Sashe 84
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ce don haka abar bauta ta nemar wa 'yarta shahara da gawurtar da za ta ci gaba da amfana da ita. A daidai lokacin da ta cika shekara goma sha bakwai kuma za ta zama sadaukarwa ce ba sai na fayyace hukuncin da abar bauta za ta aiwatar a kanta ba. Ko ma dai mene ne Fargi ta tafka babban kuskure a baya, a tsammaninta abar bauta za ta yale ta ne bayan ta auri an wata zuri'ar da ba tata ba? Kwantan auna kawai ta yi mata don haka wannan shi ne hukuncinta a fakaice. Tun da aka kafa asar nan babu wanda ya ta a aikata mummunan zunubi kamar wanda ta aikata, ka ga kuwa dole ne a tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Saboda ko mutuwar Fargi ma da tafukan hannuwana na hallakata, na so hallaka 'yarta sai abar bauta ta hana ni domin muna bu atar rayuwarta." *SHU'UMAR MASARAUTA* *44* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Basiru na fita daga Masarautar Huddan kai tsaye wata ma abarta ya nufa da take bayan garin, ya jima a labe yana dube-dube don kada wani ya gan shi a lokacin da zai shiga cikinta, don shara in aikin ba a yin tsafin ata idan za a shiga cikin ma abarta a gudanar da abin da za a yi, sai dai mutum ya shiga da suffarsa ta ainihi. Ta bayan katanga ya haura sai da ya duba sababbun aburbura sannan ya isa bakin wani sabon kabari, ya saka hannunsa na hagu ya fara walarsa da sauri har sai da ya ji ya fara ta o mamacin da yake ciki, gashin Fulani Umaima ya an dam a da hannunsa ya zura cikin kabarin sannan ya ha a da likkafanin gawar, ya zuba asar a cikin sauran gashin Fulani Umaima sannan ya yanki likkafanin ya ha a, ya arasa mayar da sauran asar wurin cikin kabarin sannan ya mi e ya fice daga cikin ma abarta. Kafin ya arasa kogon tsafin mahaifinsa sai da ebi asar wani murgujejen shuri sannan ya ha a da ta gidan tururuwa ya ha e su gaba aya. "Na gama tsorata da lamarin yaron nan Aljani Duggu kuma jikina ya jima yana ba ni Basiru zai iya zama silar ajalina. Shugaba Zurufu ya shammace ni domin ya ci amanar ajiyar da na ba shi, ya sake asar wa yaron nan da zuciya ka taimake ni a bisa taimakon da ka saba yi mini ya kai madogarata." Boka Shaddas ya yi maganar tamkar zai fashe da kuka saboda tashin hankali. "Amma kuma ka kusa ka makara Boka Shaddas! Bakin al alamin ya kusa bushewa don Shugaba ya gama horar da zuciyar Basiru, a hatsabibanci da rashin imani ya dame ka ya shanye, sai dai a yanzu ma ba za mu rasa taimakon da za mu yi maka ba." Aljani Duggu ya furta. "Babban taimakon da nake son ka yi mini Aljani Duggu ka kashe mini Basiru, ka kashe mini yaron nan kawai ko hankalina zai kwanta..." Kalaman Boka Shaddas suka katse sakamakon ganin Basiru ya dira cikin kogon dutsen, Murya na rawa ya yi wa Aljani Duggu sallama ya juya wurin Basiru ganin yana sakar masa murmushi. "Basiru har ka dawo?" Boka Shaddas ya yi maganar yana murmushin ya e zuciyarsa na bugawa. "Na dawo gawurtaccan Boka mai shinfi an tarihi." Basiru ya ba shi amsa yana sakin murmushi. "Dalilin da ya sa ka ganni na fita babu shiri saboda wani aiki da na saka a gaba kuma a daren yau ake bu atar ganin kammaluwarsa, amma yanzu komai ya zo arshe tun da na ha o duka kayan aikin." "Amma da ka yi magana ai da na sa Aljanun da ke yi mana aiki sun ebo maka." Boka Shaddas ya furta murya a sake don ya ga alamar tamkar Basirun bai ji tattaunawar da suke yi shi da Aljani Duggu a lokacin da ya shiga cikin kogon dutse ba. "A yau ba sai gobe ba za ka yi bankwana da duniya, kafin kasa a kashe ni dama tuni ni na uduri aniyar hallaka ka har lahira." Basiru ya yi maganar a zuciyarsa, amma a fili sai ya saki murmushi ya ce. "Rashin dabarar da ban yi ba kenan." Yana gama maganar ya isa bakin wasu ajiyayyun wara gwal da ke tsaye ragowar naman jikinsu yana ci gaba da zagwanyewa, Zama ya yi a gabansa ya fara ciro kayan aikin da ya samo, ya ci gaba da jan mahaifinsa da hira. Tsafatacciyar askar da ke hannunsa a ciro ya soka a tsakiyar ma ogaron aya daga cikin warangwal in, take jikinsa ya fara wata irin karkarwa, sai da ya auki lokaci a haka sannan ya zaro ta daga jikinsa, ta yi wani irin jawur tana aukan ido. "Irin azababban tsafin da yaron nan yake shirin yi sai fa ta kai ma ura nake yin irinsa, shin har da irinsa dama Shugaba ya koya masa?" Boka Shaddas ya tambayi zuciyarsa irjinsa na bugawa, ya sauke ajiyar zuciya a hankali sannan ya ce. "Basiru wa za ka gudanarwa da aikin nan? Tabbas kowaye zai ana azaba mafi girma kuma zai fuskanci bala'i mara yankewa." Murmushi Basiru ya yi sai da ya tsoma askar a cikin wani ruwan tsafi mai kama da man uli sannan ya furta. "Mai shirin cim ma buri! Domin ya samu biyan bu atar da a kullin mafarkinsa kenan." Boka Shaddas ya maimaita kalaman Basiru ba tare da ya fahimci wurin da magaanrsa ta dosa ba. Mi ewa ya yi yana an jujjuya askar ya kwashi asar kabari da sauran kayan da ya ha o ya zuba a cikin wannan ruwan, ya auka ya fara tafiya a ahankali ruwan na ta za ala. Tun da ya fara tafiya gaban Boka Shaddas yake fa uwa har sai da ya ga Basiru ya wuce wurinsa sannan ya runtse idonsa yana sauke ajiyar zuciya. Cikin Shammata Basiru ya juyo ya kwara masa wannan farin ruwan tsafin a kan Boka Shaddas, matsawa ya yi can gefe ya ga yadda mahaifin nasa ya kwarara ihu cikin azaba. Jikinsa ne ya fara amewa, fatarsa ta fara zagwanyewa ganin haka ya sa Basiru ya arasa wurinsa da wu ar, ya kai ta goshin Boka Shaddas sannan ya furta. "Ka yi ha uri da wannan hukuncin da na yanke a kansa domin na jima da mafarkin samun kaina a wannan matsayin da kake kai, mutuwarka aukakata ce don haka ba zan iya ci gaba da hangen aukakata daga nesa ba. Ba iya kai ba, ita ma mahaifiyata akwai aikin da zan sadaukar da ita, ko kuma na aiwatar da wani aikin a kanta, wanda shi ne silar aukakar da zan ci gaba da samu har arshen rayuwata." A galabaice Boka Shaddas ya ago ya dubi Basiru hawaye ya fara gangarowa daga andararrun idanunsa da suka fara andarewa. Can jikin warangwal in da ke tsaye ya nuna ya furta, "Koma can ka dawwama a haka." Tun bai rufe baki ba gangar jikin Boka Shaddas ta ja shi jikin warangwal in da ke jere wa anda ba su da adadi. Tsafatacciyar askar hannunsa ya auko ya nufi wurin da mahaifinsa yake tsaye, ya arasa ya soka masa askar a ma ogaronsa. Yana soka masa ita tuni jikinsa ya farar karkarwa naman jikinsa ya fara zagwanyewa yana zuba a asa, sai da ya ga numfashin mahaifinsa ya auke sannan ya zare askar ya mayar da ita wurin da take. Sannu a hankali cikin Fargi ya ci gaba da girma har ya kai watanni tara, a madadin ta an murje ta ciko sai ya zamana wata irin rama take yi saboda tashin hankali. Musamman wa ansu irin munanan mafarkai da take yawan yi a wannan lokacin, ta so sanar da mahaifiyarta halin da take ciki amma gudun tashin hankalinta ya sa ta ja bakinta ta yi shiru. Tun wayewar garin ranar ta tashi da an ciwon baya da mara sama, amma da yake bai yi mata tsanani ba sai take ta gudanar da al'amuranta. Tana nan zaune sa on kiran Shugaba ya je mata, haka kawai ta ji gabanta na fa uwa zuciyarta ta fara sa a mata miyagun zantuka a ranta. Da arfafa gwiwar mahaifiyarta ta samu damar fita ta nufi kogon tsafinsa, kafin ta arasa ta hangi mahaifinta zaune a bakin bishiya da alama hutawa yake. Har za ta gifta shi sai zuciyarta ta fisge ta zuwa wurinsa don haka ta arasa ta zauna a gefensa. "Na tafka maka babban kuskure da laifi mai girma mahaifina. Amma ina mai neman afuwa da yafiyarka don girman tsafi da sihirin da ka gada a wurin mahaifiyarka ka yi ha uri ka yafe mini." Ta tsinci kanta da furta masa haka, don haka kawai take ji a jikinta wani mummunan al'amari na iya faruwa da ita, sai da ta saka mahaifinta ya yi mata al awarin ba zai hukuntata ko azabatar da ita b sannan ta fayyace masa duk abin da yake tsakaninta da Sarki Sulaimanu har zuwa cikin jikinta. "Amma Shugaba ya san da wannan maganar?" Mahaifinta ya wurga mata tambaya zuciyarsa na zafi, ta sanar da shi yadda suka yi da Shugaba Zurufu tun daga farko har arshe har zuwa yarjejeniya da sadaukarwar da ta yi da abar bauta. "Babban kuskuren da kika tafka kenan Fargi, tun kafin na haifi yayyanki ba ma ke ba na san waye Shugaba. Na rantse da matsayin da na ba wa tsafi a matsayin madogarata Shugaba ba zai bar ki haka ba matu ar ba ki bi abin da yake bu ata ba. Kuskure ne tun farko kika tafka shi, na sha fa a miki abin da babba ya hango yaro ko ya hau dutsen dala ba zai gano shi ba." "Ka gafarce ni mahaifina." Ta furta cikin kuka da tashin hankalin ganin fushin mahaifinta. "Duk rintsi ni mahaifinki ne Fargi, a tsammanina tun da kina shirin zama mahaifiya ya kamata ki fahimci tasirin soyayyar da ke tsakanin a da mahaifi. Ba zan ta a juya miki baya ba sai dai ina tsoron abin da Shuga zai iya zartarwa, ina tsoron hukunci da zalincinsa..."