← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 89

Sashe 64

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da Hussaini. Na san za ka yi mamaki Sarki Abdul'aziz amma ba abin mamaki ba ne idan ka yi la'akari da sunana Boka Bamaguje kuma mahaifin matarka, wata ila ka aryata kalamaina amma shi Maharaz zai iya tabbatar maka idan ma arya nake ko kuma gaskiya nake fa a maka." Zumbur Kamalu ya mi e tsaye yana kallon Bamaguje da Dattijo Maharaz bakinsa sai motsi yake amma ya gagara furta koda kalma aya ce. "Zauna Kamalu!" Dattijo Maharaz ya furta a ta aice, bayan Kamalu ya zauna ya ci gaba da ce wa. "Na fahimci yanayin da kake ciki Kamalu, Sarki Abdul'aziz ka tura yanzun nan aje a kira maka Baiwa Inna wuro da Baffajo a sashen Bayi. Wata ila ganin iyayen da Kamalu ya saba da su ya sa shi samun nutsuwa har ya fahimci duk abin da ake tattaunawa." Nan take Sarki Abdul'aziz ya aika Yariman Muhsin don ya kira Dogari an'Sani da ke can bakin ofa, da fitar Muhsin babu jimawa sai ga Dogari an'San ya shigo. aga lalubensa ke da wuya idanunsa suka sauka a kan Kamalu da ke zaune shiru hawaye na zuba. "A je a sanar da Jakadiya ta yi gaggauta kawo mana Baiwa Inna wuro da Baffajo." Cikin girmamawa ya amsa sannan ya fice daga akin. Shugaba Zurufu na sauke kansa zai fara karatun littafin ya ji giftawar abu a bayansa, an waigawa ya yi amma bai ga komai ba. Daga can arshen bango Fargi ce a tsaye ta har e hannuwanta ta zuba masa idanu, Shugaba Zurufu ganin bai ga komai ya sa ya sake mayar da kansa sannan ya bu e shafin baya na littafin. Ga mamakinsa sai ya ga shafukan baya duk sun shafe, guntun tsaki yaki ya saki ya girgiza kansa a fili ya furta. "Lallai Shaddas ka cika hatsabibi!" Daga daidai wurin da Boka Shaddas ya tsaya a karatu Shugaba Zurufu ya bu e ya fara karantawa. "Kin san wace ce masoyiyar an autan Darri?" Sarki Hafiz ya sake furzo mini tambayar don ina tsamani ya zaci ban ji tambayarsa da farko ba. Girgiza masa kai na yi sannan na ji ya ci gaba da cewa. "Sarauniya Hazima! Awancan lokacin ita ta sace zuciyarsa, don a yadda aka ba ni labari an autan Darri ya kasance mai son matan tsiya. Kwatsam sai mahaifiyarki ta wayi gari da jin labarin an autan Darri ya dam a wa Sarauniya Hazima karagar da ta dam a masa, a yadda kakana ya ba ni labari kuma an yi hakan babu jimawa a tsokane-tsokanensa ya ta o 'Yar wani malami da ke asar Saudiyya, babu jimawa mahaifin yarinyar ya one shi urmus don an ce an kai ruwa rana da shi a kan ya fita daga jikinta ya i. A wancan lokacin an ce wannaan labarin ya ka a mahaifiyarki matu a na rashin masoyinta, a angare aya kuma ta fa a kogin nadamar dam a masa karagar mulkin da ya bayar da ita zuwa wani gidan. Sarauniya Hazima ta shimfi a mulkinta cikin aminci da salama, hakan ne ma ya an rage ra in da ke cikin zuciyoyin mahaifanki. Kuma tun da wannan karagar ta koma hannun Sarauniya Hazima sai da ta shekara sama da ashirin sannan ta yi murabus ta dam a wa babban anta mai suna Sarki Bilal. Tun da Sarautar gidanku ta koma gidan Sarauniya Hazima ba ta sake fita ba har zuwa kaina ni Sarki Hafiz da nake ba ki wannan labarin, akwai sarakuna da dama da aka yi a cikin Masarautar nan wasu sun auki shekaru a kan mulki wasu kuma ba su da e ba, a cikin kundin tarihi ma na ji an ce akwai sarkin da kwana aya tal ya yi a kan mulkin Allah ya yi masa rasuwa. Kin san dalili?" Na riski tambayarsa. "Ban sani ba Sarki Hafiz." Na amsa masa a ta aice don na agu ya are labarin da yake ba ni ko na ji ina labarin iyayena da saurn zuri'ata suke. "Saboda yadda masarautar nan ta auki tsafi da muhimmanci domin cim ma manufar duk wani mai neman udurin hayewa sarauta. Ke ba iya gidan nan ba, zan iya bugar irji na ce miki a duk fa in nahiyar nan babu wata masarauta da ba sa amfani da tsafi da sihiri, sai dai kin san a komai ba duka a ka zama aya ba amma mafi rinjaye a kan doron haka ake." Kalamansa sun matu ar ba ni mamaki, ina shirin wurga masa tambaya ya katse ni. "Idan har kin fahimci labarin da na ba ki kin ga asalin sarautar gidan nan ta fito daga gidanku ne, sannan ta fa o hannun zuri'armu. Amma kin san ya aka yi aka san da cewar ke ce za ki dawo ki kar i kambun sarautarku?" Da sauri na ago na furta masa. "Ina sauraronka sai ka fa a Sarki Hafiz." Takun tafiyar da Shugaba Zurufu ya ji a bayansa ne ya sa ya yi saurin rufe littafin ya rungume shi a irjinsa ya waiga da sauri, a jikin bangon dutsensa ya ga an yi rubutu da ajami cikin manyan ba i an saka. "FARGI." A fili ya maimaita sunan nan take gabansa ya yanke ya fa i, da sauri ya arasa bakin atuwar wutar tsafinsa da ke ci balbal sai da ya saki dariyar mugunta sannan ya wurga littafin ciki. Bayan Fargi ta koma cikin dajinsu ware kanta ta yi a cikin bukkarsu ita ka ai take sakin murmushi, wani irin farinciki take ji a ranta sai dai kuma ta ci alwashin bin duk wata hanya ta toshe arakar da duk wani daga cikin zuri'arsu zai iya kawo mata dangane da ala arta da Sarki Sulaiman, musamman Shugaba Zurufu da take ganin take-takensa na nuna mama hassada a duk lamuranta. Ba mahaifianta ba hatta sauran mutanen zuri'ar Rumzu sai da suka fahimci farincikin da take ciki don haka a ranar ta yi shelar yin aikin sihiri da tsafi kyauta ga duk wanda yake da wata matsala, kuma hatta su kansu Aljanun da suke tayata aiki sai da ta gwangwaje su da tukwicin da take yi musu a duk lokacin da za su taya ta aiki. Kwana biyu a tsakani ba ta ga Sulaiman ba; ba ta ji motsinsa ba hakan ya sa ta shiga matsananciyar damuwa a tunaninta yana can wurin amaransa yana shan amarci don haka wani tu in haushi da acin rai ya mamaye ta. Tana zaune a bakin wata atuwar bishiyar tsamiya, hawaye ya shiga gangaro mata. Daga samanta ta hangi inuwar mutum tana agowa karaf idanunsu suka ha u wuri aya. "Me ya sa ake mini asara hawaye?" "Saboda mamallakinsa ya yi watsi da shi." "In ji wa?" "Zuciyata ce ta sanar da ni." Sarki Sulaiman ya saki murmushi. "Zuciyarki ba ta gaya miki gaskiya ba." Juyar da kanta gefe ta yi ya zagaya ya tsugunna a gabanta. "Kwana biyu kin ji ni shiru ko ki tuntu i lafiya Fargi." Wani abu ta ji ya soki zuciyarta sai da ta ha iyi yawu mai aci ta ce. "Saboda ba na son shiga hurumin matanka." Ya fahimci kalamanta cike suke da kishi, sai da ya yi murmushi a fakaice ya ru o hannunta. A sanyaye take bin sa da kallo, ta ji ya ce. "Na zo tafiya da matata." Rass! Gabanta ya fa i, bai jira cewarta ba ya arasa da ita wurin dokinsa, ilahirin jikinta ban da karkarwa babu abin da yake yi. Ya fahimci tsoronta a fili amma sai ya yi tamkar bai son tana yi ba, sai da ta zauna sosai sannan ya hau suka fara tafiya. Sun kusa fita cikin gari Sulaiman ya shafi saman kan dokin da suke kai take suka ace, zuciyarsa fes don a yadda mahaifansa suk matsa masa a kan iyalinsa alwashi ya ci ba zai fara sanin kowacce macce a duniya ba sai Fargi domin ita ce za insa. Bawa an Sani har aki ya arasa ya sanar da Jakadiya a lokacin ta dawo daga binne tsokar da Shugaba ya ba ta babu jimawa, ko da Bawa an Sani ya sanar da ita sa on Takawa ba ta kawo komai a ranta ba, har za ta wuce Bawa an Sani ya yi asa da murya sannan ya sanar da ita ganin idanunsa biyu ya ga Kamalu a turakar Sarki Abdul'aziz. Jakadiya tana isa akin Inna wuro ta same su suna zaune suna 'yar hira ita da Mai gado da Jawahir, sai da ta sanar da ita sa on Takawa bayan sun fito Jakadiya ta an tsegunta mata ganin Kamalu da Bawa an Sani ya ce mata ya yi, amma da shara in idan da gaske ne za ta ba ta tukwici, cikin farinciki Inna wuro ta amince ta le a ta gaya wa Mai gado sa on farincikin da ta ji a wurin Jakadiya, ta yi maganar tana yin asa da murya. Sun nufi hanyar fita daga sashen Bayi suka ha u da Baffajo a nan suka sanar da shi sa on Takawa, gaba aya suka nifi hanyar sashen Mai martaba ta bayanta Jakadiya ta ji ance. "Jakadiya zan biyo ku." Muryar Basiru ta ji, nan take gabanta ya fa i da ta tuna Shugaba ya ce mata zai turo aljani a surarsa, amma gudun kada wani ya fahimci lagonta ta wayance da cewar. "Mu je mana ranka shi da e Basiru dama ai wurin Takawa za mu je." Jawahir da ke la e a bayansu sai da ta ga sun wuce sannan ita ma ta rufa musu baya. Da sallama gaba aya suka shiga cikin akin jikin Inna wuro sai rawa yake tana fargabar abin da za su tarar, Jakadiya ta yi turus tana kallon mutanen da ke cikin akin. "Fa uwa ta yi daidai da zama Maharaz! Ina bu atar sa bakin Jakadiya akan aryatawar da Umaima take mini dangane da aikin yaron nan da na yi Abubakar." Boka Bamaguje ya yi maganar yana nuna Jakadiya. Jawahir na zuro kanta cikin akin kanta ta ji ya yi wata irin sarawa, juya ta fara aukanta. Wani irin luuu ta ji tamkar ana fisgarta, "Ki bu e rijiyar uwar akin nan domin wannan aikinki ne. Dalilin haka ya sa tun farko ban ago zancanta ba tun da ba hurumina ba
Chapter 64 · 0% Book details