cikin fargaba da tunanin halin da zai tararda da mahaifiyarsa ga kuma tausayinta da ya cika masa zuciya ya shiga dakin. Slowly ya isa inda gadonta yake. Kusan dakin cike yake da na'urori kala kala na kula da ita, tana kwance a wani kasaitacen gadon asibiti sai bachi take, fatar jikinta ta yi haske sosai kamar ba nata ba, ga bakinta ya canja wani yanayi mai kamar tsufa ya bayyana a fuskarta. Zaunawa yayi a kujerar dake kusa da gadon ya kai hannunsa ya rika hannunta dake sanye da wata karamar na'ura yana kallonta, hawaye ne kawai ke zuba a idonsa kamin ya fashe da kuka marar sauti ya kifa kansa a gadon yana jin kamar ya mutu ya huta. Ummi bata farka ba sai kusan asuba domin ta dade bata samu bachi mai dadi irin na yau ba. Har lokacin kuma Ameer yana tare da ita yana jiran farkawar nata. At first rufe idonta ta yi bayan ta kalleshi a zatonta mafarki take, ta bude ido ganinsa ya saka ta sake rufewa wannan karon kuma sai ta yi tunanin gizo idonta suke mata. Har sai da ta ji hannunsa a fuskarta kamin ya kwanto ya dora kansa a saman kanta. Da sauri ta bude ido ta karkata kan tana kallonsa sai ya kirkiri murmushin karfin hali ya ce. Ssnnu Ummi Ba mafarki nake ba? Zahiri ne, ban Fada miki zan zo ba shiyasa kika ganin kamar bs gaske ba ne Ta gwada yunkurin tashi zaune saman babu kuzari. Ameer how are you I'm fine Ummi ys jikinki Alhamdulillah ina ta ibada kai kadai ka zo Yeah kina son ganin wani ne? Ta yi shiru bata ce masa komai ba, sai kallonsa take irin kallon nan na kauna da take jin kamar ta bude zuciyarta ta saka shi, dayan hannunta ta kai ta taba fuskarsa. Tun yaushe kake nan? Tun jiya, na yi missing dinki ne sosai Ummi ina son ganinki Murmushi ya bayyana a fuskarta. Kullum sai na yi maganar ka, ina yawan fada ma Abiey ya kula min da kai ko bayan raina Ya kwanto ya rungume yana magana kamar rada Ba zaki mutu yanzu ba Ummi sai kin ga yayanmu da jikokina ma Ta yi murmushi. Haka Abiey da Maleek suke fada, nima zan so haka idan Allah ya ara mana time, sai dai ban ga wani kokari da kuke akan haka ba Muna yi Ummi, na ma zo miki da albishir amman ba zan fada ba sai gobe ya kamata ki koma ki kwanta yanzu Na yi bachin enough kuma na farka na ga abun da nake ta muradin gani a kusa da ni da na Tana maganar tana kara rike shi da dayan hannunta... Ban samu enough time na kula da kai yadda ya kamata ba, shiyasa kullum ina tunanin ko a wane hali kake yanzu? Gashi ciwo ya kwantar da ni na fadawa Abiey na fi son mutuwa a gida cikin family na amman ya ki saurarena Haba Ummi kar wannan ya dame ki you have done enough, and yanzu time dina ne da zan iya idan ma kina jin ba ki yi enough ba idan kika samu lafiya sai ki yi Allah ya nufa Fada min albishir din minene? Albishir din da zan miki zan fada miki cewar ina son na yi aure soon very soon Ummi ta kalleshi da sauri da mamaki da kuma jindadi marar misaltuwa. Da gaske Ameer? Da gaske Ummi ai ban taba miki karya ba, kuma ba zan fara a yanzu ba Oh ya Allah na, yaushe wace mai sa'arce haka? Ya shafa kansa yana murmushi. So Ummi kina tunanin idan wata ta same ni a yanzu ita mai sa'arce? Sosai kai fa dan Abiey ne, dan Mr Bashir dan Deen kuma dan mamansa Zahra Still murmushin yake yana tuna makamancin wannan furucin da Humairah ta taba yi masa. Na san surukata ba zata wuce Nuwaira ba No Ummi ba ita ba ce, Nuwaira tana da wanda take so, and idan muna son mutane dole ne mu so farincikinsu Wa take so? Fada kuka yi please don't break her heart I didn't ita ta yi breaking heart dina, ko ba ita ba ba zan sake breaking heart din wasu ba balle kuma ita da take karkashin ikon uwata What happen? Babu kawai dai na fahimci bata ra'ayi kin san shi so wani abu ne da yake gina kansa a zuciyar bawa, tana so zan iya fadar haka domin muna da kyakkyawar fahimta da ita, sai dai ba irin so na aureba kamar yadda ta fada, kuma na fahimce ta na mata uzuri Ummi ta ji wani iri a zuciyarta tausayinta danta ya kamata, sai dai kuma ya san bata isa ta saka Nuwaira son Ameer a dole ba kamar yadda bata isa ta cire wanda ke zuciyarta ba, ko ba a fada mata ba ta san ba zai wuce Maleek ba, domin Ummi ta ga irin kukan da ta sha lokacin da ta san da Maleek za a tafi, and duk gaisawar da zata yi da Ummi idan ta tambaye Ummi yaushe zata dawo sai ta ce Ya Maleek yaushe zaka dawo, shi kansa Maleek din tana lura da irin yadda yanayinsa yake canjawa idan yana video call da ita a gaban Ummi. Ameer dan Allah kar wannan ya saka ka a damuwa, komai nufi ne na Allah kuma so da yawa mukan so abu ya zama ba alheri ba ne a garemu, wani lokacin kuma sai mu ki abu ya zama alheri a garemu Yeah shiyasa na daga mata kafa ai, a yanzu dai ina nan ina ta addu'a Allah ya yaye min duk wani abu da nake ji a zuciyata akan son Nuwaira Ni ma zan taya ka da addu'a, amman kuma a cikin wannan halin kake zancen yin aure wa zaka aura? Ban gama yanke hukunci ba, domin a yanzu bana jin sonta a raina kamar yadda nake jin Nuwaira, bana son na aureta na cutar da ita, wata kila kuma zan iya koya har na fara, ina jin zan iya zama da ita na bata kulawar da ya kamata amman ba zan ji sonta kamar Nuwaira ba, sai dai idan har ta tabbata abun
Chapter 155 · 0% Book details