← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 89

Sashe 16

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga aukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye. *Masu orafe- orafe ta pc da groups zan rage 100 daga yau zuwa ranar da zan gama free pages. Free pages za su are a page a 10 daga yanzu zuwa ranar duk mai son karanta littafin za ta turo 400* SHAFI NA TAKWAS RIGAR AR A gajiye tu us suka dawo gida sakamakon yawon kiwon da suka je cikin dokar daji, zamansu babu wuya wata farar dattijuwa ta auko orai guda biyu sai da ta fara zuba nono a cikinsu ta mi a wa mai gidanta Baffajo. Ta jima a tsugunne tana jiran ya kar a tana agowa ta lura da yadda ya dulmiya cikin kogin tunani, a sanyaye ta kai hannu ta ta a shi. "Yanzu Baffajo ba za ka daina wannan tunanin ba? Idan kai kana yi ni kuma sai a?" Ajiyar zuciya ya sauke. "Inna wuro aradun Allah lamarin yaron nan ara ci mini tuwo a warya yake, yanzu a ce an mutum ba shi da abokan rayuwa sai gidan tururuwa da dokar daji? An ya Inna wuro ba za mu kai Kamalu wurin Malamijon farar riga ba?" Inna wuro ta yi jim cike da damuwa sanna ta furta, "Eh to hakan ma wani abu ne amma ni sai na ga kamar har da sabon shiga dawa..." "Kayya mu ba a dawa muka yi rayuwa tun daga uruciya ba? Kin manta a lokacin baya tsakiyar dare nake tsintoshi a bayan rumfar can wurin shurin da ke gabas da shi." Kamalu ya ago fuska a ha e don jin abin da Iyayensa suke furtawa, motsa baki yake kamar wanda zai yi magana, amma sai ya gimtse ya kawar da kai gefe. "Kamalu kai fa ba yaro ba ne a alla shekarunka sun haure goma, mahaifinku girma ya kama shi ba ka ganin sauran 'yan uwanka ba haka suke ba." Kamalu ya sunkuyar da kai asa ba tare da ya kalle su ba, A'iru da ke gefe ta furta. "Kwarankwasa dubu rannan har gani na yi yana ibar wani abu a kan gidan tururuwa yana sha, dubi wancan zobe." A'iru ta yi maganar tana nuna hannun Kamalu mai auke da wani zoben azurfa mai auke da wani irin zane. "Da bakinsa ya ce mini tsintarsa ya yi a kan shuri wai gadon Masarautarsu ne." A razane su Inna wuro suka dube shi, Baffajo ya ce. "Kamalu wa ya ba ka wannan zoben?" "Tsintarsa na yi." Kamalu ya furta kai tsaye ba tare da ago ya kalle su ba. Haushi ya fara kama Baffajo don haka ya ce, "Kai Kamalu hai ka shiga taitayinka, ba ka san dawa ba ko?" Kafin Kamalu ta ya ba shi amsa daga sama suka fara jin gudun dawakai da iface-ifacen mutane, kafin su yi wani yun uri tuni wa ansu Dogarai da sojojin masarauta suka farmusu cikin shammata suka ri a ta e su suna aure su da wasu murtuka-murtukan igiyoyi a jikin manyan itatuwa. Lokaci aya garin ya hautsine ban da ura babu abin da yake tashi, wa anda suke da rabon tsira tuni suka shu a daji. Wa anda aka riga da aka rubuta zanen addararsu kuma tuni aka dam e su, a cikin wa anda suka tsira har da Salele an gida Baffajo. Shi kuwa Kamalu ko da ya ga abin da yake faruwa ko gezau bai yi ba, yana nan zaune wani Dogari ya isa gare shi ya fisgo shi da niyyar ta e shi, ayan hannun nasa ya sa ya bigi gefen hannun Dogari, wata irin azaba ya ji tamkar an zuba masa ruwan dalma. Da kansa ya arasa wurin wasu Dogarawa da ke tsaitsaye suna aure ragowar mutanen da aka kama wanda ko tantama babu sun riga da sun zama bayi. Sai da aka aure Baffajo da wa ansu mutane biyu sannan aka aure Kamalu, a angaren mata kuma tuni aka aure Inna wuro da sauran mutanen da ke cikin rigar. Kafin wani lokaci rigar ta yi fayau sai kukan dabbobi da ananan tsuntsaye da ke tashi. AUYEN GANGARE Jiki a matu ar sanyaye suka arasa cikin auyen gangare hannun Mai gado auke da jaririya, tun daga ofar gari aka fara jefa musu tambayoyin inda suka samu jaririya sabuwar haihuwa. Sai dai amsa aya suke bayarwa tsintarta suka yi a cikin gona, da haka suka samu suka arasa gida. Da zuwansu babu jimawa gidansu ya cika ma il da mutane, wasu na taya su murna ya yin da wasu suka fara tsegungumi da ananan maganganu. Wani tunani Umaru ya yi take ya sa Mai gado ta auki jaririya har ta ora ruwan da za ta yi mata wanka ya dakatar da ita kai tsaye suka wuce gaba aya wurin Mai gari. Umaru yana zuwa fadar Mai gari ya zube ya kwashi gaisuwa sannan ya gabatar da jaririyar hannunsu da mahaifiyarta ta yi mata la abi da Jawahir, bayan ya tsahirta ya kar e ta daga hannun Mai gado ya mi a wa Mai gari, san ira yana ra e a gefensa. Tun da aka ago jaririyar Malam Malmo ya zura mata idanu ko iftawa ba ya ni, wannan ya haddasa fargaba da tashin hankali a zuciyoyin Mai gado da Umaru, sakamakon sanin Malam Malmo sarai da mugun aikinsa. A sakaye Umaru ya an yi gyaran murya ya furta. "Allah shi ba ka yawan rai yanzu haka Mai gado ta ora mata ruwan wankan da za a yi mata wanka da shi." Mai gari ya jinjina kai tare da yi musu nasiha a kan su ri e ta da ri on amana. Su Umaru har sun mi e bayan mutane sun watse yana waigawa ya ga Malam Malmo yana yi wa Mai gari ra a a kunne, haka kawai ya ji zuciyarsa ba ta aminta da wannan ra ar da yake yi wa Mai gari ba. Tsawar da san ira ya yi masa ce ta sa shi zura takalman fatarsa ya yi gaba jiki a sanyaye kamar kazar da aka watsawa gishiri. "Mai gado ina tsoron Malam Malmo a kan yarinyar nan kada fa a ce ya gano wani al'amari game da ita." Umaru ya fa a bayan Mai gado ta yi wa Jawahir wanka tana shafe mata jiki da mai. "Ni kaina ina tsoro amma In shaa Allah babu abin da zai faru sai alkhairi." Wannan awarin gwiwar da ya samu daga wurin Mai gado ya sa ya tashi ya fita don tatso wa Jawahir nonon akuyar da za a shayar da ita. Sannu a hankali suka ci gaba da rainon ta, tun suna ari- ari da ita har suka saki jikinsu sakamakon babu wani abu da suke gani na ban tsoro a tattare da ita. A angare aya kuma wata irin soyayya suke nuna mata, ga shi sai ta wuni ba a ji kukanta ba idan ba yunwa take ji ba. Abu aya ne ya fara damun Mai gado da yake faruwa da Jawahir cikin dare, duk lokacin da ta farka don ta ba ta nonon akuya da dare sai ta ga wani ba in jini ya tsattsafo a goshinta, idan kamar bacci ya auke ta har asuba ta yi, sai da ga goshin na ta ya yi an duhu amma babu jinin a jiki, zuwa wayewar gari kuma sai ta nemi komai ta rasa jinin ya washe. Tun tana barin maganar a ranta har ta ta a tashin Umaru ta sanar da shi, shi kansa ya yi mamaki amma gudun kada ilu ta ja bau! Ya ce su zuba wa sarautar Allan ido tun da ba ta kuka wata ila abin ya mata ciwo. Kwanan Jawahir goma Mai gari ya aika a kira masa Umaru, tun da Umaru ya ji kiran Mai gari gabansa ya fa i har sai da Mai gado ta arfafa masa gwiwa sannan ya nufi gidan Mai gari cikin wasuwasi. Yana zuwa aka yi masa iso har cikin shagonsa da yake hutawa a soro, ganin Malam Malmo ya sake tsinka zuciyarsa. Dole anwar na i ya zuba wa fuskarsa murmushin ya e cike da girmamawa ya gaishe su. "Umaru ka sani a gaban Mai gari kake don haka muke son duk maganar da muka tambaye ka ta zama gaskiyarka za ka fa a. Wace ce yarinyar da ka zo da ita kuma a ina ka same ta?" Malam Malmo ya jefa masa tambaya. "Allah ya baka yawan rai wallahi tsintarta muka yi..." "Idan tsintarta kuka yi ina mahaifiyarta? Ko kuna nufin jaririya anyar haihuwa za ta kawo kanta ne?" Mai gari ya katse Umaru. Shiru Umaru ya yi yana tsoron kada ya ba da kai bori ya hau, yana cikin nazari ya tsinci kalaman Malam Malmo. "Sanin kanka ne Umaru duk yankin nan babu wanda ya kai ni sanin sirrin tsafi da sihiri, na bincika kuma na gano wa ansu bayanai tun ranar da na ora wayar idona a kan yarinyar nan. A zahiri ne kuke ganinta anuwa amma a ba ini basarakiya ce, shu'uma ce kuma tana auke da rikitattun al'amura. Ita ba kamar kowa ba ce dalilin da ya sa mahafiyarta ta yo gudun fanfalaki da ita kenan daga cikin danginta, mukuma a angarenmu na masu aikin tsubbace-tsubbace wannan yarinyar ta kasance tamkar taki ce da ke farfa o da shukar da ke cikin gona. Ya zama wajibi ka mallaka mana ita domin cikar muradinmu, a zahiri Mai gari zai kar i ri onta ta koma gidansa da zama. A ba ini kuma zan aiwatar da aikin da za ta kasance a ashin ikona. Shara i na biyu ya zama dole ka nuna mini daidai wurin da gawar mahaifiyar yarinyar nan take, idan ba haka ba wallahi sai na shayar da kai ruwan mamaki." Gumin da ya shiga keto wa Umaru ne ya banka a sirrin da ke cikin zuciyarsa, cikin matsanancin tsoro ya ago jiki na rawa ya furta. "Duk abin da kuka bu ata haka za a yi ranka shi da e, da kai da kaya duka mallakar wuya ne." Malam Malmo ya saki murmushi cikin jin da i don ya ga tsoro malale a saman fuskar Umaru don haka ya furta.
Chapter 16 · 0% Book details