Sashe 89
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
yace tsintacciyar mage bata mage, da na san wannan ranar zata zo da ban karbi wannan kyautar da Zahra ta yi min ba tun farko Cikin yanayi mai ban tausayi Mommy take kallon jagoranta nata idon na kwarar da kwalla ta ce. Ka yi hakuri, haka Allah yake ikonsa idan ya zo, da ace ya so da dauke Ameer zai yi gaba daya ya mutu, ba ku san abun da zai faru gaba ba, dan Allah ku bar jayayyarsa, masu iya magana sukan ce ba a jayyyar a da miji, idan aka yi jayayyarsu tafi suke su bar masu jayayyar Mommy bata taba sanin cewar ba shi ya haifi Ameer ba sai a yanzu da komai ya lalace. shakuwarsu da yadda kaunar Ameer take a zuciyar mijinta take tunawa sai tausayinsa ya kamata. Tun da ya aureta be taba zancen mahaifiyar Ameer da ita ba idan ma ta dauko masa sai yace mata baya son maganar a dole take kawar da zancen domin ita macece mai matukar son farincikin mijinta yana aya daga cikin dalilin da ya saka take nunawa Ameer kauna, domin ta lura yana matukar kaunar Ameer ya kuma tabbatar mata da hakan tun kamin ya aureta. Baka taba kuskuren aikata wani abu da zai nuna Ameer ba anka ba ne, ko da wasa baka son bacin ran Ameer, Wallahi a rayuwata ban ga wani uba da ya nunawa ansa gata fiye da yadda ka nunawa Ameer ba, lallai duniya zata girgiza idan labarin nan ya fita Tana fada tana kuka, ita ma tausayin Ameer din take jin cewar be sani ba sai a yanzu, kara ma Daddy ya san da sirri amman ya boye saboda farinciki ansa, amman Ameer fa? Dare daya da wuni aka ruguza masa komai. Wata kila da Jamila bata aikata abun da ta aikata tun farko ba, da ba mu jefa yaron nan da kanmu a matsala kamar haka ba, ina tsoron kar ya shiga wani hali Jamila ai dole ta fada masa gaskiya, saboda ta bata alakarku, na yi imani ba zata tado maganar kai tsaye ta fada ba, amman idan har ya bukata zata fada masa domin tana kallonka a matsayin wani wanda ya samu farinciki da kyautar a silarta amman ya kasa zama da ita, ya ki yarda ta bawa wannan yaron kulawa a karkashinsa, kai ma baka yi mata adalci ba, domin saboda kai ta aikata haka sai gashi kuma ka rabu da ita.... Mommy na aje ayar zancen Daddy ya rufe da fada, domin ji yake a yanzu ba shi makiyiya a rayuwarsa kamar Zahra da Jamila, ba ma kamar Jamilar da ita ce silar komai. Toh zama zan yi da ita? Bayan ta yaudare ni? Ta jefa a matsala ta aikata kuskure da addinin musulunci ma be yarda da shi ba, sannan yanzu ki kalli idona ki ce wai na kyale ta? Haukace ne ni da zan zauna da ita? Ko kuma neman haihuwa hauka ne? An isa ayi ma Allah wayo ne? Yanzu da ya tashi ba ni yayan ba ya ba ni ba? Taya za zauna da macen da bata da tawallaki da imani a zuciyarta? Idan har zata iya aikata hakan me kike tunanin gaba? Da ace ban gane gaskiya ba haka zamu yi ta zama ina kallonta a matar kirki? Ashe ke ma dai baki da hankali, ina ganinki mai ilmin ashe na banza ne Allah ya huci zuciyarka, ban ce ka zauna da ita ba, kawai ina fadar abun da na fahimta ne Fahimtar banza fahimtar wofi, mai daki ai shi ya san inda yake masa yoyo, karki fada min maganar banza, ina neman abun da zai zame min mafita ni da ana sai kuma ki fara fada min wata maganar banza akan Jamila Malama tashi ki fice daga daki Ka yi hakuri dan Allah... Ki tashi ki fice na ce Ta mike tsaye cike da nadamar maganar da ta yi ta fice daga dakin ta bar shi sai huci yake, abun da ba halinsa ba domin mawuyacin abu ne ta ga bacin rai a fuskarsa idan ma ransa ya bace yakan yi kokarin boye abun ya barshi a ransa. AMEER POV. Ji yake kamar shi kadai ya rage a duniyar nan he's feeling so lonely. Wani irin tarin bakinciki da damuwa ne a cikin ransa, ya dade a cikin motar kwance idonsa a rufe sannan ya bude motar ya fito ya shiga ciki, sai da ya fara bude fridge ya dauki gorar ruwa ya sha sannan ya dawo falonsa ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Be yi bachi ba kuma be tashi daga falon ba har kusan 11pm, tunani yake wani abun yana zuwa masa baibaiwa wani a daidai, wani tunanin kuma idan ya fadada sai ya ji kamar ya fashe da kuka. Sha daya na dare da yan mintuna kiran Abdull ya shigo wayarsa, yana ganin sunan mai kiran gabansa ya fadi zuciyarsa ta raya masa cewar Maleek ya labarta abokansa abun da yake faruwa shiyasa Abdull ya kira shi by this time. Amsa kiran yayi ya saka wayar a speaker yana tunanin kalar amsar da zai bawa Abdull idan ya tambaye shi. Hello Ameer ya fada cikin rashin kuzari murya can kasa. Kai tsaye Abdull ya fada masa dalilin kiran. Ameer ka ji kanwar Maleek ta rasu Jin an fada masa abun da ya sha gaba komai wato mutuwa ya saka shi zabura ya gyara zama da sauri. W-w-w what? Wace wace wace please wace? Nimra, ta rasu da daren nan asibiti Ameer ya aje wayar akan center table dake kusa da shi ya dora hannunsa saman kai ya gurfana a kasa kamar mai neman gafara. Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Allah ya Abdull how? Why? Why? Mutuwa ai bata da magani, ba kai ka fada min an kaita asibiti ba? Maybe ciwon be barta ba Ya girgiza kai ya rufe bakinsa yana kuka. Na kasheta Abdull ni ne... Ni ne silar mutuwarta.. Na rabata da duniya... Oh my God yanzu ya zan yi da hakkinta? Ameer lafiya kake kasan me kake fada? I break her heart, na yi ne kawai saboda na bakantawa Maleek, and ba son gaskiya nake mata ba, kuma na fada mata and.... Shi ne silar sumanta har aka kaita asibiti now you're telling me ta mutu, Me yasa abubuwan nan za su zo min a yanzu Abdull I'm such bad person i didn't deserve anything good at all, ina zan roki yafiyarta? Yanzu ya zan yi da hakkinta Dauke wuta Abdull domin shi dai ya kira ne kawai ya sanar masa kamar yadda abokinsu Dawood ya sanar musu so that su taru su tafi gurin abokinsu domin jajanta masa kuma ayi komai da su, kamar yadda suna gudanar da al'amurransu a can da, duk kuwa da kasancewar babu wanda ya taba rasa rai a cikinsu sai a yanzu da Maleek ya rasa, sai dai duk abun da ya samu suna taruwa su jajanta ma juna, ba dan ma matsalar da Ameer ya samu da Maleek ba da a kullum tare suke rayuwa. Ameer... Kasan me kake fada kuwa? Amman Ameer ya sani? All this fadan da kuka yi har abun ya kai su gurin police iyaye suka shiga abun be tsaya iya nan sai da zuciyarka ta raya maka ka aikata ma yarinyar nan wani abu? Yanzu miye amfanin aikatawar da ka yi? Gashi ka zama silar mutuwarta, innocent live, da ma ace kana sonta da gaske sai abun ya zo da sauki amman kasan baka sonta ka aikata hakan saboda kawai ka cutar da ita? Kana da matsalar rayuwa Ameer, idan ka dauki gaba da mutum kai ala dole sai ka ga bayansa, burinka ka wulakanta kowa cikin har da mu da muke abokanka, kuma babu wanda zai fada maka ta ji wannan ba rayuwa ba ce mun sha nuna maka amman baka ji ba, yanzu kana tunanin hakkin yarinyar nan zai barka? Idan iyayenta suka yi kararka ma za a iya kwatar musu hakkin yarsu, bayan haka kuma ka karawa kanka kiyayyar kanka a gurin Maleek da iyayensa.. Sannan.... Yanke wayar yayi fahimtar Abdull ba zai gaba zuba masa kalaman da suke kona masa rai ba. Nimra... Ya furta yana hawaye, wayarsa ta sake ringing wannan karon Dawoo ne ya kira shi, wata kila shi ma zai sanar masa an yi mutuwar ne, sai ya ki daga wayar sai hawaye kawai yake, wani rauni da nadama suka mamayeshi. Sai a yanzu yake ganin be kyauta ba, be aikata daidai ba, be dace yayi haka ba, me yasa ya cutar da Nimra? Son zuciya ne ya kai shi ga aikata hakan ko kuma rauninta? Wa gari ya waya yanzu? Gashi Ummi ta fada masa kanwarsa ce, that's mean Ummi ta haife ta kenan? If wani ya aikata wa kanwarsa haka ya zai ji balle kuma ace shi da kanss ya aikata? Ya mike tsaye ya fara safa da marwa a falon, dariyarta ce ta fara fado masa a rai yana tuna yadda take nishadi idan ta zo gidan, saboda tana tunanin son gaskiya ya nuna mata, yadda ta rike hannunsa tana rokon ya rike ta amana ya tsaya mata a duk lokacin da za su tsinci kansu a cikin mawuyacin hali, yadda take yawan fada masa tana kaunarsa ga kuma irin marin da Abiey yayi mata a lokacin da suka zo daukarta restaurant ya tsaya masa a rai, kiran da ta yi masa a waya na karshe har ya fada mata cewar shi baya kaunarta ya hana shi sukuni. Sai da ya kai tsakiyar falon ya fadi durkushe ya fashe da wani irin kuka mai taba zuciya, sosai yake kukan da ace gidan ba babban gida ba ne da makota ma za su iya jiyo muryarsa. Nimra ki yafe min.... Ki yafe min Nimra.... Na shiga uku, i hurt this innocent girl, i hurt her hakkinki ba zai bar ni ba, me yasa na aikata? Akan me zan dauki dansa akanta? Meyasa na zama wawa? Why ido zai rufe na kasa ganin abun da zai biyo baya? Fada yake da kansa kamin ya daga hannunsa ya dauke fuskarsa mari, ya daga hannayensa ya buga kasa, be taba jin ya cutar da wani cutar da ta kai makura ba irin wannan, sam be dorawa Nimra mutuwa