← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 165

Sashe 5

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

kwana a gurin, zaki iya samun wani kyalle ki rufe shi akai gudun kar wani abu ya taba, da safe zaki duba ki dauko ki wanke sai ki saka girishi kadan, shi saka gishiri da a ciki rubutu yana da karfi sosai, wasu malaman man suka ce har ya fi zuma, duk wani sirri da ake da madubi ko ake saka zuma farar saka ko gishiri yana da kyau sosai gaskiya Hajiya Saude taja dogon numfashi ta sauke yana jinjina lamarin yadda kawarta ta san sirrin da ita bata sani ba. Lallai Hajiya yanzu duk kin san wannan amman kika bar ni ina zaune haka nan To ai baki bukata ba ne, ni Wallahi ba boka ba Malam amman mijina sai abun da na ce, amman fa ina hada masa da biyayya sosai da kuma balmar baka, kin san mata sai da salon zancen da kisisina. Bari na kara miki da wani sirrin mai karfi gaske shi wannan ma mijinki ba zai taba iya boye miki sirrinsa ba, idan kina da koshiya ki saka sunanta ita ma zata biki sau da kafa ku zamu zaman lafiya, wannan tawada mai kyau zaki samu ki sai ki dauki Kur'anenki ki bude suratul Yusufa, ita wannan ayar ana sarrafa ta kala kala ko da yarki ce ta rasa mijinki aure zaki iya sakawa ayi mata sai dai kowane sirri da yadda ake hada shi... Shigowar da Ameer yayi a falon cikin tsananin fushi babu riga a jikinsa ya saka ta yanke maganar da take da Hajiya Saude ta juyo tana kallon an mijin nata, ba abun mamaki ba ne ta ganshi rai a bace domin abu kadan ya bata masa rai ko da be taka kara ya karya ba, sai dai na yau kamar ya dara na kullum, domin ya shigo falon kamar an korashi a waje. Ameer lafiya? A maimakon ya amsa mata sai ya aika mata da tambaya cikin zafin rai. Balarabe ya shigo nan? Be shigo ba, Allah yasa ba shi yayi maka laifi ba Momy na aje numfashi, Baba Balaraben ya kwankwasa kofar falon, sannan ya turo ya shigo a hankali, jiki na rawa ya karaso kusa da Ameer yana fadin. Ranka ya dade Wallahi ban gane abun da kake magana kai ba, ka ga abubuwan da na samu Ya bude bakar ledar dake hannunsa ya ciro wasu kanan gel na wanke fuska yana nuna masa, kamar kibtawa da bismillah haka Ameer ya dauke tsohon da zai kai shekara sittin da uku mari, a take ledar dake hannun Baba Labarabe ta subuce ta fadi, ya dafe kuncinsa yana kallon Ameer, Momy da Hajiya Saude suka mike tsaye. Ameer ni ka mara? Okay tambaya ma kake kenan? Bayan kaje ka yi min shirme? What do you expect na gode maka? Tun ina hanya na kiraka na fada maka ka samo min chemical na wanke fuska shi ne zaka kawo min wannan shirmen? Momy ta yi saurin karasa kusa da Ameer ta dafa shi ta yi baya da shi har ta danganashi da kujera ta zaunar, sannan ta juyo ta kalli Baba Balarabe dake dafe da kunci har lokacin ta ce. Dan Allah ka yi hakuri, Ameer idan ransa ya bace baya iya controlling kansa Babu komai Hajiya, duniya ce amman dai kam aiki a nan na hakura da shi har abada domin talauci be kai ya saka an cikina ya mare ni ba, ban yi wannan lalacewar ba Ya fada ciki wani da ya fi kama da tausayi da bakinciki, Hajiya Saude ta saka baki gurin bada hakuri amman ina be saurareta ba har ya fice. Sai wani ya bata maka rai ka zo ka huce akan na gida miye haka ne Ameer? Momy ta fada a tsawace a kokarinta na nuna masa abun da yayi ma Baba Labarabe be kyau ta. Shi ma wacan ba kyale shi zan yi ba, na ra tsantse sai yayi nadamar abun da yayi min Waye kuma? Wani dan iska ne, wai ni zai watsawa yawu a fuska? Ban san yadda zan wanke fuskata ba, i don't want to use my hands, ji nake kamar na daye fatar fuskar nan na saka wata Shi ne kawai dalilin sakawa a siyo maka chemicals na wanke fuska? Sai kace wanda yake dauke da wata cuta? Kallon mamaki yayi ma Momy domin shi a gurinsa kazanta ce. Yawu fa Momy, kuma na bakinsa? Ya zan rayu? Ya runtse ido numfashi ma daker yake yi domin ji yake kamar idan ya maida numfashinsa zai shaki wata cutar ne. Momy ta juyo ta kalli kawarta Hajiya Saude Hajiya zamu yi waya Toh Allah ya saukewa, zan kira anjima ko gobe Na gode sosai da ziyara, sai mun yi wayar Hajiya Saude ta dauki jakarta ta nufi kofar fita tana jin cewa ita kam ba zata iya daukar abun da kawarta take daukarwa an mijinta ba. Yanzu tashi muje na wanke maka fuska na san kyamar ba zata bari ka saka hannunka ba Ke ma idan kika saka hannunki ba zan iya sake cin wani abu da kika girka da hannun ba Zan saka safa kuma zan fara wanke maka da cotton Kamar wani karamin yaro haka ya wuce gaba ta bi bayansa har bandakin, sai da ta rufe hannayenta ta da safa, sannan ta saka kada ta fara wanke masa fuskar kana ta saka sabulukan da suke nan, ta wanke masa fuskar ya fi a kirga sannan ya kyale fuskar tasa ta huta ba dan ya gamsu, datti ya fita ba sai dan babu yadda zai yi fuskarsa ta sha murza har ciwo take masa. Wai waya maka wannan abun ne? Momy ta tambaya a yayinda yake goge fuskarsa da tawul. Wani banza ne, ai sai na masa hankali Tana jin haka sai jikinta yayi sanyi, domin ta san a cikin biyu dole ayi daya, wanda ya aikata wannan abun be san waye Ameer ko kuma wani ne wanda ya fishi isa da jin kai, tabbas ta san Ameer ba zai kyale ba sai ya rama, wanda ramuwar zata iya zama ta zalinci ga wadanda suka yi laifi ko kuma ta zama kofar budewar wata sabuwar fitinar domin shi ma wanda za ayi ma ba zai kyale Ameer ba. Wannan zafin zuciyar duk na minene Ameer miya hada ku? Abokina ne an group din mu ne Ai zaka iya yafe masa indai har abokinka ne, Manzon Allah Sallalahu alaihi wa'asalam.... Bata karasa ba ya mike tsaye ya nufi inda keys dinsa suke ya dauka. Bana bukatar wannan kullum da anyi abu ki wani fara yi min wa'azi bana so, musulunci be yarda a cutar da kai ka kyale ba Ya fada mata sannan ya fice a fusace, binsa ta yi da kallo har ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya. Wannan fushin naka yayi yawa Ameer, dole ne na fara baka ragowar ruwan sallah La'asar saboda ka rage wannan yawan fushin, sai dai ta yadda zaka yarda ka karba ka sha ne matsalar Tana rufe baki Ameer ya turo kofar dakin ya shigo, sai da gabanta ya buga sau hudu a lokaci daya. Ka yi mantuwa ne? Sarewata zan dauka Ya amsa mata da muryar dake kara bayyana har yanzu akwai fushi da bacin rai a tare da shi. Boutique dinsa ya shiga ya bude box din da yake ajiyar sarewar ya daukota tana kamshin turare ya fito, ko kallon inda Momy take tsaye yi ba ya fice. Yadda yake saukowa stairs din sai ka dauka fasa kasa zai yi domin da karfi yake sauke ko wane taku na kafarsa a kasa har suna fitar da amo. Aljannun tsabtarsa ba za su bar shi ya shiga motar da ya dawo da ita yanzu ba, saboda gani yake kamar yawun da Maleek ya watsa masa a fuska sun shafi motar daman rigarsa tun a hanya ya cireta ya jefar. Wata motar ya nufa ya cire ledar da aka saka aka rufe ta ya jefar kasa ya bude motar ya shiga yayi mata key, kamin ya isa gate masu aikin bude gate din gidan har sun kammala aikinsu domin sun fi kowa sanin yadda ya tsani jira a bude masa gate. Tuki kawai yake ba dan ya san gurin da zai tafi ba, baya son zuwa gurin abokaninsa domin ya san za su dame shi da maganar Maleek ne, kamar yadda Step mother dinsa ta fara bashi hakurin akan abun da bata sani ba wannan dalilin ya saka ya baro mata gidan ba dan yana da gurin zuwa ba sai dan ya jira daga wa'azin da take son yi masa. Gefen wasu manyan itatuwa ya faka motarsa, nesa da wata motar yan mata guda biyu dake zaune gefen motarsu sun shimfida carpet suna ciye ciyen kayan kwalan da maskulashe. Fitowa yayi rike da da sarewarsa a hannu ya hau bayan motarsa yana ta kallon titi da babu motoci sai jefi jefi, har lokacin zuciyarsa tafasa take tana wani tiriri, be taba jin kaskanci da wulakanci ba irin na yau da Maleek ya tofa masa miyau a fuska, Ameer yana ganin babu wanda ya isa yayi masa wulakanci ko ya tozarta shi sai dai shi yayi ma wasu, amman a yau Maleek ya masa kuma a gaban friends dinsu. Tun da ka fara sai ka karasashi Maleek sai ka kai kasa da guiwoyin ka kana ba ni hakuri Maleek Har wani tauna hakora yake yana furzar da numfashi da karfi kamar shi yayi masa laifi. Ya dade yana kallon sarewar dake hannunsa sannan ya kaita bakinsa ya fara busawar irin busar da babu wanda ya iyata a isa saninsa sai shi da wanda ya koya masa, yana jindadin busar sarewa ko wace kala ce balle kuma wannan da take ta musamman a gurinsa, tana saukar masa da nishadi a duk lokacin da yake yinta, lumshe ido yayi yana busar cike da karewa. Fararen yan matan dake zaune gefen motarsu suna motsa baki suka fara kallon junansu da mamaki, kamin su mike tsaye suna lekonsa. Wow.... Nimra kin ji wannan? Dayar ta fada tana kallon dayar dake kokarin rufe kanta, sai duk suka yi murmushi suna jin yadda busar ki tsara iska tana shiga kunnuwansu kamar ana musu susar kunne. Wanda aka kira da Safna ce ta fara daga kafa ta taka zuwa
Chapter 5 · 0% Book details