Sashe 128
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
can zata fita, ta windows Ya kalli Windows din dake rufe ya kalli gadon ya sake kallon Waira. You're scared me please, idonki na jini and now kina fada min wata a gadona zata ta windows you're acting weird Ta sauke kanta kasa. Ni na san na ga mace, kuma ina ganinta a duk lokacin da zan shigo dakin nan And kin ce ina taba ki when? Kullum tun a wani dare da ka rakani dakina, ka fita sai ka sake dawowa ka taba ni, daga lokacin kusan kullum sai ka yi min haka Nooo ba ni ba ne, maybe dai mafarki kika yi Ban yi mafarki ba, na ga hakan a zahiri ba bachi ba, idan ma ina bachi tashina kake yi har sai ka gama tukuna nake iya bachi, wannan ya saka bana kwantawa wani lokacin har sai ka gama Ganin ta gaske take fada ya saka shi mamaki, sai dai mamaki irin na wanda ke lafiya wata lalurar rashin lafiyar kwakwalwa ta same shi, domin a yanzu be kallon Waira a matsayin mai hankali. Ba ni ba ne, ni ban taba yi ma kowa haka ba, kwalkwalwarki ke nuna miki haka, can you tell me why kike zubar da jini a idonki? Ta sake kai hannu ta taba jinin. Hakan na nufin faruwar wani abu, a gareni ko ga wani masoyina wani abu da zai min ciwo Kamar ya? Ya Maleek ni ina da banbanci da kai, ina ya ji abubuwa da yawa da zaka iya ji ba, zan iya ganin abubuwa da yawa da ba zaka iya gani ba, wata kila shiyasa nake ganin mace a duk lokacin da na shigo dakin nan alhalin kai mai dakin baka ganinta Haka ne, wata kila shiyasa kike ganin wani mai kama da ni yana shiga dakinki yana taba ki, saboda ya bata ni a idonki, maybe fuska ya saka mai kalar tawa ko kuma Ko kuma kai din ne... Kin ce kina iya gane abubuwa me yasa baki gane waye shi ba? Saboda ban taba rumgumarsa ba, sai na rumgume mutum ne nake iya ganewa Toh ki gwada yau mana, kina tsafi ne Waira Ta girgiza kai a daidai lokacin da hawayen jinin ya daina zubo mata. Ba tare da tace masa komai ba ta juya. Dole ne sai kin tafi? Indai saboda ni ne ki zauna mana, ba zan sake yin wani abu da zai saka Ummi ta yi fushi da ke ba Ba saboda kai zan tafi ba, zan tafi ne saboda lokacin tafiyar yayi, wata kila lokacin mutuwar ne yayi, daman na fada muku, wata rana za amin sako, ashe ba sako za a min ba ni zan tafi da kaina Ta bashi amsa ba tare da ta juyo ba sannan ta bude kofar dakin ta fita, ido hudu suka yi ita da Ameer, ya fito dakinta ita kuma ta fito dakin Maleek. Ya kalleta sama da kasa zuciyarsa na suya kamar yayi mata magana sai kuma ya dauke kai ya karaso inda take ya wuce ya sauka kasa. Ita kuma ta bishi da kallo sannan ta sake nufar kofar dakin Ummi ta murda kofar ta tura ta shiga. Daga bakin kofa ta tsaya tana kallon Ummi dake zaune gaban madubi tana hawaye, ta cikin madubin take kallon Ummi, Ummi ma take kallonta kamin ta kai hannu ta dauki tissue ta goge hawayen idonta ta juyo ta kalli Waira saboda jinin da ta hango a fuskarta da saman rigarta. Me ya same ki? Me ya faru? Ina kika samu jini? Waira ta kalli rigarta sannan ta kalli Ummi. Ummi me yasa kike kuka? Fara fada min dalilin jinin da na gani a jikinki, kina tsorata ni a yanzu Waira Hawayene, daga ni ne hakan na nufin faruwar wani abu a gareni ne marar dadi, tun a lokacin da aka sakamin tsafi ina jin irin wannan sako ne Idon Ummi ya sake cika da hawaye, ta kai hannu ta cire dankwalin dake kanta, Waira ta yi arba da gashin kanta da babu komai a kai sai kwalluwar kai. Lokaci yana ta tafiya Waira, shekaru na ta raguwa, ko da ciwo ko babu na sani zan iya mutuwa, amman ciwo na tunatarwa ce a gareni na mutuwa, na kusan cinye lokaci bukatu kuma sun ki biya, burika sun yi wuyar cika, kullum da kyakkyawa niyar nake aikata komai, amman daga karshe sai na karbi mummunan sakamako, kalli abun da na aikatawa Ameer daga karshe kaina na cutar, ke ma na rike ki da zuciya daya, gashi sanadinki kan yayana zai tarwatse, burin da nake da shi yana da wahala ya iya cika, kin saka min tsoronki a zuciya zaman dardar nake dake ba kamar da ba, zaman a gidan daga karshe ya haifar min matsalar da ba zan iya magancewa ba Waira ta zube kasan guiwoyinta. Mai baki tsoro ta shigo ta yi miki bankwana ne, wanda kike ganin kamar burinki ba zai cika ba idan tana kusa, zata tafi tafiyar da babu dawowa, lokaci yayi da zan koma cikin dangina na karbi hukuncin abun da ban aikata ba, da kuma wanda na aikata na guduwa na bar garinmu bayan dokokin da aka gindaya min, zan tafi Ummi hankalinki ba zai sake tashi saboda ni ba, yayanki ba za su sake fada saboda Waira ba, kuma ni ba zan taba cutar da ke ba, kin rike ni kamar yarki, kin nuna min soyayya da kauna, kin wayar da ni kin bude min ido daga duk wani jindadi na gode, sosai na kwadaitu da addininku kuma na so ace na yi rayuwa a cikinku, sai dai ban samu wannan lamanin ba, ba zan taba iya bari a cutar da ke ba, ina kaunarki Ummi, ke kika nuna min dadin uwa, a jikinka da siffarki da kalamanki, kulawarki da kaunarki ta sanar min da abun da ake nufi da uwa, ni ban taba sanin uwa ba, sai dai na zo gurinki, ban taba rabar jikin wata ta kaunace ba sai ke, kuma duk bayan wannan sai na saka miki da cutarwa? Sai na zama sanadin zubar hawayenki na zama silar damuwarki? Ta mike tsaye tana kuka, Ummi ma kukan take tana jin kamar tace mata kar ta tafi sai dai ta san tafiyarta zai fi zamanta a gidan alheri, idan ma ta roke ta ta zauna gidan Ameer ya aureta Maleek zai yi ta kallonta da ciwon zuciya ne Waira ta fice daga dakin ta nufo dakinta, ga mamakinta sai ta samu Ameer a tsaye yana jiran shigowarta. Tana kallonsa sai ya sauke idonsa kasa kamar mai tsoronta, murya can kasa kasa ya ce Na kasa natsuwa da jinin da na gani a idonki, ciwo kika ji? Ko kuma wani abun ne? Bata amsa masa ta taka daga bakin kofar da take tsaye ta isa inda yake tana kallonsa. Ameer ka cire ni a zuciyarka, ka manta da an taba halittar wata mace kamar ni a duniyarka, ka goge duk wani hoto rayuwata da idonka suka dauka, ka karya alkalamin dake zana maka shirme akaina, ka yage littafin layin kaddarar dabam tawa dabam, babu ta inda muka dace da juna, ko da ma mun dace aure ba zai taba wanzuwa a tsakaninmu ba It's because of abun da Maleek ya fada miki? Aa saboda ciwon da kake sakawa Ummi, da kuma gabar da kake yi da dan'uwanka saboda ni, sanadinka Ummi ta canja min, ta zubar da hawaye a kaina, kuma take tsorona, idan ka shiga rayuwar mutum lalata kake yi Ameer Kamar ba shi ba, haka ta risina kasa yana kallonta. Zan canja Waira zan zama duk yadda kike son na zama, karki duba yadda soyayya ta maida wani sakare a gabanki ki yi amfani da wannan ki cutar da ni, ban taba so ba sai kanki saboda haka ban san zafinsa da haukarsa sai a yanzu, ban san haka yake maida mutum ba sai a yanzu Yanzu kana iya jin yadda Nimra ta ji? Ya mike tsaye. Sunanta kawai idan kika kira, ji nake kamar hukunta ni kike yi, karki duba abun da na yi dan Allah Waira, abun da ya wuce mu bar shi a wuce Shiyasa zan bar maka gidan, ba zaka sake ganina ba, and it means forever Ba sai kin tafi ba, zan iya bar miki gidan na yi nisa da inda zaki gan ni, amman please ki zauna a nan din, karki tafi saboda ni, idan baki so ne ba laifi ba ne, zaki iya auren Maleek, ki musulunta ta hannuna ko da wannan sai na karu Ya kauce daga gabanta ya fice daga dakin yana jin zuciyarsa kamar zata rabe biyu, be taba jinsa a irin wannan yanayi ba, sai a yau shi kam da ma zai mutu ya hutu, yaushe soyayyar Waira ta kama shi amman sai azabtuwa yake da abun da be yi zato ba, yaushe ya zurfafa a kaunar ko dan be taba yi ba sai a yanzu, ko kuma saboda yana tarayyar kaunarta da wani ne? Ya sauko kasa yana jinsa kamar ba shi ba, kasar ma takawa kawai yake yana tafiya amman ji yake kamar ba duniya yake ba. Yana isa gurin motarsa ya jingina jikin motar ya kife kansa ya rasa abun da ke masa dadi a duniyar nan. Ya bude motar ya shiga yayi mata key baya yaja motar ya tsaya saitin da zai iya hango window Waira ya faka motar ya bude ya fito ta jingina yana kallonta, kallon windows dinta ma dadi yake masa, a haka zai ji sanyi ko da kuwa be shiga ya ganta ba. He spends hours yana kallon gurin yana jin kamar ta leko ta ce masa magana. Ta inda be yi zato ba ya ganta tsaye a bakin kofar falon tana saukowa ta nufo inda yake, da sauri ya mike tsaye daidai yana kallonta zuciyarsa sai halbawa take, da ace wani ne ya fada masa cewar zai hadu da yarinya kamar Waira ya haukace a sonta ba zai yarda, ko da kuwa za a buga kasa a kafa masa haka. Akwai abun da kike so ne? Ya tambaya yana jin kamar yaje a gushe ya rumgume ta. Ta tsaya daidai shi ta daga kai ta kalleshi. Kai ka wayar min da kai akan addinin musulumci, ka fada