Sashe 12
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
a yana sake le en wani koren maciji da ke sa ale da wata koriyar bishiya. "A'a Malam tsakani da Allah ni kam na manta ka san sai da na ce idan za mu fito ka tuna mini." Da sauri ya ciro wata anuwar kwari da baka daga cikin ugunsa, bai cika harbi da ita ba don haka ya so Mai gado ta taho mata da farar bakar wurinta. Ya kalli macijin ha e da matsa wata laya da ke sa ale a wuyansa, ya sakar wa macijin harbi nan take ya tsire shi wani koren ruwa mai kauri ya fara fita daga jikinsa. Yana shirin mi a hannu ya ciro kibiyar daga can gefensu suka fara jiyo numfarfashi, Mai gado da sauri ta fara matsawa don tabbatar da zarginta. "Wash wayyo! Ku taimaka mini, ku kawo mini auki tsafi zai taimake ku. Tsafi zai shiga lamarinku, ku taimaka mini kada na mutu idan na mutu tsafi zai yi fushi da ku." Gaban Mai gado ya fa i ganin wata matashiyar mace mai tsohon ciki tsugunne babu kaya a jikinta, ugunta ne ka aure da ganye sai saman irjinta. Kanta da wani irin cukurku an gashi ya zubo har irjinta. "Malam zo ka ga." "Kada ki ta a komai Mai gado, har yanzu ba ki gama sanin sharrin daji ba. Wannan ba kamar sauran dajijjika ba ne, ki yi takatsantsan." Yana arasawa idanunsa suka yi tozali da matar, ta galabaita da alama na uda take duba da yadda jikinta ya aci kace-kace. Mai gado ji ta yi ba za ta iya daurewa ba don haka ta arasa ta ru o ta tana fa in. "Baiwar Allah me ya kawo ki na uda cikin dokar dajin nan?" Wani irin nishi suka ji ta yi cikin galabaita da fita hayyaci tana fa in. "Tsafi, tsafi ka dafa mini. Abin bauta ka tserar da jinina ko on ta gagara magautana, tsafi ka taimaka mini." Rufe bakinta babu jimawa suka ji ta walla ara nan take ta haifo jaririyar 'yarta mai tsananin kama da ita. Mai gado na shirin ta a jaririyar da sauri matar ta dakatar da ita, ta hanyar ture hannunta tana girgiza mata kai. "Zuri'ar RUMZU daban take da sauran al'umma, idan muka haihu tashin farko jinin wata al'umma ba ta isa ta ta a mana 'ya'ya ba har sai mun gama da 'ya'yanmu ake ta a mana su. Idan ba haka ba yanzu za ki mutu, abin bauta zai hallaka ki." Mai gado ta an zaro idanu cikin tsananin mamaki. Umaru da ya juya bayansa ya jinjina kai yana ta e baki. Hannu ta sa a ugunta ta ciro wata aramar ba ar aska ta yanke wa jaririyar cibiya, ta sa wata siririyar fata ta aure cibiyar tamau. Hannunta ta saka ta lakuto jinin da ke fita daga asanta ta shafa a saman goshin jaririyar lokaci aya jaririyar ta tsanyare da wani irin matsanancin kuka, jinin da ta lakata mata a goshi ya shiga wata irin tafarfasa a kan goshin jaririyar. Wani irin ba in jini ya fara zuba daga cikin hancin jaririyar, kunnuwanta da asanta. Mai gado tana tsaye tana kallon abin da matar take yi cikin al'ajabi da tsananin mamaki har sai da tsoro ya fara kamata. Ganin jinin ya zarce a'ida ya sa matar ta saka bakinta ta zu o shi sannan ta fesar a gefe, take ciyawar wurin ta one urmus. Ta jima tana zu e jinin jikin jaririyar tana iban jinin gabanta tana zubawa a goshinta, idan ya tafasa sai ya shige jikin jaririyar. Sai da matar ta gama ta ago ta dubi Mai gado cikin karyewar zuciyata tana fa in, "Ban san ku su waye ba, amma na tabbata daga yanayinku ku masu karamci ne kuma tsafi zai shiga lamuranku ya dafa muku..." Da sauri Umaru ya waigo ya katse ta. "Baiwar Allah mu ba mu dogara da tsafi da sihiri ba, mun dai dogara da Ubangijin sammai da assai." Jinjina kai ta yi tana murmushi ta furta. "Koma da wa kuka dogara ban damu da na sani ba, zan bar muku amanar 'yata domin na san dangina ba za su bar ni ba mutuwa zan yi, don na hangi tsinin mashin tsafin da Mahaifina ya wurgo min, idan ban dam a muku ita ba tabbas har ita za su hallaka mu. Ba a nan doron asa ba, ko ashin asa na nutse matu ar ina numfashin na tabbata zuri'ata ta Rumzu ba za su bar ni ba." A firgice suke kallonta. "Wace ce ke? Mutum ce ko aljan?" Mai gado ta wurga mata tambaya a tsorace. "Sanin matsayin hallitata ba shi ne mafita ba, domin a yanzu ba lallai ya amfane ku da komai ba. Ga amana zan bar muku ku dubi darajar abin bautarku ku ri e ta amana, na so a sanya mata suna HAIZAT amma dalilin mahaifinta ya nunke nawa don haka ya ce mini ya fi son a saka mata sunan JAWAHIR, ban san ma'anar sunan ba don ba ya daga cikin sunan zuri'ata. Sai dai na tabbata wannan sunan zai amfane ta zuwa nan gaba, idan ta isa zama budurwa ku auke zuwa bakin kowacce irin bishiyar kuka akwai ajiyar da mahaifinta ya ta a yi wanda ita za ta tono gadon da zai bayyanar da ita jininsa ce da hannunta. Wannan jaririyar ita za ta sanar da ku asalin wace ce ni har zuwa zuri'ata ta Rumzu, tun daga zubin hallita har zuwa tushenta. Na san dangina da bibiya, kafiya da matsanancin ru o duk rintsi kada ku bayyana ba kune asalin iyayenta ba matu ar za ku shiga ba on wuri ko al'umma, wata ila ta iya tsira da rayuwarta daga kaidinsu." Tana gama maganar ta ora jaririyar a kan saman wani aton gidan tururuwa, ta dam asar gidan tururuwar tana runtse idanunta ha e da furta wa ansu irin kalaman tsafi da su Mai gado ba su ta a ji ba, tana gamawa ta shafa a jikin jaririyar gaba aya, take jinin da ke saman goshin jaririyar ya ace at. Ta sunkuya saitin kunnen jaririyar tana yi mata ra a, lokaci aya jaririyar ta yi shiru tamkar wacce take sauraron kalaman mahaifiyarta. Wani irin jini ne ya alle wa mahaifiyarta amma duk da haka cike da warin gwiwa da dakiyar zuciya ta auki jaririyar ta fara takawa har zuwa bakin ramin kwarmin bishiyar kukar da ke gefenta ta ora jaririya a ciki, ta saka hannu ta dafa saman goshinta nan take suka ga ta fara wata irin jijjiga, idanunta suka firfito numfashinta ya auke rai ya yi halinsa. Daga Umaru har Mai gado kusan mutuwar tsaye suka yi saboda al'ajabi don tun da suke a duniya ba su ta a ganin makamancin irin wannan lamarin ya faru a gabansu ba. Mai gado ce ta iya motsawa ta arasa ta auki jaririyar da mamaki ta kalli Umaru jin jikin jaririyar ya yi wani irin sanyi kamar ara. "Malam yanzu ya zamu yi da wannan gawar?" Ajiyar zuciya ya sauke yana shirin yin magana suka ga gawar matar na matsawa ha e da nutsewa cikin bishiyar kukar da take jigine a jikinta. Cikin tsoro suka ja da baya suna kallo, kafin wani lokaci babu gawar babu alamarta ta nutsa cikin bishiyar kukar sai shatin jinin da ke manne a jikin bishiyar. Jiki na karkarwa Mai gado ta ajiye jaririyar a asa tana ja da baya ta furta. "Mai gida Allah ya sani ba zan iya ri on wannan abin ba, domin ba na ko tantama mahaifiyar yarinyar aljana ce ita kanta yarinyar dubi irin siddabarun da mahaifiyarta ta yi mata kafin ta mutu." Cike da gamsuwa Umaru ya ago zai yi mata magana, gabansa ne ya yanke ya fa i sakamakon mugun gamon da wayar idonsa ta yi. Da sauri ya ja hannun Mai gado suka fa i can gefe ha e da kurma ihun neman taimako. _Ummou Aslam Bint Adam_ 07062062624 *SHU'UMAR MASARAUTA*