← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 165

Sashe 31

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi dai be sake ce mata komai ba ya fice. AMEER POV. Fitar Ameer da kamar minti biyar da fitar Ameer Daddy ya kira Momy sai a lokacin yake fada mata abun da ya faru, da kuma response din Ameer akan cewar shi be san da labarin yarinyar ba. Wata kila da gaske ne, kasan Ameer baya tsoron amsa laifi idan ya aikata kamar yadda ya amsa maka cewar ya karbi motar Ajiyar zuciya ya sauke mai dauke da damuwa. Ina fatar haka, sai dai ina jin kamar ba yarda da shi ba, kwana biyun nan abun da Ameer yake ya fi karfin na baya Jarabawa ce, dole hakuri zamu yi muna masa addu'a har Allah ya shiryar da shi, kuma ni ina ganin kamar ayi masa aure a zai saka ya natsu Tun da nake da Ameer be taba min zancen soyayyar ba, gaba daya mata basa gabansa shiyasa na sha mamaki lokacin da yake fadar akwai wata yarinyar shi har suka samu matsala da abokinsa Kai mahaifine ai, zaka iya zaunar da shi ka nuna masa inda kuskurensa yake, idan ya manta karatun sai ka tusa masa, yaran yanzu sai da haka, kuma duk wata lalace da kake ganin Ameer yayi laifinka ne, sam baka yarda ayi masa magana idan yayi kuskure Akwai yara da yawa da suka tashi a cikin gatan irin na Ameer, amman basa yin abun da yake yi, zai fi kyau mu dora abun a babin kaddara Allah ya hukunta kawai Toh Allah ya shirya mana, amman gaskiya a maida hankali gurin yi masa aure kasan aure yana natsar da Mutum kuma idan an tashi kar a nema masa yar Babban Mutun domin ba ko wace mace ce zata iya zama da shi ba, sai dai a nema masa mai hakuri wanda zata iya bin halinsa Idan kuma yana da wanda yake so fa? Shikenan ta kwana gidan sauki, sai a aura masa daman ai ya kai munzalin auren kuma Allah ya hore komai Nima kuma shekaru suna ja, ina da burin ganin haka kamin ta Allah ta kasance Furucin da Daddy yayi sam be yi mata dadi ba, hakan ya saka bata sake cewa komai ababin maganar ba. Zan aje waya, saboda ina shirya abincin rana Yayi murmushi ya sauke wayar, sannan ya sake kiran CP, duk wani abun da za ayi a kashe maganar Daddy yayi domin baya son damuwa a yanzu kamar yadda likitansa ya tabbatar masa. Jikin Motar Momy ya jingina thinking of din yarinyar ta mutu yadda zai bata ma Maleek da kanwarsa suna, a yanzu din ma tunanin yadda zai yi amfani da wannan damar ya taba martabar gidansu Maleek yake, he just wants to take revenge shi dai zuciyarsa suna masa take Maleek yayi masa Zagon Kasa, ya bude motar ya shiga yayi mata key jin kamar yana marmarin gurin da suka saba zama da abokansa ya saka shi nufar wani gurin shakatarwar na dabam, domin baya son ya sake shiga safgarsu tun bayan wulakancin da suka masa na zabar Maleek su barshi. MALEEK POV. Babu wanda yace Uffan a cikinsu bayan Abiey ya gama labarta cewar Ameer yace shi be san yarinyar ba be san inda ta fito ba kuma ba shi da alaka da ita. Amman karyar yake yi yana son ya kulla mana wani abun ne kawai Namra ta fada cikin jin haushi domin ji take kamar ace yana gabanta ta kwada masa mari. Ummi ta kalleta a hankali jin yadda take magana da zafin rai sai dai bata ce komai ba ta mai da kanta kasa tana jin zuciyarta ba dadi. Maleek ya saka hanayensa aljihu Wata kila kuma gaskiya ya fada, domin na san waye Ameer baya shakar ya amsa laifi komai girmansa matukar ya aikata zai ce shi yayi, idan har be amsa ba to be aikata din ba ne Namra ta girgiza kai. To waya aikata? Waye zai yi hakan bayan shi? Ko da ma ace wani ne yayi ai shi ne sila, kai da Ummi kamar kuna son kare Ameer din nan makiyin mu ne fa Maleek ya nunata da yatsa. Don't you dare raise your voice on me, na ce be aikata ba and i meant it tun da ya amsa cewar ba shi ba ne ba shi din ne ba, beside ai yarinyar tana da baki sai ta fadi wanda ya dauko ta CP yace yarinyar bata jin hausa, kuma bata iya turanci ayi communicate da ita ma ya zama aiki Cewar Abiey with curious face. Ummi ta kalli mijinta da fuskarta ta wadanda lafiya bata wadace su ba. Yarinyar tana Katsina ne? Eh likitoci sun ce zata samu wata daya zuwa 6 kamin ta warke garau We can stay with her a nan har ta samu sauki kuma ta iya fahimtar yarenmu ko kuma mu mu fahimcin nata, then sai a hadata da yan'uwanta Maleek ya karba mata. Shi ne akwai yafi daman police sun san da maganar in case of wani abun ya faru suna sane, tun da yarinyar bata da wanda zata zauna a gurin can KT din, maybe ma daga wata kasar aka satota aka samu motar a ajeye aka saka ta a ciki, mude Allah tana raye that's just it Shi ne, tun da mace ce be kamata a barta a can ba, ba zata samu kula yadda ya kamata ba, kuma babu kowa a can tare da ita, ko ba komai mu muke da hakkin kula da ita saboda a motar Nimra aka ganta Ummi ta sake fada duk da ta san ba lallai ne Abiey ya yarda ya dauki shawarata a yanzu ba, Nimra kam bata ma falon domin ganin take kamar mahaifinta be bukatar ganinta a yanzu bayan duk abun da ta jefasu ciki, itama kanta tana kunyar hada ido da shi. Kar kuma mu aikata abun da zai zama mana na nadama daga baya! Kar ta zama mana cuta Abiey ya fada a nasa fahimtar kamar be kamata yarinyar ta zauna a gidan ba, domin mai son abin ka ya fika dabara. Ko da ta zo da wata muguwar manufa Allah ba zai barta ba, domin mu mun yi da niyar kwarai ne, kuma Allah yana kallon zuciyar kowa Wannan karon da gwarin guiwa Ummi take fadar haka, Mahmood ma be ce komai ba domin shi dai baya goyon bayan kawota a gidan kamar yadda yake a zuciyar Namra. Idan ma haka ne, ai shi Mahaifin yaron ya fi cancanta ya rika saboda dansa ya jefar da motar Idan kuma be rikata ba, sai mu rika rayuwa ce be kamata a salwantar da ita saboda jayayya ta son zuciya ba, In Shaa Allah babu wata matsala da zata faru Ummi ta amsawa Abiey da yayi maganar with full confidence. Khadeeja Candy Copyright 2023 KHADEEJA CANDY 17 Tun a jiya da ya gama aikinsa ya bar asibitin be sake shigowa ba sai washe gari, yanayin aikin da ya tarar a office na duba patient ya saka be bi ta kan patient din suke kwance ba, sai abokin aikinsa ne yayi da zimmar shi zai duba su da rana idan zai fice. Misalin karfe daya da yan mintuna ya tashi aikin, sai dai be dauki komai nasa ba ya fita yayi Sallah a Masallacin, sannan ya dawo Office din ya bude akwatinsa ya dauki Stethoscope tare da wasu files ta saka Lab Coat ya fice, ya dade yana magana da wani abokinsa da ya tarar a ward din yana hira da nurse, tattauna suke akan zaben da za a gabatar na Nigeria da kuma wanda suke ganin idan aka zaba zai kawo canjin da sauyi a Nigeria. Safar hannu ya fara sakawa, Nurse din da suke duty suka rufa masa baya su biyu domin gabatar da na su aikin. Daya bayan daya ya rika bi yana duba mutane kamin ya kawo gurin yarinyar da ya duba jiya, gaba daya gadonta a zagaye yake an rufe shi da curtains din da ake rufe gadon marasa lafiya, yana daga curtains din Nurse din dake gefensa ta ce. Yarinyar fa ina tunanin kamar bata da hankali, tun jiya bata barin kowa ya taba ta kuma ta koma karkashin Bed din sai kuka take Halima tace min ko bachi bata yi sai ta leko sai ta koma ta boya Shiga yayi ya leka karkashin gadon sai ya hangota ta cunkushe guri daya ta rumgume hannunta mai ciwo. Hannunsa ya saka aljihu ya ciro wayarsa ya kunna flashlight dinsa ya haska ta sai ta yi saurin rufe idonta domin hasken yayi mata yawa, tun da take a rayuwarta bata taba ganin hasken gulub ko na fitilar hannu ba, iyakar su hasken aci balbal ko na wutar itace ko ta kara. Nurse din zata yi magana sai ya daga mata hannu ya kashe fitilar ya mika mata hannunsa. Baby girl zo nan Kin kallonsa ta yi balle ma ta mika masa hannun, mikewa yayi tsaye ya ciro kudi aljihunsa ya fita daga gurin ya aiki daya daga cikin masu sharar gurin ta siyo masa apple da ruwa. Tun jiya bata ci abinci ba, kuma aka rasa wanda zai kula da haka? An kula fa masu jinya sun bata abinci ko dazun, amman ba ta ci ba ruwan kawai ta sha, kuma ta ki fitowa a kasan gadon Police din jiya ba su dawo ba? Bana jin sun dawo, shi ma wanda aka bari nan ba a nan ya kwana ba kuma be dawo ba, da sun dawo da mun samu labari kuma babu wanda ya zo dubata, ni ina ganin kamata yayi ace sun dauki hotonta sun saka a Internet ko Allah zai saka a dace da yan'uwanta Dr Shuraim dai be sake cewa komai ba, ya cigaba da duba masara lafiyar da suke gabanta, har sai ya gama sannan ya karbi aikan da yayi ma mai share sharen Asibitin, son ganin yadda zata kaya ya saka suka biyo bayansa har da wace ya aikan. Dukawa yayi ya lekata tana ganin fuskarsa sai ta yi saurin rufe ido. Sabuwar takardar ya karba ya dora mata apple din akai ya tura mata, sannan ya aje ruwa ya dauke kansa. Be yi zaton zata yi saurin aminta ta taba ba, sai gata ta miko hannu ta dauki Apple
Chapter 31 · 0% Book details