← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 165

Sashe 92

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

na kwanciya a huta. Be sararba ya ji an rumgume shi a baya ana kuka. Cak ya tsaya da busar yana sauraren yadda zuciyarsa ke bugawa da mugun karfi, bugawar da be taba jin irinta ba, bugawar da ta wuce kima, har take neman danne numfashinsa. Da sauri ya juyo sai yayi arba da kyakkyawar fuskar da zuciyarsa ke raya masa be ga wata macen da ta fita kyau ba on earth, hawaye ke mata zuba jikinta rawa yake bakinta na motsi kamar ta yi masa magana kuma ta kasa furta komai, kanta a sama tana kallonsa domin yayi mata tsawo sosai kamar yadda Maleek yake mata kasancewar ba wata mai tsayi sosai ba sai dai kuma ba zaka kirata gajera ba. A yanzu kam baya bukatar tuna inda ya santa ko ya ganta, ya fahimci wacece ita tun a karon farko da yayi arba da ita a gidan Ummi, sai dai siffarta gaba daya ta canja sam ba zaka ganta a yanzu ka ganta a can baya kuma ka ce mutum daya ne ba, sai dai kamanin da suka zo daya. Me kike so? Ya tambaya sai ta rumgume shi ta fashe da wani kukan, rayuwarta ta baya ta tuna mata, rumgumar da ta yi masa ta farko ta rumgume shi ne ba dan tasan waye ba, a yanzu ta gane Ameer ne hakan ya bata gwarin guiwar sake rumgumeshi domin a gurinta ba laifi ba ne, kasa motsi yayi har sai da ta gaji da kukan ta dago kanta. A ina ka iya wannan busar? Waya koya maka? Wannan ne karo na biyu ta ji yayi busar bayan busar da yayi a cikin dajin lokacin da take boye. Yawo yake da idonsa a fuskarta kamar mai kirga abu. Ya aka yi kike magana? Waya kawo ki nan? Ka fara amsa min ni Wani ne ya koya min Wani wa? Baki san shi ba, waya kawo ki nan? Amsa mata yake yana tambayarta idonsa akan kyakkyawar fuskarta mai daukar hankali ko kyabtawa ba yayi, wani irin kallonta yake kamar zai cinye ta, irin kallon nan dake tafiyar da hankalin mai yinsa ya mantar da shi a inda yake da duk wata damuwa da yake ciki. Ya aka yi kika zama haka? Ya aka yi kike iya magana yanzu? Ya kama hannunta yana dubawa, ko tabo babu balle alamar cizon maciji. I have so many questions for you Girl, you change alot, kamar dai bake ce yarinyar nan ba Ni ma ina da tambayoyi da yawa Ta amsa tana fisge hannunta daga riko da yayi mata. Ya dafa kansa ya daga sama. Oh my God Gani yake kamar ba ita ba ce, a lokacin da ta yi masa magana a gidan Ummi hankalinsa ba akanta yake ba dan haka be yi realize duk wani abu da ta fada ba, shi dai ya san ta rumgume a sa'ilin da kasa rabata da jikinsa kuma ya kasa ce mata komai har sai da Yesmin ta fisgeta a jikinsa. Ya Maleek ya kawo ni Ya dawo da kansa kasa ya kalleta. Fada min waya koya maka wannan busar? Me yasa kike son ki sani? Saboda mutum daya yake wannan busar, wani be isa ya ko yi yadda ake yi ba, kai ya aka yi kake yi? Ina Eid? Eid..? How do you know him? Ya tambaya yana karin hancinta. Kamin ta amsa masa ya nufi hanyar fita Garden din tunawa da yayi ta fada masa Maleek ya kawo ta, me Maleek zai kawo ta yi me yasa ya kawo ta? Ta fada musu tana da alaka da shi ne. Ina Maleek din yake? Yana can waje Ta nuna gate tana biyo bayansa, da sauri ya nufi gate din ya bude ya fita. Maleek na tsaye yana kallon wasu gidajen, zuciyarsa cike da haushin Ameer, saboda Ummi kawai ya tsaya nan ba dan ita ba da babu abun da zai tsayar da shi a kofar gidan. What now? Me ka zo yi? Ameer ya fada yana daga bayansa tsaye, Maleek na jin haka ya saka hannayensa aljihu ya cigaba da kallon da yake, sai yayi kamar be san da mutum bayansa ba. Are you here to celebrate? Maleek ya bawa banza ajiyarsa, domin ya san idan har ya juyo yayi masa magana to ba zai fada masa mai dadi ba, shi a yanzu baya ma son ganin Ameer din da idonsa. All those years kana min kallon wani kalar mutum na dabam right? Saboda kansan gaskiya, boye gaskiyar me ya haifar? Da ace na san gaskiya da ban yi soyayyar karya da kanwarka ba Sai a lokacin Maleek ya juyo. Matsala ta da kai kenan, kai ba shaye shaye ba, sai surutai kala kala, ka san mun rasa Nimra kenan? Amman kake tsaye a nan kana fada min magana marar kan gado? Saboda ka zama an Ummi sai na yi celebration? Maleek ya kara takowa ya isa daf da Ameer. No na ji ba dadi ne saboda Ummi bata cancanci a kamar kai ba, arrogant, wanda be iya komai ba sai son kai da wulakanta mutane, Ameer har duniya ta nade ba zan manta cewar kai ka yi silar mutuwar Nimra ba, kuma ka gode Allah Ummi tana tare da kai, ka ci albarkacinta saboda ka zama daga tsatsonta, if not Wallahi da sai na saka nadamar da sai ka yi nadamar haihuwarka da aka yi Ameer yayi murmushi. Kai kasan waye ni Maleek ba yi wani wanda zai saka ni nadamar ba, sai dai idan na ga lokacin nadamar yayi na yi dan kaina, ka ce Ummi bata cancanci a kamar ni ba, sai kuma ga shi ta hada jini da ni? Ya aka yi? Fitowar Ummi ce ta saka duk suka kalleta, tana ganin yadda suka yi kirko kiro ta san ba lafiya ba, sai dai ganin Ameer da ta yi ya kawar mata da damuwar sanin dalilinsu na tsayuwa har suna fuskantar juna kamar abokan gaba. Ameer a na, i just come to check on you Ta kai hannu ta taba shi sai ya kauce ya matsa baya, ya dauke fuska. This should be the last time da zaki zo duba ni, ba ki ba ni kulawa a lokacin da nake bukatarta karki ce zaki yi kokari yi a yanzu Maleek ya watsa masa wata uwar harara yana jin kamar ya shaki wuyansa. Sai dai shi mutum ne dake kokarin danne abun a zuciyarsa dan haka ya budewa Ummi mota. Ummi shiga muje Ummi ta kalli Motar sannan ta sake kallon Ameer cikin wani yanayi mai kamar na tsoro ko fargabar zuciyar Ameer ta ce. Akwai abubuwa da yawa da ya kamata ka sani, ka ba ni dama na bude maka komai Ameer Ya tari numfashinta. Bana bukatar sanin komai Ya juya sai kuma ya juyo. Sorry for the lost na ana daga cikin yayan da kika fi kauna, Allah ya mata rahma Ya sake juyawa zai shiga cikin gidan, sai Waira ta bi bayansa. Maleek ya kirata, ta juyo kamar a razane. Ina son zan tambaye shi wani abu ne Ta fada muryarta na rawa. Maleek ya bude mata ido. Shiga mota Ta kalli Ameer kamar zata fashe da kuka ta zagaya gurin motar da Maleek ya bude ta shiga. Sai anjima Ameer, na gode Ummi ta fada sannan ta shiga motar, sai gashi ya juyo yana kallonta har ta shoga motar Maleek yaja suka bar gurin. Kansa ya daga sama hawaye suka zubo masa ta gefen ido. Ummi magana kawai zan yi da shi, wani abu zan tambaye shi Waira ta fada tana girgiza hannun Ummi, so take Ummi ta cilasta Maleek komawa gidansu Ameer ta yi masa tambayoyi abubuwan da take son sani da kuma wadanda suka shige mata duhu. Ummi ki ce ya koma Duk magiyar da take Ummi, Maleek be ce komai ba har sai da suka faka compound din gidan. Ummi please ki ce Ya Maleek Juyowa yayi ya watsa mata harara sannan ya bude motar ya fita, ya budewa Ummi ta fito tare da Waira. Abun ka da mai na ci sai ta sake rokon Ummi ba Maleek umarni komawa gidansu Ameer, ko kuma ya kaita ya barta a can har sai ta gama abun da take sannan ya daukota. A nan ya daka mata tsawa daman ransa a acen yake. Ba zan koma ba, babu wanda zai koma gidan nan, ko sunansa na sake ji a bakinki sai na miki dukan tsiya, Ummi that's enough ba zaki sake zuwa ganin yaron nan ba, ko da ba ni zan kai ki ba zaki sake saka kafa da sunan ganin Ameer ba, ba zan jire yadda yake amsa miki magana son ransa ba i won't tolerate that Ummi ta yi murmushi cikin tattausan lafazi ta ce. Shi ma ana ne, banbancin ka da shi kai Aliyu ne ya haifeka, Shi kuma Zaharadeen, kai sunanka Maleek shi kuma Ameer, amman a cikin uwa aya kuka fito, a mahaifa aya kuka zauna, a yanzu ya fika bukatata, domin ban samu rayuwa da shi a lokacin da yafi bukatata ba, kai ma lokacin da kake kyamata ma jure zama da kai, da duk wani abu da kake yi min har zuwa yau da komai ya yaye maka, miyasa shi ba zamu ba shi damar yin fushi har ya fahimci manufata ya sauka ba? Ummi yaron nan ba shi da tarbiya idan ba haka ba, ai ko wace uwa a bar girmamawa ce a gurin ko wane an halak, amman daman can shi ne matar kirki a cikin abokanmu, kalli abun da yayi ma Nimra Mutuwa ma tana kunyar idon mahaifiya, ya kamata ka tausasa kalamanka kuma maganar Nimra! Ni ya kamata ka dorawa laifin, ba wanda be san komai ba. Ya fahimci Ameer an uwanka ne na jini That's the most painful part Ya fada ya rufe motar ta karfi ya nufi cikin gidan da wani irin fushi da Ummi bata saba ganin Maleek a cikinsa ba. Idan aka samu rashin hadin kai a tsakaninku, wani sabon ciwo ne a gareni, Allah ka hada min kan Ta kama hannu Waira suka shiga ciki. A falo Ummi ta samu Dr Zaune zaune Namra na cinyarta kwance daga ita har Namra sharar kwalla suke. Namra na ganin Ummi ta tashi
Chapter 92 · 0% Book details