Sashe 79
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
motar har ta bude ledar few abubuwa ne a ciki, chocolate, biscuits, sai wani katon milk candy dake cikin gwangwani mai kyalli kamar an watsa masa zinari. Na ki ne you can eat, dan dana na ji akwai dadi Ba ko wane kalar abu take ci ba, dan haka bata taba komai ba sai chocolate shi ma saboda rubutun chocolate ne a jiki, tasan ba irin wanda ta saba ci ba, sai dai a yadda ta fahimta ko wane chocolate yana da dadi sai dai dandanonsu ya babanta. Bakinta ta saka a take hakoranta dake da kaifi suka yanke mata ledar sai ta yaye ledar daga sama ta fara ci a hankali. Akwai dadi? Ta daga masa kai, bata san rowa ba dan haka ta gutsura rabi ta mika masa. Yayi murmushi yana girgiza mata kai Sha abun ki ni bana shan kayan zaki Ta rike da dayan hannunta idan ta ci na hannu dama sai ta ci da hagu, shi dai be ce mata komai ba har suka isa gida kamar yadda ta bukata, ba tare da ya je inda yayi niya ba. A gurin ya tsaya yana kallon motar su Jabir har ya ja suka wuce, sannan ya faka tasa gefen titin. Daman fitowa kawai yayi daga gidan ba dan yana da gurin zuwa ba. Sosai ya zurfafa a tunani yana son gano inda ya san Waira ko ya taba ganinta amman ya kasa, kallon da yayi mata a mota ma yanzu ya ki ya fita idonsa, sai da yayi da gaske sannan ya iya focusing akan abun da ya kamata ace shi ne a gabansa ba tunanin kyaun wata yarinyar da bata san da zamansa ba, kuma karamar yarinyar kanwar kanwarsa ba ma babbar mace ba. Ac motar ya kara sannan ya dauki wayarsa dake aje a inda ya saba aje ya yi dialing number Ammynsa. Kiran farko bata daga ba haka ma na biyu da na uku sai da yayi mata na hudu sannan ta daga. Ameer my son how are you? I'm good Ammy Ya kai hannu ya rage ac jin kamar baya bukatarshi kuma. Ammy wani abu nake son na tambayeki, i don't want you to lie to me, kin san na yarda da ke, karki rushe wanann amince da ke tsakaninmu, kuma karki dubi Daddy ko ni ki fada min abun da ba gaskiya ba please.. Mene ne haka zaka tambaye ni Ameer? Daddy ya kira ki? Ta yi jim kamar mai son ya canja mata tambaya. Eh ya kirani I know na tambaya ne saboda na tabbatar zaki fada min gaskiya ko akasin haka, seriously bana son ki fada min abun da ba gaskiya, idan kika min haka zai yi wuya mu sake shiri da ke, you know how much i love you ko? Kin san ke na kallo kamar uwata right Ni din ma uwarka ce Ameer, tambaye ni duk abin da kake so na maka alkawarin zan fada maka gaskiya Akwai wata mata da na hadu da ita dazun, ta fada min maganar ban da da maganarta ba sai dai kuma sunanki da ta ambata ta ce na aje na tambaye ki idan kina raye ya saka na ji kamar akwai kamshin gaskiya a ciki.... Sai da ya fara bata labarin abun da ya faru tsakaninsa da Maleek duk kuwa da ya san Daddy ya fada mata komai, sannan ya dora da abun da ya shiga tsakaninsa da Nimra zuwa yau da Ummi ta fada masa wannan maganar. Me kika sani game da ita? Ameer Ta kira sannanshi a a hankali, sai ya amsa yana duban agogon hannunsa. A ina kake? Ina kan hanya Tuki kake? Ya amsa tare da bude motar ya fito. A tsaye kake Eh yanzu na fito mota Nemi guri ka zauna Ya koma cikin motar ya maida gambun ya rufe gabansa na faduwa. Akwai wani makami ko wani abun da zaka iya yi ma kanka rauni a kusa da kai? Ya juya ya kalli wukar da ya dauko daga restaurant, wadda ya firgita Humaira da ita. Matsar da shi Ya kai hannu ya dauki wukar ya bude motar ya fita ya jefar da ita sannan ya dawo cikin motar ta saka wayar hands-free ya lakata a mazaunin ta dake cikin motar. Done Yarona akwai ruwa kusa da kai Akwai ruwa a motar Ammy just go on Matar da ta fada maka haka fara ce? Fara ce sosai Sunanta Zahra right? Ban san asalin sunanta ba, amman dai Ummi Nimra take kiranta Ita da mijinta yan asalin garin Kano ne? Nimra ta taba fada min haka Wani labari zan baka da ya shafi rayuwata, kuma ya gurbata zamana da mahaifika, ya nisanta ni da kai Ya gyara zamansa a cikin motar. Ina saurarenki Mahaifinka ya taba baka labarin shekarun da muka dauka ba mu haihu ba? Ya fada min Amman be fada maka miyasa ya rabu da ni ba? Har yau be fada min ba Ameer na kwashe shekarar da ta kusa goma a tare da Mr Bashir, Allah be bani haihuwa ba, na yi iya yadda zan iya ta bangaren asibiti na da hausa amman Allah be bani ba, sai a yanzu na gane ashe ba a rubuto ni cikin wadanda za a rabawa kyautar yaya a duniya ba, yan'uwan mijina suka tsangwame ni, ni ma kuma na matsawa kaina, idan na ga yaya kamar na sace nake ji, ko kukan jariri naji sai hankali ya tashi, Ameer akwai kunci da damuwa matuka a zuciyar uwar da bata taba amsa sunan uwa a bakin jininta ba, ni kadai na san irin kuncin da mace take ji a lokacin da take sha'awar dandana azabar zafin nakuda da dawainiyar daukar ciki. Hankali ya tashi matuka a lokacin da mahaifinka ya gabatar min da magana aure, ina ta jin tsoron kar wata ta zo ta haihu ya juya min baya, duk kuwa da kasancewar ban ga alamar haka a tare da shi ba, a lokacin idan na hana shi aure ban masa adalci ba, kuma yan'uwansa ba za su kyale ba, ina ji ina gani aka daura masa aure sai zuciyata ta kasa hakuri har na fara bin bokaye, duk mace da ta shigo sai a fitine ta ta kasa zaman auren, a haka har ya auri mace hudu dayar har bari ta yi amman ban barta ta zauna ba, sabida jna kaunar mijina sosai. Daga baya na samu wani likita ya ba mu shawarwari akan hanyoyin da zamu bi mu samu haihuwa, a ciki akwai dashen kwan haihuwar, bayan ta tabbatar mana da cewar ni da shi duk bama da matsala zamu iya haihuwa a duk lokacin da Allah ya so, sai na kasa hakuri shi kuma ya ki ya amince da zancen dashen kwan da aka fada mana, yace ya fi son haihuwar ta zo daga Allah kai tsaye Ta tsinke zancen da take ta dauki ruwan dake kusa da ita ta sha. Sannan ta cigaba. Akwai wani Yayana sunansa Dr Hamid, kwararen likita ne dake aiki a Kano, da shi na hada kai yayi min duk abun da ya kamata na magani da allura na fara laulayi irin na masu ciki, kuma ya bani duk wani evidence da zan tabbatar wa da Mr Bashir da gaske cikin ne, farincikin da na gani a fuskarsa shi ya kara min kwarin guiwar cigaba da abun da nake, yan'uwansa suka dawi suna kaunata kamar sun lashe, daman na tsara cewar idan zan haihu zan bar kasar kamar yadda shi ma Mr Bashir ya bukata, na yi ta rainon cikina ni da Yayana muna ta neman inda zamu samu macen da zata ba mu a, ba mu samu ba saboda abu ne dake bukatar sirri, wata rana tsawan Yayana ya kira ni cewar an samu wacce zata siyar da cikinta saboda ayi wa mijinta aikin, na yi matukar murna kuma na jidadi, shi ya nema mana inda zamu hadu har muka ga juna muka kulla yarjeje ta saka hannu nima na saka, na bata copy takardar daya na rike daya dayar kuma tana hannun lauyana, a lokacin da zan haihu sai na ki yarda na bar kasar na haihu a gurin yaya a private hospital da yake aiki, tana haihuwa aka karbo yaron aka kawo min sannan na sanar da dangina da mijina cewar na haihu, mun dawo gida cikin farinciki sai dai yaro idan ya sha nono na baya Lafiya, idan aka bashi madara ko nonon wasu sai yayi ta zawo yana kuka, daga karshe a dole aka yanke shawarar gwada ba shi nonon mahaifiyarsa ta asali, ana gwadawa sai ya karba kuma be bashi matsala ba, hakan ne ya saka na rika aikawa ana tatsar nononta ana bashi daga baya kuma sai tace ba zata yarda da haka ba, sai na biyata kuma zai dai ta dawo gidana ta zauna, babu abun da ya wuce bin umarninta saboda ina son yaron, na sama mata gurin a gidan ta dawo ta zauna, ashe na matso da mutuwar aurena kusa ne ban sani ba, ta ko'ina akwai camera a gidan mu, kuma kanwar mijina Ummiter ta saka min ido sosai a lokacin saboda tana ganin kamar bana sonta na mallake yayanta kuma na kori yar'uwarta, zuwanta a cikin gidan shi ya tona asirina ya wargaza shirina, har mijina ya gano gaskiyar komai ya mallaka mata anta yace ba zai iya cigaba da zama da ni ba, babu kalar magiyar da ban masa ba, amman be saurareni ba, ni kuma hankali be tashi ba sai bayan da ya sake ni saboda soyayyar yaron ta shiga raina, sai dai kamin ya sake ni yayi min alkawarin ba zai fadawa kowa abun da na aikata ba, saboda rufin asirinsa da nawa, ba zan iya fadar dalilin dawowar yaron a hannun Mr Bashir ba, wata kila uwar yaron bata da bukatarsa a wacan lokacin ne, wata kila kuma mijin da zata aura yace baya son yaro, ko kuma tana tsoron fuskarta shari'ar yan'uwan uban yaron na asali ne, ko kuma dai arzikin Mr Bashir ta yi ke ma anta sha'awa saboda idan ya girma ita ma a sha miyar da ita, ni dai kam na san uwar da ta amsa sunan uwa take kaunar yaronta da gaske, kuma take son uban yaronta to