Sashe 38
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
shiga ciki, domin akwai masu gadi da yawa a gidan Shikenan ya sha banza kenan? To ya zaki yi Toh Allah ya isana, Allah ya hana shi farinciki duniya da lahira, yadda ya ci amanar marainiyar Allah ka saka shi cikin damuwa Direba dai sai dariya yake, ya san Ameer be kyauta ba, sai dai lamarin Humairah ne abun dariya domin bata barin ta kwana sai gashi kuma an kai inda ba zata iya ramawa ba. Har ta bude motar ta fita bata daina masa Allah ya isa ba da bakar addu'a, sai da ta yi tafi mai nisa sannan ta shiga isa gidansu dake cikin kwana, irin gidan nan ne da ake na yawa a bada haya wanda saka zamu falo da daki biyu lo daya sai toilet a cikin dakin, gurin girki kuma sai an fito wajen, yawancin gidajen duk kabilu ne ke hayarsu da kuma masu sana'a a garin abuja kamar masu siyar da nama ko wasu aikin da suke tare da iyalinsu. Ta shiga gate din ta nufi kofar dakinsu ta buga Kakarta ta taso ta bude mata, sai ta shiga ciki ta rufo kofar, sai da kanenta suka tashi zaune suna kallonta tausayinsu ya kamata domin kullum ita take zuwa musu da abincin sai sun ci sannan su kwanta yau kuma bata riko komai ba sai hawayenta da ta kusan kararwa. Lafiya kike Humairah Ta zauna saman kujerar roba dake dakin tana jin wani sabon kuka na sallamo mata. Mutumen da na fada muku cewar ya wulakanta ni saboda na je neman abu a kamfaninsu, shi ya watsa min ruwan zafi na tea a yau kuma ya mareni Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un Maihaifiyarta ta furta tana tasowa ta fito daga cikin dakin da take zaune tana sakar zaren olu. Cikin kuka ta fada musu abun da Ameer yayi mata. Hawaye ya fara saukowa a idon Ummanta. Allah ya isar miki Humaira Allah ya saka miki Kakarta ta amsa sannan ta dora mata da dogon sharhi. Ameen duk mai nema daman dole yayi hakuri, kuma wata rana sai labari dole sai kin jure, kuma tun da kin ga halinsa sai ki yi taka tsantsan, kin san da aikin nan kika dogara muma kuma da shi muka dora sai dan baran da nake ina samu, dole mu yi hakuri kamin Allah ya kawo mana mafita, idan Allah ya sa kika gama karatunki kika samu aiki ai mun warke, amman kamin ki kao ga wannan dole mu hakura da halin da muke ciki, mai hakuri mawadaci ne wata rana, kin ga wannan saurin fushin naki da daukar zafi, ga nacewa ki ce sai kin rama idan aka yi miki abu ki tattara shi ki aje a gefe, ki rika hakuri da rayuwa, idan ba haka ba fitina zaki janyo mana, Humaira ke marainiya ce karki manta da wannan baki gata sai na Allah Ai wanda yake da gatan Allah shi ya fi kowa gata, Wallahi ni sai Allah ya isar min, ba zan yafe masa ko kabarinsa na balbala da wuta Ta tashi ta shige dakin da suke kwana ita da kanenta. AMEER POV. A lokacin da ya fito daga cikin zuwa yayi ya tsaya jikin motarsa not knowing what to do, har lokacin ransa a bace yake, a gurin Abdull ya same shi shi ma fuska babu annuri yake kallon abokinsa da mamakin yadda yake da zafin zuciya da daukar komai da girma. Wani lokacin ina mamakin yadda Allah ya halicce ka Ameer, wannan halinka sam ba shi da kyau, yanzu me yarinyar nan ta yi maka da zaka mareta ka watsa mata tea mai zafi a fuska? Idan wani abun ya same ta fa? Ba damuwata ba ce, kai baka ji abun da take fada min ba? Ni tsararta neda zata kalleni ta fada min maganar banza? Amman kai ka shiga sha'aninta ai, kuma a yadda na fahimta daman akwai wata daba a tsakaninku, sai dai yadda ka yi mata be dace ba, arziki ba hauka ba ne Ameer muma duk muna da arzikin nan amman miyasa ba ma yin abun da kake yi? Miyasa ka fita dabam a cikin mu? Na kira nan ne saboda mu tattauna akan rayuwar da kuma abun da ya faru tsakaninka da Maleek amman ji abun da ka yi causing? Kasan idan yarinyar nan ta yi maka addu'a sai ta kama ka? Sahoda abun da ka yi mata zalinci ne Yanzu ma ni ne mai laifi kenan? Kullum burinka a bawa wani rashin gaskiya a baka gaskiya, ko da kuwa baka da ita, wannan ba hali na gari ba ne ka canja Ameer Yana kaiwa nan ya kara gaba gurin motarsa ya bar Ameer din a tsaye yana binsa da kallo. Ya kusan minti talatin a gurin tsaye sannan ya bude motarsa ya shiga ya dauki hanyar gidansu. Sakon kar ta kwana ne ya shigo wayarsa da number Angel daga bisani kira ya fara shigowa, be kula sakon ba balle kuma wayar da idan zata shekara tana ringing ba zai daga ba. Ya faka motar a harabar gidansu yana tunanin abubuwan da Abdull ya fada masa, so yake ya gane idan da gaske abubuwan da yake bana kwarai ba ne, amman ya kasa ganin haka har yanzu ganin yake ita ta yi masa ba daidai ba, but still ya dan ji babu dadi na watsa mata ruwan da yayi domin zai iya illata fuskarta but ai ita ta janyo ma kanta. Ta shiga falon yana lumshe ido saboda kamshin turaren wutar da Momy ta turare falonta da shi, yana dalilin ne ya saka yake kaunar matar uban tasa ban da wannan babu wani dalili domin kullum ganinta yake kamar tana nuna masa kiyayya kuma tana tsanarsa saboda ba ita ta haife shi ba. Wanka ne first abun da ya fara yi sannan ya sauko kasa ya ci abinci, then ya koma sama ya bude windows din dakinsa ya tsaya a gurin yana kallon backyard din da Allah ya wadata musu da itacen kayan marmari wani iska mai dadi na kadawa. Ko tana ina yanzu? Ya tambayi kansa tambayar da bashi da amsarta kuma be san wanda zai amsa masa ba, ta rayu ko ta mutu ma? Ya za'ayi a gane yan'uwanta wannan ma ya san wani sabon aiki ne, samun kansa yayi da murmushi tuna yadda ta dauke macijin ta rike a hannu ko shi da yake namiji ba ya rikon maciji balle kuma ita da take mace, he thought macijin ba zai iya mata komai ba amman ji yadda ya cijeta har ta suma. Can kuma ya yamutsa fuska tuna yadda take da kazanta a jiki ga wasu bera a hannunta, shi da yake jin ba zai iya rayuwa a gurin da bera yake rayuwa ba ma balle har ya taba shi amman ji ita har rikonsa take. Allah kadai ya san garin wannan yarinyar ta fito Wannan karon a fili yayi maganar ya zuba hannayesa aljihu yana kallon sararin dake dayan gefen. ABIEY'S HOME. Mamaki ne sosai a fuskar Nimra miyasa Ameer zai yi requesting na following dinta? Why? Is he the one ma? Bayan duk abun da ya faru? What now wani abun zai fada mata ko kuma hakuri zai bata? Or maybe ya yarda cewar ba da hadin bakinta aka shirya masa komai ba? Shi din ma ne na gaskiya. Ta shiga account dinsa ta duba da kyau bata gani abu dake nuna fake account ba. Tunani kala kala a ranta at the end ta yanke shawarar karba masa zuciyarta na bugawa da mugun karfe, wani irin yanayi take samun kanta a ciki a duk lokacin data tunkari wani abu daya shafe Ameer, har yanzu ta kasa ganin laifinta kuma ta kasa mantawa ko cireshi a ranta, kamar yadda tausayinsa yake cika mata zuciya bayan kuma ta fishi zama bar tausayi a yanzu domin mahaifinta baya magana da ita saboda abin da ta aikata. Tashi ta yi zaune daga kan kujerar da take kwance ta kalli Mahmood daya shigo falon Maleek na bayansa sannan Abiey dake sanye da manyan kaya idonsa da garin gilashi hular da ya dora a kansa ta zauna das ta masa kyau irin kyaun nan na magidanta masu iyali da hurhura ta fara fitowa ta yi musu ido. Sannu da zuwa Abiey Ta fada cikin girmamawa da fargabar amsawarsa, ko inda take be kalla ba, ya kalli Mahmood ya ce. Je ka kira Umminku, kai kuma ka ce su shigo da ita Ya karasa yana kallon Maleek dake wasa da key motar dake hannunsa, Mahmood ya nufi Upstairs dakin Maleek kuma ya juya ya fice daga falon. Da kuzari Mahmood ya tura kofar falon ya dakin ya shiga. Ummi Abiey... Ya kara karasa maganar saboda ganin hawaye sharkab a fuskar mahaifiyarsa, sai ta yi wuff ta sauke kai kasa ta kawar da fuskarta daga kallon madubin, ta boye gashin dake hannunta. Jiki babu kuzari ya karasa kusa da ita ya risina har kasa yana kallon fuskarta a nan ta kasa boye hawayenta, ya mika hannunsa ya kama hannunta ya cire gashinta dake ciki ya kalla sannan ya mika hannunsa ya kai gurin kanta ya riko gashinta sai ga gashin ya biyo hannunsa, take na shi idon suka cika da hawaye hankalinsa yayi mugun tashi irin tashin da be taba yi ba, zuciyarsa ta hau bugawa da mugun karfi har fitar numfashinsa ya sauya. Ummi mi ke faruwa? Ta dauki dankwalinta ta saka sannan ta saka hannu ta karbi hashinta da yake hannunsa. Wannan a tsakanin uwa da anta ne kawai, bana son mahaifinka ko Nimra Maleek da Namra su ji, ka bar wannan daga ni sai kai sai Allah ka ji ko? Binta yake da kallo gaba daya jikinsa yayi la'asar ya kasa gane komai, tana daf da shiga bandaki ya zaburi muryarsa ya ce. Ummi zamu je asibiti ko? Ya kamata mu ga kwararen likita Zamu yi magana daga baya Ita ce amsar data bashi sannan ta shiga bathroom din, tana kallon kanta a jikin madubi sai ta fashe da kuka Mahmood ya dawo gurin kofar ya tsaya gaba daya ya rasa natsuwarsa, tunani kala kala suke zo m asa, wanke fuskarta ta yi ta fito. Me Abiey ya ce? Yace na kira ki an zo da yarinyar suna kasa Magana yake