Sashe 73
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
gadon da take kwance sannan ta bude, a nan suma suka gane ba bachi take ba. i thought bachi take ma Mahmood ya fada, Namra kan ido ya mata bata iya magana hawaye kawai take ganin yar'uwarta a cikin mawuyacin hali. Ummi ta zauna a kujerar dake gefen gadon ta mika hannu ta rika hannun Nimra. Wayar Mahmood ta yi ringing hakan ya saka shi ciro wayar daga aljihunsa ya fice daga dakin, Namra kuma ta matso kusa da gadon tana kallon yar'uwarta. Kullum Ummi ke take yabo cewar kin fini far'a kin fi ni son mutane kin fi ni jarunta, yau kuma ke kika kasa jure zafin rabuwa da wani? Har kika zabe shi kika bar mu? Namra be dace ki yi mata wannan maganar yanzu ba Ummi ban ni na fada mata, shi fa idan ya rasata wata budurwar zai sake, nan da shekara ma ya manta da ita, mu kuwa idan kika zabe shi kika bar mu mun rasa ki kenan har abada, ba zamu iya cigaba da rayuwa babu ke a gidan nan ba, rayuwa zata zame mana ta dabam, tare muka taso Nimra tun kurciya har girma sai yanzu da muka girma zamu fara kafa na mu iyalin sannan zaki fara canja min? Kin san tashin hankalin da na shiga? Tana maganar da fada hawaye na mata zuba. Nimra ta lumshe ido hawaye suka sauko ta gefen fuskarta. Namra wuce ki fita waje, idan kin natsu sai ki dawo, amman ki daina daga mata hankali Namra ta bi umarnin Ummi ta fice daga dakin, sai Ummi ta kara matsawa tana kallon Nimra da idonta ke rufe. Nimra ki rika tunawa da mu mana, dubu yadda yar'uwarki ta shiga damuwa Ta kai hannu ta cire oxygen din dake bakinta ta bude idon Ke ma ai kin shiga damuwa ai Ummi Eh amman mu muka ja komai, musamman ma ni, kina kallona ni da mahaifinki a matsayin wadanda suka hana ki auren wanda kike so, kin nuna biyayya a garemu Nimra tun da har kike gudum bacin ran mu ki yi soyayya da shi a boye, kuma na gamsu ba ki watsar da tarbiyar da muka miki ba, saboda baki bashi kanki ba, abun da kika aikata kuskure amman duk da haka na yaba da yadda kika rike mutuncinki Ta maida Oxygen din dake taimaka mata gurin numfashi har sai da Ummi ta gama maganarta sannan ta sake cirewa. Ummi da gaske ke ko Abiey ba ku cilastawa Ameer rabuwa da ni ba? Wallahi ko magana ba mu sake yi da shi ba, tun bayan da ya kira mu muka zo muka dauke ki, Nimra ba dan dalilin da na fada miki ba, Wallahi da na miki alkawari ko sama da kasa za su hade sai na aura miki Ameer, saboda ina son farincikinki kuma ina jin kamar nakasu na gurina ace kina son wani abu na kasa yi miki shi Ummi ta fashe da kuka, Nimra ta cire Oxygen din. Ba mu rasa komai ba tun tashinmu har girma, ban san wata rana da kika yi mana wani abu na cutarwa ko kuntatawa ba, ba ki bar mu mun yi kewar uwa ba, tun da na girma ban san wani abu maraici ba, Wallahi Ummi har mantawa nake cewar a cikin wata uwar muka fito ba ke ba, saboda kin maye mana gurbin komai Tana maganar tana tsayawa saboda numfashinta dake gargada. Da ace na ji maganar ku da nima ban fada a wannan halin ba, a yanzu ba son Ameer ne ya fi kona min rai ba, Ummi ya yi min rantsuwa kuma ya fada min a iya gaskiyarsa cewar shi tun asali baya so na, kawai yayi hakan ne saboda ya dauki fansa, sai dai yaji tausayina bayan komai ya faru shiyasa ya hana ni guduwa, Ummi idan na yi tunanin ta wani bangare sai na gane gaskiya yake fada, Ummi wannan kalmar ta fi tsaya min a zuciya fiye da kokarin raba ni da shi da kuka yi Ummi ta kara jimke hannunta with shock. Yaushe ya fada miki haka? Dazun, na kira shi da wayar Umar dake hannuna ya fada min haka, shi ne dalilin da ya saka na kasa numfashi.... Ta lumshe ido daker ta bude kana ganin yadda take jan numfashin kasan tana cikin wahalar numfashi. Miyasa yayi miki haka toh? Saboda ya dauki fansar Ya Maleek da kuma ni da yake ganin kamar hada kai aka yi da ni a cutar da shi Ummi ta hade yawu da tana jin bacin rai akan abun da Ameer ya aikata for the first time, miyasa zai fada mata hakan a lokacin da take cikin tashin hankalin rabuwa da shi? Kuma daman can ba sonta yake tsakani da Allah ba da akwai aure a tsakaninsu haka zai saka mata ya ki aureta ya bayan yayi breaking heart dinta? Ummi ina kaunarki sosai Ta fada tana kara jimke hannun Ummi tare da dagowa ta sai Ummi ta kai jikinta kadan ta rumgumeta, suna haka aka turo kofar dakin Abiey ya shigo fuskarsa dauke da damuwa sosai. Tun da muka kawo yarinyar asibiti kin ki barta ta huta, a gabanki dazun likitan ya fada mana cewar hutu take bukata, na san kuma idan kina dakin nan ke ba zaki huta ba ita ma ba zata huta ba Ummi ta daga jikin Nimra ta mike tsaye gaba daya tana kallonta da hawaye a idonta. Mutuwa kadai ta isa ta shiga tsakanin uwa da ya Abiey, idan bana kusa da ita damuwata karuwa take, kuma zamana a kusa da ita ita kuma kara mata damuwa yake Dan Allah ki kwantar da hankalinki, ciwo ne fa kawai zata ji sauki ta tashi kamar ba ayi ba, yanzu da wanne zan ji tashin ha kalinki ko ciwonta? Ummi ta sauke kai kasa ba tare da ta sake cewa Abiey komai ba ta saki hannun Nimra ta juya ta fice daga dakin. Abiey ya zauna a kujerar data tashi yana kallon Nimra dake kallonsa oxygen a hancinta da bakinta. Ya dade yana kallonta sannan ya mike tsaye ba tare da yace da ita komai ya nufi kofa sai ta cire Oxygen din dake bakinta ta ce. Abiey ka yafe min dan Allah ka yi hakuri Ya juyo da sauri ya dawo ya zauna ya kai hannu ya shafa goshinta. Da ban yafe miki ba, ba zan so asibitin nan kuma har na shigo cikin nan ba, kin yi kuskure a matsayinki na ya kuma yar adam, ni kuma na yafe miki a matsayina na mahaifinki, Allah ya baki lafiya kuma yayi miki albarka Ameen Abiey Ta fada tana jin sanyi a ranta. Abiey da gaske Ummi ita ta haifi Ameer Abiey yayi jimm kamar ba zai ce komai ba, be mamakin sanin da ta yi ba wata kila Ummi ce ta fada mata haka saboda ta warware mata tsakanin tsare da abawa, na haramcin aurenta da Ameer. Nimra kina a yanayin da be kamata mu yi doguwar magana da ke ba, hutu kike bukata a yanzu, idan kin samu lafiya sai mu yi magana kin ji Abiey dan Allah ka fada min, ina son na sani, gaskiya ne ko? Gaskiya ne Zahra ita ta haifi Ameer kuma jininta ne Amman Abiey miyasa bata tare da shi? Mutanen da yake nunawa a matsayin iyayensa su waye su? Idan kika samu lafiya zan fada miki komai da kaina, fata dai yanzu ki samu lafiya karki zurfafa tunani zai kara haifar miki da damuwa i love you you should know that Ya sumbanci goshinta hawayensa na diga a saman kanta, sai ta yi murmushi ta lumshe ido tana jin son mahaifin nata a ranta. Bata bude idon ba har ya fice daga dakin, yana tafe yana tunanin Ummi a ransa, tausayinta ya cika masa zuciya fiye da kullum, shi da yake a tsakanin rayuwar yarsa da rasata yana jin kamar ba zai iya jurewa idan ya rasa ta, saboda mugun son yayansa da yake da kuma shakuwa da yayi da su, balle kuma Ummi da ta rayu a tsaye shekara da shekaru babu danta a kusa da ita, alhalin yana raye a yanzu kam ya tabbatar ciwon nan yana tare da ita, ta wannan babin kan ya jinjina mata matuka. Ya isa gurin da su Ummi da Dr Zajnab, Yesmin da Juwairiyyya, Mahmood da Maleek suke zaune har da Namra. Ummi na ganinsa ta mike tsaye sai yayi mata alama da ta zauna. Matukar kika ce zaki tare a dakin can to mota zan saka ki mu tafi gida yanzu nan, domin na ga alamar ba zaki barta ta samu hutu ba Ummi ta koma ta zauna suna kallonta. Ba a barin marar lafiya shi kadai ai Toh ga Dr nan sai ta tafi gurinta ta zauna, ke kuma sai ki tashi mu tafi gida saboda babu kowa a cikin gidan an kwashe duk kun zo nan kun tare, kamar ni ne ba ni da lafiya Duk sai da suka yi murmushi da ba su shirya masa ba har Ummi dake cikin damuwa. Abiey idan kai ne baka da lafiya ai har masu gadin gidan sai sun tare a nan Maleek ya fada yana daga zaune a dayan carpet din da aka shimfida. Abiey yayi murmushi ya ce. Balle ma ba zan yi ba, sai dai Umminku Ummin ma muna sonta Abiey Namra ta fada, sai duk suka saka dariya kamar babu damuwa a ransu. Sun dan taba hira sannan ya wuce tare da Maleek Juwairiyyya, aka bar Namra daman tace ba zata tafi ba, sai Yesmin dake lake da Mamarta wato tsohuwar likita Dr Zainab inda suka tare a dakin Nimra, harabar ta zama daga Mahmood sai Ummi da Abbie ya hana ta shiga ciki da Namra wacce ganin halin da yar'uwar haihuwarta take ciki yake daga mata hankali. Abiey na gaba zaune Maleek na tuka motar Juwairiyyya na baya tana taba wayarta, titi kawai Abiey yake kallo amman hankalinsa yana wani gurin har suka isa gida. Masu gadin suka bude musu gate, kamin Maleek yaja motar su shiga ciki Police din da tarbi Humaira ya iso gurin motar Maleek na ganin hakan ya saukewa Abiey gilashinsa domin ta side dinsa ya tsaya. Ranka ya dade, dazun na so na baku