← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 89

Sashe 50

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mata ba sai da ya koma mazauninsa na ainihi sannan ya ago ya dube ta rai a ace. "Idan na so salwantar da rayuwar Umaima abu ne mai matu ar sau i a wurina, amma tun a wancan karon sai na aga mata afa da ta sa na karya al awarin da na auka a kan yarinyar da ta ce za ta kawo mini. Na kawar da kaina ne domin hannunka ba zai ta a ru e ka yanke ba, amma a wannan ga ar tura ta kai ni bango domin a kan na rasa littafin nan gara na rasa kowa da komai domin shi ne tsanin da zai kai ni ga cin nasarar da na sa a gaba. Don Allah wannan shi ne hukuncin da ya da ce da Umaima, a kan anyan aikin da ta aikata mini. Kuma idan duk bokayan duniya za su ha u domin su tashe ta ba za su ta a iyawa ba, har sai na ga damar dawo da ita ainihin surarta. Umaima za ta zauna tamkar dutse a gabana, don haka ki tashi ki ba ni wuri." *SHU'UMAR MASARAUTA* *26* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Cikin matsanancin mamaki Sulaiman ya dubi Fargi da ke tsaye a gabansa, mamakin kalamanta ya sa ya dube ta ya furta. "Ta wacce hanya kike ganin zan iya mulkar Masarautarmu bayan Shugaba ya nuna mini alamun rashin nasara?" "Sai an gwada a kan san na warai an samari! Ya kamata ka dinga jarraba sa'arka a wurare mabambamta tun da an ce idan hagu ta i sai a koma dama." Tsoro ya mamaye shi a zuciyarsa yana tsoron kada dai yana gaban matsahiyar da yake jin ana fa in tsafi da duk wani sihiri ba ya ta a gagararta. Tamkar Fargi ta hangi abin da yake cikin zuciyarsa ta saki murmushi tana fa in, "Kada ka tsorata domin zubin surar hallita da tauraronka ba na ragwayen mazaje ba ne. Kamar yadda zuciyarka take kokonta ka shaida mata, kana gaban Fargi 'yar matsafa jikar matsafa mai ta ama da alfarmar tsafi da sihiri." Da sauri Sulaiman ya ago ya dube ta, ta sakar masa murmushi sannan ta fara takawa a hankali. Da sauri ya sha gabanta a tsorace murya na rawa ya ce. "Tuba nake Shugaba da fatan dai ban aikata wani zunubin ba?" A karo na biyu ta sakar masa murmshi sai da ta arasa ta kama tafin hannunsa ta ura masa, sannan ta dun ule hannunta ta ora a saman hannunsa ta an runtse idonta tana furta alasiman tsafi. Duk yadda Sulaiman ya so wacewa sai ya gagara don haka matsanancin tsoro ya sake mamaye shi, har sai da ya saki fitsari a tsaye saboda tashin hankalin abin da ka je ya zo. e hannunka!" Fargi ta furta masa a ta aice. Da sauri Sulaiman ya bu e hannu sai ga wani farin rawani ya bayyana a tafin hannunsa, wata zabgegegiyar takobi ta bayyana a ciki da sauri ta taso tamkar za ta tsire idonsa har sai da Sulaiman ya ja da baya. "Ka arasa masarautarku a yanzu haka Waziri da Shamaki na ulla yadda za su cutar da mahaifinku, idan ka je ka ebo wannan asar ka watsa musu su da kansu za su tona asirin kansu." Fargi ta arasa maganar tana mi a masa wani ullin magani. Jiki na karkarwa Sulaiman ya mi a hannu ya kar a, ya shiga zabga mata godiya. Fargi ta sakar masa murmushi sannan ta buga asa da afarta nan take ta ace at, ganin haka ya sa ruwan mamaki ya sake mamaye Sulaiman cikin ta'ajibi ya ka a linzamin dokinsa ya bar wurin. Duk abin da yake faruwa tsakanin Fargi da Sulaima a kan idanun shugaba, don haka gabansa ya yi mummunar fa uwa haka kawai yake jin kusancin yaron a gare su babu alheri a ciki. A allah ya shafe shakaru masu yawan gaske amma bai ta a tsintar kansa a irin wannan yanayin ba, don haka ya sauke ajiyar zuciya ya arasa bakin halwar tsafinsa ya binciki abin da zai faru tsakanin Fargi da Sulaiman a gaba. Hannuwa biyu a saman kanta cikin matsanancin tashin hankali ta fa a cikin kogon tsafinsa, kuka take har da magina tamkar wacce aka yi wa bushara da wutar Jahannama. Boka Shaddas na zaune a kan wata halitta da ke tsugunne tana lasar wani ba in jini da ke gabansa, da idanu yake bin Jakadiya har ta arasa gabansa. Yaraf ta zube a asa sannan ta sake fashewa da matsanancin kuka, har lokacin bai tanka mata ba sai ma idanu da yake bin ta da shi har sai da ta ci kukanta ta oshi. "Ya kai babban boka mai yi mini yau ya yi mini gobe, ya Boka Shaddas mai share mini hawaye gani gare ka na zo ka aura mini zanin da Umaima ta kwance mini a bakin kasuwa har jama'ar cikinta sun fara fuskantar rashin kyawun tsiraicin da ke tare da ni..." Tun daga farkon abin da Sailuba ta gaya masa game da halin da take ciki har zuwa ita kanta oyin da ta ji Sailuba na yi ta kwashe ta sanar da shi, ta arashe maganar tana fashewa da matsanancin kuka. Sai da ya lakace jinin da ke gabansa ya sha sannan ya furta. "Bakin al alami ya riga da ya bushe Jakadiya! Kin san a kance idan junanka sammako wani a tafe ya kwana, Umaima ta riga da ta cutar da Sailuba da cutar mai matu ar yawa, tun da har aka binne gawar kishiyarsu bakin al alami ya riga da ya bushe, tun kafin ki zo na san abin da ya faru don haka bincikena ya zartar mini Sailuba ba za ta ta a warkewa ba. Sai dai zan iya taimaka miki na yi miko hanyar Shugaba Zurufu da ke Dajin Bururu ko zai iya shawo kan matsalar ya magance miki ita. Amma ina mai tabbatar miki yadda Umaima ta kassara rayuwar kishiyarta sai ta ninka abin da ta yi shi a kan Sailuba, mafita aya ce ko ki auki fansa ko kuma ki nemi makamin kare kanki." Ajiyar zuciya Jakadiya ta sauke cike da damuwa ta furta, "Duk wacce za a yi a yi Boka Shaddas, ka taimaka mini ni da 'yata Sailuba muna cikin matsanancin tashin hankali." Jakadiya ta arasa maganar tana dafa afar Boka Shaddas. "Matso ki ji abin da zan fa a miki!" Jiki na rawa Jakadiya ta matsa saitinsa nan take ta ji wani irin oyi ya mamaye ta. Ya jima yana yi mata ra a a kunne lokaci aya Jakadiya ta bushe da wata irin dariyar eta har da hawaye, ta jima tana abu aya sannan ta furta. "Ka biyani ko ba sisi ubangidana, yadda ka ce haka za a yi a shirye nake ba ka ha in kai matu ar a kan Fulani Umaima ne domin ku kifar da jagorancinta." Sai da Boka Shaddas ya auko wani mudubi ya sa a gabansa ya ura masa ido sannan ya furta, "Amma da shara i Jakadiya domin a baya ina yi miki aiki ne saboda hannu ya san na gida, a yanzu kuma dole za ki rama wa kura aniyarta." Jakadiya ko ka an ba ta damu da abin da Boka Shaddas zai bu ata ba don haka kai tsaye ta furta. "Duk abin da kake bu ata a shirye nake na aiwatar maka da shi duk rintsi duk wahalarsa matu ar zai biya mini bu atata." Boka Shaddas ya saki murmushi a karo na biyu sannan ya sake yi wa Jakadiya ra a a cikin kunne, a hargitse ta ago cikin tashin hankali tana kallonsa, ya gya a mata kai cikin halin ko inkula. "Idan har kina bu atar na yi miki jagora wurin Shugaba kuma na wanke acin ran da Fulani ta dasa miki a zuciya sai kin aiwatar da abin da na sanar da ke, kuma ki san duk yadda za ki yi ki kawo mini duk abin da na bu ata cikin kogon tsafin nan." Nan take Jakadiya ta ji zuciyarta ta bushe ta dubi Boka Shaddas cike da warin gwiwa. "Na amince Shugaba zan an aiwatar da duk abin da kake bu ata." Boka Shaddas ya yi mata jinjina da hannu sannan ya ebo wa ansu garin magani da wata yamurarriyar mage wacce kallo aya za ka yi mata ka fahimci an tsaface ta ya dam a mata. Jakadiya ta yi masa godiya sosai sanan ta yi masa sallama ta baro Kogon zuciyarta fes. Mahaifiyar Umaima ta tafi da gudu wurin da Umaima ke ame tana ambatar sunanta tana ta a ta, tamkar dutse haka jikin Fulani Umaima ya koma ta andare a wuri aya ko wayar idonta ba ta iya motsawa. Wannan ya sake aga hankalin mahafiyarta don haka ta sake zubawa a guje ta nufi Bamaguje tana gunjin kuka. "Kai taimaka mini Bamaguje ka yi ha uri duk da ban san laifin da Umaima ta yi maka ba, don Allah kada ka kashe mini ita Bamaguje..." Da sauri ya buga mata tsawa ha e da katse ta. "Idan kika sake ambatar sunan Allah a wurin nan sai na halaki, ta u kamarmu ba sa ambatar sunan Allah a wurin ta ewa kamar nan." Gya a masa kai ta fara yi har lokacin kuka take ta furta. "Tuba nake Bamaguje tsafi ya shiga lamarinmu, ka dubi girman tsafi Bamaguje ka kada ka kashe mini Umaima. Duk cikin 'ya'yana ita ka ai na fi auna a zuciyata." Murmushin takaici Bamaguje ya saki sannan ya furta, "Gara ke kina da su da yawa idan kin rasa ta akwai 'yan uwanta. Kin fi kowa sanin Umaima ita ka ai ce 'yar da na mallaka a duniya kuma bayan ita ba zan sake samun haihuwa ba. Amma hakan ba zai hana na hallaka ta ba idan za ta kawo mini cikas a harkar bokancina, abin da ba ki sani ba hatta mahafina ni na datse numfashinsa na arshe don haka babu wanda ba zan iya kawarwa a fa in duniyar nan ba." Tsoro arara ya bayyana a fuskar Mahafiyar Umaima, nan
Chapter 50 · 0% Book details