← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 89

Sashe 58

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamalu babu alamarsa, tun suna ganin abin kamar wasa har aka shafe kwana guda ba tare da an ga Kamalu ko gawarsa ba. Tun a daren ranar zazza i mai zafi ya rufe Inna wuro da Baffajo saboda matsananciyar damuwa da suka shiga, kallo aya za ka yi musu ka fahimci suna cikin matsananciyar damuwa don ko abinci ranar ba su iya ci ba. "Wallahi ni dai na gaji da yin bauta a wurin nan haka kawai wari ya addabe ka, saboda Allah don dai shi Bawa ba shi da gata sai a ce kowanne cin kashi shi zai auka. Hanne dubi wancan zanin na Sailuba ban da ruwan mugunya da tsutsotsi babu komai a ciki." Hanne ta sauke ajiyar zuciya bayan ta gana sauraron Furaira sannan ta furta. "Wallahi gara ke Furaira nesa ba kusa ba, idan kin wanke ai shi kenan sai wani ya sake aci. Ni kina ga kullin ina tare da ita ina aikin kashe mata kwarkwata, ga uban oyin da nake sha ewa. Wallahi ni kaina na agu na sauya..." Kalaman Hanne suka katse sakamakon hango Jakadiya da ta yi a tsaye. "To tsofaffin munafukai, uban me kuke tattaunawa?" Take suka yi tsilli-tsilli cikin tashin hankali, fargabarsu aya Allah ya sa Jakadiya ba ta ji abin da suke fa a. "Babu komai Jakadiya hutawa muke." Furaira ta wayance. Jakadiya wafa ta yi sannan ta wuce wurin Sailuba da ke kance a aki ta yashe afafuwa tana shan iska. oyin da ya daki hancin Jakadiya ne ya sa ta an ja baya da sauri, gabanta ya buga dum! Da matsanancin arfi. Ta zura wa Sailuba idanu cikin tashin hankalin, Sailuba da ke kwance ta bi Jakadiya da jemammun idanunta cikin sare rai da yanke auna. "Sailuba idanuwana ne suke yi mini gizo ko da gaske haka kika sake lalacewa. Yanzu warin da ke fita daga jikinki har ya ta'azzara haka?" Sailuba ba ta tanka wa Jakadiya ba saboda tsananin takaicin da ya cunkushe ta, a duk fa in duniya gani take babu wanda ya jefa ta a wannan halin sama da mahaifiyarta. "Dama kowa ya sayi rariya ai ya san za ta zubar da ruwa Inna! Kin fi ni sanin wace ce Umaima a kan me za ki tsaya kina tambayata? Na nemar wa kaina mafita amma kin ce ba haka ba kin ga idan na mutu shi kenan kin kowa ya huta. Ita Umaima hankalinta zai kwanta ta mallaki mijinta ita ka ai, ni kuma na samu salama a rayuwata ke kuma ki huta da yawon neman magani." Sailuba ta arashe maganar walla na zuba daga idanunta. Tun da sabuwar lalurar nan ta samu Sailuba wannan ce rana ta farko ta kalamanta suka daki zuciyar Jakadiya, wata irin nadama game da auren Sailuba da Takawa ta mamaye ta. A sanyaye ta tsugunna idanunta suka ciko da wallah. "Jakadiya wannan maganin Takawa da kansa ne ya ce ki kawo mini? Amma dai na ji da i ko ba komai a wannan karon Takawa ya nuna mini kulawa. Allah ya sa idan na haife cikin nan albarkacinsa ya sa na ci gaba da samun kulawa daga gare shi." Kalaman Fulani babba na baya suka dawo wa Jakadiya ra au a cikin kunnuwanta, a lokacin da ta kai mata wani garin turare da suka ha a baki da Fulani Umaima a zuwan Sarki Abdul'aziz ne ya bayar da shi. "Allah ka gafarta wa Fulani babba, Ubangiji ka sa ta yafe mini abin da na aikata mata. Ya Allah kada ka jarabce ni da ha inta a kaina." Jakadiya ta furta zuciya a raunane. "Inna me kalamanki suke nufi? Shin kin ta a yi wa Fulani babba wani abu ne?" Ajiyar zuciya Jakadiya ta sauke sannan ta furta. "Ba huruminki ba ne Sailuba." "Ba hurumina ba ne amma ai ta silata kike neman yafiyar Ubangiji. Inna me kika aikata ne da abubuwa suka ca e mana lokaci guda. Ni fa na fara ora zargi a kanki don na tabbata ruwa ba ya tsami banza." "Zan shawarci Takawa domin na fantsama nema miki magana, ba zan zura ido na ga kin lalace a banza ba, idan ta kama ma na auke ki na mayar da ke can sashena tun da na lura idan na tsaya kallon ruwa kwa o zai iya yi mini afa." Daga haka Jakadiya ta fice daga akin zuciyarta na suya. Ta kowacce fuska abin duniya goma da ashirin ne ya mamaye zuciyar Fulani Umaima, hannuwa bibbiyu ta zauna ta rafka uban tagumi tana tuna irin rayuwar jin da i da rashin tarin matsalolin da ta yi a baya. "Ta wacce hanya zan samu damar yankar gashin kan Basiru? An ya Muhsin zai ba ni ha in kai a kan abin da nake bu ata na kai yarinyar nan wurin Shugaba kuwa?" Fulani Umaima ta watsa wa kanta tambayoyi, murmushin da ya jima bai sauka a saman fuskarta ba ne ya su uce mata da ta tuna dabarar da ta fa o mata game da Muhsin. Ta yun ura za ta mi e ta sake jin asanta ya zazzago mata, tsoro ne ya sake kamata don a kullin asanta sake zazzagowa yake yi. "Me ya sa haka? Me ya sa al'amurana suka ca e lokaci aya?" Daga can bayanta ta ji an furta. "Saboda ni ma ba ki bar ni na zauna lafiya a lokacin da nake raye ba." Ra au ta ji muryar Fulanu babba a kunnuwanta. Da sauri ta waiga a an tsorace karaf idanunta suka sauka a kan anjamammiyar mage ta zuba mata idanunta masu abin tsoro. Matsanancin tsoro ne ya sake mamaye Fulani Umaima tana shirin guduwa azabar da ke addabarta ta sa ta fa asa, tana daga zaune ta fara jan jiki a hankali magen ta ci gaba da tunkaro ta har sai da ta arasa gabanta. "Duk inda za ki je ina biye da ke Umaima!" Magen ta furta sannan ta nutse ashin asa ta ace daga wurin. Rashin samarwa kai mafita da damuwar da ta cunkushe Fulani Umaima ta sa ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya. Inna wuro ce ta fa akin a firgice jin sautin kukan Fulani Umaima. "Allah ya taimaki uwar akina ya ara wa Fulani lafiya. Ranki shi da e shi da e..." Da sauri Fulani Umaima ta katse Inna wuro. "Inna wuro muna bu atar ke ewa." Inna wuro ta fice da sauri don ita kanta har lokacin tana cikin matsananciyar damuwar rashin ganin Kamalu. Furhussam na aukan Kamalu ya fara zabga matsanancin gudu bai sauke shi a ko ina ba sai a can ungurmin dajin Buhdu, a can cikin aton wani farin dutse mai matu aukar idanu. Dajin cike yake da dogayen bishiyoyi a jajjere tamkar wani ne ya dasa su. Sai dai kallo aya idan ka yi take hantar cikinka za ta ka a sakamakon yadda suffarsu take da yanayin tsoratarwa. Dutsen a mulmule yake babu ofa ko a huda ko ka an a jikinsa, sai da ya tsaya a wurin sannan ya ora tafin hannunsa a jikin dutsen, nan take ya tsage gida biyu wani ruwa mai garai-garai ya fara ulowa daga ciki. Ta cikin ruwan Furhussam ya shiga, yana shiga dutsen ya sake ha ewa ya mulmule. Hallitu ne kala-kala a ciki wa ansu auke suke da siffar tsuntsaye kawunansu auke da aho, wa ansu kuma siffar jikin birrai gare su bayansu auke da jeluna. Duk ta hanyar da Furhussam ya wuce aya bayan aya hallitun suke zubewa asa suna gaida shi cikin wani irin sar en yare. Tafiya ya anyi ma nisa sannan ya isa tsakiyar babban filin da wata atuwar rijiya a ciki, yana bu e murfin rijiyar take wani asaitaccen gado ya bayyana. Da kansa ya ora Kamalu a kan gadon, daga angaren hagu Hullat ce tafe cikin surar tsuntsu mai an ban tsoro ita da yarta Furtuhmu, sai da suka arasa gaban gadon sannan suka riki e cikin surar bil'adam. Furtuhmu ce ta matsa gefensa cikin shau i ta sa hannu ta shafi gefen fuskarsa, a hankali Kamalu ya sauke ajiyar zuciya sannan ya bu e idanunsa. A hankali yake bin wurin da kallon mamaki, ya ura wa Furtuhmu kallo yana jin tamkar ya ta a sanin fuskarta. "Barka da hutawa." Ta furta masa a ta aice. Furhussam da ya riki e zuwa siffar da Dattijo Maharaz yake zuwar wa Kamalu ya matsa kusa da shi ya furta. "Kamalu ka farka kenan? Barka da tashi Sadauki." Sai a lokacin Kalamu ya sauke ajiyar zuciya hankalinsa ya kwanta. "Dattijo Maharaz ina ne nan ka kawo ni?" Murmushi ya sakar masa. "Kada ka aga hankalinka Kamalu nan ne wurin da za ku samu 'yancin kanku kai da iyayenka." Rufe bakinsa ke da wuya sai ga wa ansu dattijai sun araso wurinsa masu auke da siffar Inna wuro, Baffajo da A'iru. Murmushi Kamalu ya sakar musu yana sake jin karamci da aunar Dattijo Maharaz a zuciyarsa. Sarki Abdul'aziz tun da ya kwanta ban da juyi babu abin da yake yi, tunaninnika da dama suka mamaye kwanyarsa yana sake juya kalaman Dattijo Maharaz. Abubuwan da suka faru a akinsa suka ci gaba da dawo masa, a angare aya ga tagwayen larurorin matansa da suka fara ci masa tuwo a warya. "Idan Dattijo Maharaz ya warware maka zare da abawa ka ara aure." Wani tsagin na zuciyarsa ya shawarce shi. "Kada ka yi aure ka dai nema musu magani, ina ganin shi zai fi maka sau i tun da kana gani a sakacinka ka rasa matarka kuma uwar 'ya'yanka."Zuciyarsa ta sake shawartarsa. "Don Allah ranka shi da e ka nemo mini magani, ni ka ai na san irin azabar da nake ciki a kullin ji nake ana fisgar asana tamkar zai fito waje." Kalaman Fulani babba suka dawo masa cikin kunnuwansa. "Astagafirullah! Allah ka gafarta wa Fatima Ubangiji ka yafe mini akan sakacin da na yi a kanta." Sarki Abdul'aziz ya furta a fili idanunsa na cikowa da walla. Duk da ya kasance abokin 'yar tsamarta ne ba aramin jimamin atansa ta yi ba, a angare aya fargabarta ta ninku da ta tuna kusan ta silarta hakan ya faru sai dai ta gagara furta kowa har Mai gado. A duk lokacin da ta ke e ba ta da aiki sai
Chapter 58 · 0% Book details