Sashe 47
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
nema a gurinka lallai dan ya san kana da shi ne, ka fi karfinmu nesa ba kusa ba, amman karka bari sherin shaida da zuciya su rinjaye ka, ka yi hakuri dan Allah... Ta duka har kasa tana bashi hakuri idonta dake cike da hawaye suna kallon fuskarsa, ba shi kadai take gani ba zubun fuskar da tsarin hallitar da tsayin take ganin kamar na anta aya tilo da ya rasu, Kamar har ta so ta yi yayi sai dai wannan ya fi anta manyan ido da kyau da fadin kirji. Baya baya yayi ba tare da yace komai ba ya juya ya fice daga gidan cikin rashin kuzari, yana jin wani abu marar dadi a ransa. Khadeeja Candy Copyright 2023 *W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660* Cikin motarsa ya dawo ya zauna yana ta kallon mutanen dake wucewa, ya duba duba hannunsa daidai saitin inda ta rika wutsiyar hannun ta ja zuwa cikin gidansu. Isowar Nimra ya saka shi sauke gilashin motarsa yayi mata horn, sai ta fito motar Ummi ta nufo inda yake rike da Box din ta saka mask a fuskarta tare da katon bakin gilashi, bude motar ta yi ta shiga ta zauna ta cire mask din da glass. Na karya dokar da Abiey ya saka min, kuma na karya alkawarin da na yi ma Ummi Ya kalleta a lokacin da hankalinsa da kuma tunaninsa suka dawo kanta. Wace doka? Na yi ma Ummi alkawarin ba zan sake haduwa da kai ba, ita ta bukaci haka kuma na yi mata, Abiey kuma yace ko sunanka kar ya sake jin a gurin mu, yanzu kuma na fito ba tare da sanin kowa ba na zo nan Ya taba baki. Just Ta kalleshi. Just ne kawai? Yeah don't tell me this is the first time da kika yi breaking rules din gidanku, yanzu fa an waye ba komai zaka aikata ka bar iyayenka su sani ba like this Ya kwanta jikin kujerar da take ya sumbanci gefen bakinta. You can't tell them same one kissed you Ya rika hannunta ya murza a hankali. And you can't tell them someone hold your hand, akwai abubuwa da yawa ba zamu fadawa iyayeba amman muna aikatawa, an waye yanzu Nimra muna wani zamani ne da muka fi iyayenmu wayo da iya sirranta abu Rawa jikinta yake, ba rawa ta tsoro ko fargaba ba, rawa irin da macen da namiji be taba rika hannunta ba ya fara a yanzu, wani abun take jin mai kamar faduwar gaba tana ji tana gani numfashinta na son sarkewa, so take ya janye hannunta daga rikon da yayi mata domin har yanzu murza mata yatsun yake amman ta kasa. Kiss din da yayi mata ma ta aje shi a wani ma'auni na dabam. Ta kasa kallonsa sai yawo take da idonta a titi. Ga... Ga.. Sarew... War... Ta samu kuzarin mika mishi bayan ta yaki zuciyarta. Be saki hanninta ba sai ya saka dayan hannunsa ya karba yana hadawa da hannunta ya rike, sai kuma ya daga hannunta ya sumbanta. Na gode sosai sarewar tana da muhimmanci a gareni Wannan karon ka ta samu kuzarin fisge duka hannayenta. Wannan be dace ba Ameer haramun be Dariya ya saka mata yana mata kallon mamaki. Karki ce min baki taba yin saurayi ba, or baki taba rike hannun namiji ba ko kissed even slept with him? Subhanallahi Wallahi ban taba ko daya ba, ban taba saurayi ba balle har na kai ga aikata abun da kake tunani So you're still Virgin? Ta dauke idonta tana kallon wani gurin. You miss alot, babbar yarinya kamar ke? Baki da kawaye ne? Ina kika yi rayuwa? Ta bude motar. Ya kamata na tafi kar wani ya dawo be same ni a gidan ba Hannunsa ya mika ya juyo fuskarta ya matso da ta shi yana kallon bakinta sai ta juya ya sake juyawa da ita wannan karon gaf da ita yake, har tana shakar numfashinsa. Taya zan yarda baki taba kissed wani namiji ba? Saboda ban taba yi ba, kuma ba zan yi karya ba Can you swear? Wallahi ban taba yi ba Ameer Idan kuma kin taba yi kika min karya Allah ya halakaki kamin ki isa gida kin yarda? Na yarda Tana rufe baki ya saka bakinsa cikin nata, abun ka da wanda be saba ba sai ta kasa komai har ya gama yawo da halshensa a bakinta ya cire, a nan kam tsoro ya bayyana a idonta sosai kamar yadda ya bayyana a jikinta take rawa har yana iya gani, wannan kadai ya isa ya yarda cewar bata taba tarayya da wani ba. Ki aje mana wannan sirrin, saka min number wayarki zan kira ki anjima amman zaki min wani alkawari a duk lokacin da na bukaci ganinki zan ganki? Ya dauko wayarsa ya mika mata, ta karba ta saka mashi number, sannan ta juya zata sauka ya sake riko hannunta. Baki min alkawari ba Zan duba Ba zan ce dubawa ba ne, zance ake na rayuwata i can not breathe when you're not near idan kuma kin fison na rika zuwa gidan ku kai tsaye then fine zan dauki ko wane risk just to see you Nimra... Kallonsa take, da gaske so take ta gane idan kalaman da suke fitowa a bakinsa har a zuciyarsa suke, miyasa zai sauya mata a iya yau kadai? Ya sumbace ya fada nata ba zai iya numfashi idan bata kusa ba, ya rika hannunta kuma yayi mata godiya da kawo masa sarewar da ta yi. Ganin irin kallon da take masa ya saka shi cewa. Na san fada muke, amman dukan abun da kika ba ni na karba na karba ne saboda na yarda dake, and now na bukaci ganinki kawai ba dan ina son sarewar ba, na san hakan kadai zan miki ki yarda mu hadu, zuciyata taan samawa kanta abun da take so ne Nimra ba tare da duba matsayi ko gaba ba Mutumen da ke ta rigima da ita ya ki yarda ba da hadin bakinta aka shirya masa komai ba, mutumen da girma kai kadai ya isa ya hana shi yin godiya a gareta. Da gaske abun da yake fada haka ne har zuciyarsa? Ta janye hannunta ta sauka a motar. Zamu rika haduwa wani gurin ba gidan mu ba Okay take care of yourself Ta juyo ta kalleshi sai yayi mata murmushi, wata kalmar bata sake fitowa bakinta ya nufi motar da ta zo da ita ta bude ta shiga. Har ta yi ma motar key ta hau titi be bar gurin ba kuma be fasa kallonta ba har sai da ya daina hangota. Tana tukin tana tunanin yadda zuciyarsa ta karaya da wuri haka, ya yarda da ita kenan? Ta kai hannu ta taba bakinta amaimakon ta ji haushin abun da yayi mata domin bata taba aikatawa sai ta yi murmushi tana jin wani irin kimarsa na karuwa a idonta. Is this the sight of love? Ta tambaye kanta, domin wani irin yanayi take ji na dabam tun farkon haduwarta da shi har zuwa yau da wani abun ya shiga tsakaninsu? So ne ya saka take ganin abun da ba daidai ba a daidai har take iya karya dokar gidansu data mahaifinta? Take iya kyale wanda ba muharraminta ba ya rika hannunta har ya sumbance ta? Wata kila shi ma son ne ya saka shi saurin yarda da ita, daman ance wanda be taba yi ba idan ya fara masa baya masa da sauki. Kamar wanda aka yi ma albishir da yafiya haka Nimra ta wuni da farinciki da annashuwa a ranta ba ma kamar lokacin da ya kirata yana ta kashe ta da kalamai duk kuwa da be furta mata cewar yana sonta ba, gaba daya sai ta manta da wata damuwa ta tattara rayuwarta da duk wani tunani nata ta maida a gurin Ameer cikin wuni daya ta canja kamar ba ita ba. Tunanin yadda zata yi da iyayenta idan ta kulla alakar soyayya da Ameer sam be zo mata a rai ba a lokacin saboda farinciki ya dauke mata hankali. AMEER POV. Yana isa gida wanka ne abun da ya fara yi, ya wanke sarewar tas sannan ya zo gaban madubi yana kallon yadda Allah ya tsara halittarsa da mazantaka aka jera masa six pack kamar shi yayi kansa. Yaushe na yi arha haka, i kiss Nimra i hold her hands Shi kansa ba zai iya fadan yadda kyamarsa ta boye kanta har ya iya Sumbanta Nimra kai tsaye ba, duk kuwa da yanayinta da jikinta be nuna bata kula da kanta ba and the most abun da ya ja hankalinsa fada masa cewar bata taba yin kiss ba, ya kuma yarda domin ya lura da yanayinta macen da bata taba kebewa da namiji ba tana da banbanci da wacce ta saba yi ko ta taba, ita ce mace ta biyu da yawun bakinsa ya taba kaiwa a bakin wata bayan Angel, ita ma kuma Angel ribantarsa ta yi da tsabtarta da kuma aske gashin kanta da tayi kamar yadda ya bukata bayan ta daukar masa alkawarin tsare kanta, shi kuma shaidan ya rinjaye shi har ya saka rike kansa, a duk lokacin da bukatar hakan ga taso masa baya cilastawa kansa hakura da abun da yake ganin yana da iko da halin yinsa akan me zai cutar da kansa then? Ya tsuke baki, tunanin daukar fansa da son lalata rayuwar kanwar makiyinsa ya mantar da shi wani abu kyama, wata kila kuma ita din bata da kazanta shiyasa be ji hakan a lokacin da yayi unkurin karya tarbiyar da iyayenta suka bata. And this fitinanniyar yarinyar ta ja hannunsa har cikin kazamin gidansu be mata komai ba. Ya tuna irin kalaman da kakarta ta yi masa cewar ita marainiya ce kuma ta dogara da abun da take samu a gurin aikin ne. Ya dan tabe baki zai kyale ta ne kawai saboda Kakarta da ta durkusa har kasa tana rokonsa ba dan haka ba sai ya koreta saboda ta masa tsiwa shi kuma baya son haka ya lura tana da zafin zuciya kamar shi. Tawul ya nufa ya dauka ya daura ya fada kan gado ya ya dauki wayarsa