← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 89

Sashe 9

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga aukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye. SHAFI NA BIYAR Cikin mugun yanayin ta kafe shi da wala walan idanuwanta masu razana duk wanda ya yi tozali da ita, a hankali Sarki Abdul'aziz ya fara ja da baya jikinsa na karkarwa. Bai yi tsammani ba ya ji bayansa ya bugu da bangon akin, cikin tsinkewar zuciya yake sauke ajiyar zuwa. Da wata irin san a ta taso daga kan gadon tana durfafo wurin da yake tsaye, ganin tana gabda cin masa ya sa ya fice da sauri daga cikin akin ya arasa wurin dogaran da ke tsaron sashensa. Yanayinsa ka ai ne ya tabbatar musu da tabbas Takawa yana cikin damuwa, tun bai arasa wurinsu ba suka zube cikin girmamawa. "Allah ya taimake ka ya ara lafiya da nisan kwana, awisu sarkin ado mai ta ama da ikon Allah..." "Ya aka yi kuka bar waccan hallitar ta shiga har cikin turakata?" Mai martaba ya katse su fuska a tamke babu igon fara'a. "Tuba muke ranka shi da e, Allah ya huci zuciyar amale a gafarce mu wannan ne na farko na arshe." A daidai lokacin Jakadiya ta arasa ita da Baiwa Saro hannunsu auke da kayan lambun da ake kai wa Sarki Abdul'aziz kamar wannan lokacin. Dogaran ta gani sun nufi turakar Takawa kafin su arasa su ka ga wata ba ar mage ta fito daga cikin turakar idanuwanta jawur kamar gauta tana bin mutanen wurin da wani irin kallo. A zabure Jakadiya ta furta. "Ka gafarce ni uban gidana ka yi mini afuwa, amma ba ni da masaniya game da sakacin Dogaran ofa da har suka bar kyanwar nan ta shiga cikin turakarka." Jakadiya ta yi maganar jikinta na karkarwa don ta san a duniya babu abin da Takawa ya fi tsoro sama da mage, wannan oyayyan sirri ne da ba kowa ne ya sani ba saboda gudun kada magauta su fahimci lagonsa. Ita ma Jakadiya abin da ya sa ta sani tun wani lokacin da ta ta a shiga sashen Mai babban aki (Mahaifiyar Takawa.) wata mage ta shiga har suma ya yi a wurin, kuma ko da ta ga haka sai da Mai babban aki ta tsawatar mata a kan wannan sirrin. "A kiyaye gaba, ba na bu atar sake ganin kowacce hallita a sashena." Gaba aya suka amsa masa cikin girmamawa. Jakadiya da kanta ta shiga ta jera kayan lambun kamar kullin sannan suka fice bayan ta tambayi Takawa ko akwai wani abin da yake da bu ata, ya ba ta amsa fuska babu walwala. Har bayan wani lokaci Sarki Abdul'aziz bai saki jikinsa ba, ganin bai sake jin motsin komai ba ya sa ya an saki jikinsa. Cike da warin gwiwa Fulani Umaima ta arasa cikin turakar Mai martaba, ganinsa zaune a gefen gado kusa da baiwa Maimuna ya sa ta zaro idanu cikin fargaba har sai da ya fahimci ru ewar da take ciki. "Lafiyarki Umaima?" Cikin kissa ta daidaita nutsuwarta ta ce, "Dama na yi mamaki ne ganinka shiru, kar dai ka jima kana jirana." Murmushi ya sakar mata ha e da girgiza kai. Ta arasa wurinsa asirtaccan amshinta ya ratse hancinsa, ya lumshe ido cike da jin da amshinta. "Ki tabbata kin sa shi ya shiga bayan gida kafin ki saka wa Maimuna turare a gabanta." Kalaman Boka Bamaguje ya dawo mata ra au a cikin kunnuwanta. Mi e wa ta yi ta furta. "Sarkina bari na ha a mana ruwa mu an watsa ko?" Ba ta jira cewarsa ba ta nufi ban aki ta ha a komai da kanta sannan ta zuba turaren da Bamaguje ya bata, bayan dawowarta ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa sannan suka wuce ban aki. Da kanta ta ebi ruwan ta watsa masa cikin sigar tsokana, sai kuma ta yi farat ta furta. "Na yi mantuwa." Kallon da ya yi mata ne ya alamta mata yana bu atar arin bayani daga gare ta. "Ina zuwa." Kawai ta furta ta fice a gaggauce. Sai da ta tabbatar da ta rufe ofar ta baya sannan ta koma turakarsa cikin sauri ta aga doguwar rigar Maimuna ta kwara mata turaren a asanta sannan ta shafa mata a fuskarta, ita ma ta murtsuke jikinta da shi ta rage kayan jikinta ta sake komawa cikin ban akin. Tana shiga amshinta ya daki hancinsa, take ya ji wani irin yanayi ya tsarga masa. Bu atar ya kusance ta ta yun uro masa, ganin sa wannin da yake aika mata ya tabbatar mata da ha onta zai cim ma ruwa, don haka ta fara neman shawarar da za ta yanke wa kanta. A hankali ta yakice shi tana fa in, "Sarkina a ban aki muke mu arasa turaka." Bai musa mata ba, ta arasa she a musu ragowar ruwan sannan suka fito hannunta na ri e da shi, idanuwansa a rufe suka arasa don haka ko da ta zaunar da shi a gefen gado ta ga ya rarumo Baiwa Maimuna da ke zaune kamar gawa. Fulani Umaima ta koma gefe ta zuba masa ido zuciyarta al, tana nan tsaye Takawa ya gama mu'amalarsa da Maimuna ya koma gefe aya sai gani ta yi numfashinsa ya auke. Da sauri ta arasa ta ebi najasar jikinsu ta isa bakin rijiyar da tun da take shiga cikin turakar ba ta ta a taka wurin ba, wata irin ku a ta fara ji a cikin kunnuwanta ga wata 'yar juwa-juwa da take ji sama-sama. A haka ta samu ta zuba najasar a kan rijiyar take murfinta ya bu e, wata ba ura ta turnu e ta. Sai daga baya komai ya washe, ganin haka ya sa Fulani Umaima ta koma ta janyo hannun Baiwa Maimuna sai da suka je bakin rijiyar Fulani Umaima ta furta. "Maza ki shiga rijiyar nan da afar hagu." Ba musu Maimuna ta aga afarta ta zura cikin rijiyar ta zauna a kan wani mulmulallan ba in dutse. Kamar yadda Bamaguje ya gaya mata Maimuna na gama shiga murfin ya taso da kansa ya rufe ruf. Ta koma can gefen Sarki Abdul'aziz ta kwanta tamkar da ita Takawa ya gama mu'amala. Bayan an wani lokaci Mai martaba ya fara motsawa, jin haka ya sa Fulani Umaima ta fara sauke ajiyar zuciyata tana rarumo shi cikin kissa da kisisina. Wani irin nauyi dum! Kansa yake yi masa don haka ya gagara tunano abin da ya faru a baya, ganin yanayin da suke ciki ya sa ya sakar mata ajiyar zuciya ya yun ura suka wuce ban aki don tsaface jikinsu. Irin rawar jikin da yake yi a kanta ne ya sake tabbata mata da tabbas al aluman tsafin Bamaguje ba su zube a asa banza ba, ta ci gaba da narke masa tana cin karenta babu babbaka. Daren ranar a sashen Sarki Abdul'aziz ta arashe shi har zuwa wayewar gari. Cikin abin da bai fi wuni biyu ba, maganar haihuwar Fulani ta ya u cikin da wajen Masarautar Huddam, musamman da ya kasance an san Takawa ba shi da a namiji sai a wannan lokacin. Manyan mutane da masu ku i haka suka dinga zuwa suna bada gaisuwa ha e da yi masa barka da samun aruwa, mafi yawa daga cikinsu har da sha tara ta arzi i suke kawowa. Duk da Fulani Umaima ta san jaririn a nakashe yake hakan bai hana ta jin yashi, ba in ciki da unci a kan kyaututtukan da Fulani Babba take samu ba. A lokacin sai ta tsiri kwanciya da tsirfar ciye-ciye wani lokacin har amai take alowa a turakar Mai martaba, duk da cikin jikinta babu abin da yake saka ta. Ganin haka ya aga hankalin Takawa har ya aikata sashen magunguna aka kira masa Ungozoma da jikar Baushe don su duba ta su ba ta magani. Tashin farko aka sanar wa da Sarki cikin da ke jikin Fulani Umaima, farin ciki kamar zai zuba ruwa a asa ya sha. Ita kuwa Fulani Umaima ko ka an ba ta nuna wa Takawa ta san da cikin jikinta ba, nan ta shiga gwalangwaso da fele e wani lokaci hatta amshin Turakarsa ce wa take ba ta so. Cikin wannan yanayin aka ebi kwanaki mai jego tana angarenta tana jego ita kuma Fulani Umaima tana rainon cikinta, gaba aya gidan sarautar ya zagaye da ananan maganganu. Jin labarin cikin Fulani Umaima da Fulani Babba ta yi ba aramin faranta ranta ya yi ba, kuma rashin ganinta kwana biyu a angarenta ko ka an bai dame ta ba don ta san yadda laulayin ciki yake ba shi da da i. A angare aya Fulani Babba na cikin matsanancin tashin hankali sakamakon yadda fitsarin da yake zuba daga jikinta yake sake ta'azzara, tun tana oyewa har ya zamana sai da Baiwa Zainaba ta fahimci halin da take ciki, ga shi abin kullin gaba yake yi da ta kwanta ko bacci minti biyar ba ta yi tana farkawa sai dai ta ji ta sharkaf da fitsari, ga kuma jinin bi i duk shimfi arta ta ha u ta dagule. Ana gobe suna da asuba bayan ta tashi ta sake ganin wurin ya yi sharkaf da wani irin zarnin da ke tashi har ya wuce misali. A wannan lokacin take zuciyarta ta karye ganin lalurar tata a kullin gaba take yi ba baya ba, a daidai lokacin yayarta da suka zo daga Masarautar Bassar ta shiga akin, ganin ta a zaune ya sa ta an yamutsa fuska. "Fatima wai mene ne yake wari ne?" Da yake mai shirin kuka ne aka jefe shi da kashi awaki take Fulani Babba ta fashe da matsanancin kuka, da mamaki Halima ta furta, "Fatima me yake faruwa ne?" Sai da ta yi mai isarta sannan ta mi e tana nuna wa yayarta ta ce. "Ki duba ki gani Yaya Halima wai ni ce yau nake malala fitsarin kwance. Ni dai na fi zargin tun ranar na haihu na ha u da wannan iftila'in, duk yadda zan yi takatsantsan ina runtse idona duk gajarta bacci sai dai na tsinci kaina a cikin fitsari." Jakadiya da ta zuro kanta da niyyar sanar da Fulani Babba ruwan wankanta ya yi
Chapter 9 · 0% Book details