Sashe 30
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanayin da Fulani take ciki na rashin Ru ayya ya sake tunzura ta game da Bayinta don haka kowannensu yake kaffa-kaffa da shayin yin abin da zai sa a mata. Ko motsi ka an idan ka yi matu ar bai yi mata ba nan take za ra zartar maka da mummunan hukunci. Dama yaya lafiyar kura ballantana ta ci nama. Lokacin da mutanen Masarautar mahaifanta suka arasa Masarautar Huddam domin yin gaisuwa sai Bayinta suka samu sau i game da tsangwama da yarar da suke fuskanta. Ranar larabar da Boka Shaddas ya umarce ta a ranar ne ta je turakar Sarki Abdul'aziz don ta aiwatar da udurinta, ta ji da i matu a da ta samu turakar tashi ba ya nan. Da sauri ta ada maganin a saman gadon sa ta yadda wayar ido ba za ta yi saurin fahimtar komai ba. Ta kewaya ban aki ta ha a masa ruwan wanka tana fitowa ta ji shigowarsa, cikin kissa ta sakar masa murmushi. Martanin murmushi ya mayar mata don bai manta ba rabon da ya ga fara'arta tun kafim rasuwar Ru ayya, ya rungoma ta jikinsa suka zauna a gefen gado yana kallon fuskarta da ta yi fayau saboda ramar da ta yi. "Sarkina barka da hutawa, da fatan kana cikin walwala da farinciki?" Tallafota ya yi suna fuskantar juna. "Sarauniyata kin fi kyau a haka don Allah ki cire komai daga ranki. A lokacin da Allah ya ba mu Ru ayya bai shawarce mu ba, don haka da zai kar e ta ba zai yi shawara da mu na. In shaa Allah, zai ara azurta mu da wasu masu albarka a nan gaba." Take idanunta suka ciko da walla, ganin haka ya sa ya goge mata yana kwantar da ita a irjinsa. "A baya ne nake kewar Ru ayya Sarkina domin sha uwar a da mahaifi daban take, ta fi gaban duk mai tunani. Babu wacce za ta fahimci hali da damuwar da nake ciki mahaifiya kamar. Damuwata ta yaye unci ya kau, a yanzu tun da ina da kai ba za ka sake ganin walla a saman fuskata ba, ka zame mini taurarom da ke hasken birnin zuciyata don kawar da duhun da ya ratsa ta na 'yan kwanakin d suka shu e. Allah ya ara lafiya da nisan kwana Sadaukina, kulawarka a gare ni na ara mini warin gwiwa ari bisa ari." Ya ji da in kalamanta warai don haka ya ci gaba da bubbuga bayanta, babu jimawa hirar ta su ta fara sauya salo har Fulani Umaima ta ribace shi suka gudanar da mu'amala a saman shimfi ar kamar yadda boka Shaddas ya gaya mata. A wannan karon Takawa ne ya fara zuwa ban aki ya tsaftace jikinsa da ruwan da Fulani ta ha a masa wanda ya ji magani da sihirtattun turaruka masu amshi, bayan ya fito ita ma ta fa a ta yi wanka ta dawo kusa da shi ta kwanta. "Ki taso mu je bakin bishiyar kukar can kada ki sa na yi asarar ku ina Sailuba, ke fa idan kika sa kanki kin fiye gardama da taurin kai." Jakadiya ta yi maganar asa- asa ganin Sailuba na ata fuska. "Inna ya za a yi a ce na tu e a bakin bishiya da tsohon daren nan don Allah, ni wallahi kunya nake ji ba zan iya ba." "Sakaryar banza da wofi, wannan ita ka ai ce damar da ke gaban kuma idan ta wuce ta tafi kenan har gaban abada. Matu ar kika bi umarnina nan da an wani lokaci kema za ki zama Fulani a gidan wallahi ko tantama ba na yi, sai kin kasance matar Takawa kamar yadda Umaima ke ji da kanta." Jin haka ya sa Sailuba ta mi e da sauri, cikin san a suka nufi bayan akunan Bayi, a bakin wata bishiyar kuka suka tsaya sai da Jakadiya ta kalli hagu da dama sannan ta kunto garin maganin ta juye shi a butar gabanta da ke cike da ruwa. Daga can jikin katanga Uwar tuwo ce a ra e tana le en Jakadiya cike da mamaki, dawowarta babu wuya daga ban aki ta ji kalaman da Jakadiya take yi wa Sailuba. Tana nan tsaye har Sailuba ta tu e kayanta Jakadiya ta fara watsa mata ruwan maganin har ya gama gauraye jikinta gaba aya, tana ganin sun tunkaro wurin ta yi saurin komawa ta fa akinta. Jakadiya ce ta fara wucewa sai Sailube da ke lullu e kamar sabuwar amarya. Uwar tuwo na ra e a jikin labulenta ta ga giftawarsu. Jinjina kai ta shiga yi cike da mamakin Jakadiya, wani tunani ya gangaro cikin kwanyarta lokaci aya ta saki wani shu'umin murmushi mai auke da wasu ma'anoni. "Boka Bamaguje ya sanar da ni kin janye jikinki daga wurinsa, sai dai duk yadda na so jin dalilin haka abin ya faskara daga bakinsa. Me ya sa kike son jefa kanki a angin rayuwar da ba za ta fisshe ki da komai ba, kin san muhimmanci Bamaguje kuwa da kike son watsa masa asa a ido?" Mahaifiyar Fulani Umaima ta rattabo kalamanta cikin acin rai. Fulani Umaima ta ha e fuska, da farko kamar ta sanar mata abin da ya ha a su, sai kuma ta ce. "Na samu wani sabon boka ne kuma aikinsa tamkar yankan wu a haka yake." "Ai shi kenan tun da haka kika za a kowa rai ya yi wa da i ba ya mai shi ba, ni kaina ba don taimakon Bamaguje ba kin san ni da ke da ba mu samu wannan fadar haka ba." Fulani Kilishi wato mahaifiyar Fulani Umaima ta fa a, don ba ta son ja da nisa saboda ko ka an ba ta san abin da za ata mata rai. Bayan kwana biyu tuni kowa ya watse ya rage sai ainihin mutanen cikin masarautar. Wataranar Juma'a da yamma Jakadiya auke da tiren kayan marmari ita da Sailuba suka nufi sashen Takawa, fuskar Sailuba ta sha kwalliya kamar wacce za ta gasar kyau. A lokacin da suka shiga yana zaune yana rubuta wasi ar da Sarkin Gumel ya turo masa a game da wani kasuwanci da yake son su fara ullawa, Jakadiya ce ta arasa gabansa ta dire tiren hannunta. "Barka da hutawa Uban gidana, farincikin talakawa da marayu. Hatta masu iyayen ma ka riga da ka gama musu komai. Allah ya ja zamaninka ya tsare gabanka da bayanka, gaba salamun baya salamun an toron giwa." Sai da ya arasa rubutun da yake ba tare da ya kalle ta ba ya furta, "Jakadiya an yi sara a kan ga a, don yanzu muke shirin aikawa a kira mana ke." Jakadiya ganin ba ya kallonsu ya sa ta an zunguro Sailuba da ta yi galala tana are wa falon hutawar Sarki Abdul'aziz, da ya sha kayan ado da yali iri-iri. "Allah ya baka yawan rai muna godiya da wannan nuna yabawar." Sai a lokacin Sailuba ta an sake ma e murya ta ce. "Barkanka da hutawa Sarkin sarakai, fari mai farar aniya bangon sikari a bika a lasa idan babu kai a zubar da walla." Jin sauyin murya a kan wacce ya saba ji ya sa ya ago a hankali ya dubi wurin da Sailuba take, ganin haka ya sa a yangance Sailuna ta isa gabansa da ragowar kwandon kayan marmarin ta ajiya tana fa in. "Idan Mai martaba ya lamunce shin zan iya yanka masa kayan marmarin a yanzu ko sai zuwa an jima." Wata irin ajiyar zuciya ya sauke har lokacin idanunsa irr a kan Sailuba, mamakinsa aya bai wuce yadda aramar yarinya ta iya wassafa kalaman ban girma a mai girman matsayi kamarsa ba. "Idan kuma Mai martaba ba ya bu ata zan jira a ofa har zuwa lokacin da zai bu aci a yanka masa. A gafarce ni idan akwai kuskure a kalamaina ranka shi da e." Sailuba ta arasa maganar tana sunkuyar da kai asa kamar sabuwar amaryar da ke gaban surukarta. "Muna da bu atar kayan marmarin." Sarki Abdul'aziz ya furta a takaice, sannan ya janye idanuwansa da yar ba don zuciyarsa ta daina azalzalarsa a kanta ba. Jakadiya ta lura da yanayin da Mai martaba ya shiga don haka ta saki murmushin yin nasara a fakaice. Ta russuna tana fa in, "Ranka shi da e a yi mini izini na tato maka ruwan 'ya'yan ibini." Gya a mata kai ya yi sannan ta fice daga falon zuciyarta fes. Hakan da Jakadiya ta yi ne ya sa Sailuba ta samu damar yanka kayan marmarin tana yi tana karairaya cike da jan hankali. A fakaice Takawa yake satar kallonta da ta ago sai ya auke kansa ya ci gaba da abin da yake yi, suna nan zaune Fulani Umaima ta shiga cike da isa da asaita. Ganin Fulani Umaima ya sa zuciyar Sailuba ta yi ba i ranta ya yi mummunan aci, a ciki-ciki ta dubi Fulani Umaima ba tare da ta rissina ba ta ce. "Barka da shigowa." Galala ta yi tana kallon Baiwa Sailuba don ba ta jin akwai wanda ya ta a yi mata irin wannan gaisuwar ta rashin ladabi. "Dakata!" Cak! Sailuba ta tsaya tana kallonta kanta a asa. "Lokaci na nan zuwa da za mu fara ha a kafa a, ba dai ta amarki Takawa ba. Da sannu sa na mayar da ke bora fiye da yadda kika mayar da kishiyarki." Sailuba ta yi maganar a cikin zuciyarsa. "Ko mahaifiyarki ta cancanci ki gaishe ta a haka ballantana ni?" Fulani Umaima ta fa a a wula ance. Shiru ya ratsa ba tare da Sailuba ta amsa ba, kuma ba ta jin za ta iya amsa mata don gani take a yanzu marabarsu ka an ya rage. "A ba mu wuri muna bu atar ke ewa." Sarki Abdul:aziz ya furta ba don ya gaji da zaman Sailuba ba sai dai don ba zai juri ganin yadda Fulai Umaima take daka mata tsawa a gabansa ba. "Yadda kake so haka za a yi ingarman mazajen sarakuna, sarkin sarakai mai ri e da kambun da babu masarautar da ke auke da shi a kaf fa in nahiyar nan. Ka huta cikin aminci ranka shi da e hasken talakawa, na barka lafiya bujimi namijin fama." Cikin wata irin murya mai fusgar hankali Sailuba