Sashe 61
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na yi maka da jikan Malam Idi ce maka na yi idan ka kuma auko mana magana za ka fuskanci hukunci mai tsanani kuma ka amince. Furhussam me ya sa kai da zuri'arka ne ka ai kuka fita zakka a cikinmu? Ba za mu lamunci wannan isakancin ba, don haka Maharaz ka auki yaron nan ka wuce kuma daga shi har zuri'arsa duk wanda ya kuma shiga gonar yaron nan na ba ku umarnin ku one shi." Farinciki ya lullu e Dattijo Maharaz, Malam Liman ya shiga zabga masa godiya sannan Dattiijo Maharaz ya sa hannu ya rufe wa Kamalu idanu nan take suka ace sai ga su a akin Sarki Abdul'aziz. A razane duka mutanen cikin akin suka mi e wa ansu daga ciki har da masu neman wurin uya, shi kansa Sarki Abdul'aziz sai da ya yi ta maza ya iya tsayawa. "Dattijo Maharaz kai ne?" Sarki Abdul'aziz ya furta cikin tsananin farinciki. "Shin ka ba ni dama na araso cikin iyalanka?" Dattijo Maharaz ya wurga masa tambaya. "Kai da kaya duka mallakar wuya ne Dattijo Maharaz! Na baka wu a da nama, ka araso ka warware mini zare da abawa don tun tafiyarka ka bar ni a cikin duhu." Dattijo Maharaz ya ru o hannun Kamalu suka arasa cikin rumfar suka zauna, da idanu su Fulani Umaima suka bi su da kallo. "Ko ba ka fa a mini ba, na san ka sha gwagwarmaya farin Dattijo mai farar zuciya da dattako!" Sarki Abdul'aziz ya yi maganar cike da girmamawa. "Kusan alhakina ne yin hakan Abdul'aziz, kuma na yi farinciki da na sauke wannan nauyin da yake kaina. Ga anka nan halak-malak na dawo maka da shi, Kamalu ga mahaifinka nan kai an gaban goshi ne, mai gata ne kuma an asali ne kai." Da mamaki Kamalu ya dubi Dattijo Maharaz. "Ni in kuma Dattijo Maharaz? Ka san me kake fa a kuwa? Ka manta me Baffajo ya furta mini dangane da asalina?" "Akwai tarun tambayoyi a bakina Dattijo Maharaz ban san yadda aka haihu a ragaya ba." Sarki Abdul'aziz ya fa a a sanyaye. Dattijo Maharaz ya saki murmushi irin nasu na manya sannan ya nuna Fulani Umaima. "Ba za a ta a jin mutuwar Sarki a bakina ba Abdul'aziz, Umaima ita za ta warware mana zare da abawa domin ita ce ta san yadda aka haihu a ragaya." *SHU'UMAR MASARAUTA* *32* .*Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Bayan aurin auren sabon Sarki Sulaiman da Fargi cikin farinciki ya shiga akin da take zaune a takure wuri aya ta zuba uban tagumi. "A yanzu wannan lokacin ba na damuwa ko acin rai ba ne!" Sulaiman ya furta yana har e hannuwansa biyu a irji ha e da sakin murmushin farinciki. agowa ta yi ta goge hawayenta a madadin ta yi walwala sai ta sake fashewa da uka, jiki a sanyaye Sulaiman ya arasa wurinta. Ta sunkuyar da kai asa tana murza yatsun hannuwanta. "Na so a ce zamu yi rayuwar farinciki tamkar yadda sauran ma'aurata suke gudanar da rayuwarsu, sai dai kash! Ba lalle mu samu wannan damar ba. Domin ina tsoron ranar da Shugaba ko wani daga cikin dangina zai banka a labulen sirrinmu...." Da sauri ya arasa ya rufe mata baki yana sauke ajiyae zuciya. "A duk lokacin da kika yi wannan furucin irjina yana bugawa, don Allah a duk lokacin da za ki yi tunani ki dinga yi mana na alkairi." Gya a masa kai ta yi sannan ya ajiye mata gasassun 'yan shilan da ya sa aka gasa musu. Sannu a hankali Sulaiman da Fargi suka fara cin 'yan shilan hankali kwance tun tana no ewa har ta saki jiki suka ci suka oshi, sai da ya ja ta hira sosai don ya kawar mata da duk wani tsoro da fargabar auren nasu da ke cikin zuciyarta sannan ya ce ta shirya don ya mayar da ita. Murmushi ta sakar masa sannan ta ha a hannuwanta ta tafa su nan take ta riki e zuwa siffar tantabara, a daidai kan kafa ar Sulaiman ta hau tana ka a fukafukanta. Shafata ya fara yi yana murmushi don ya fahimci tun da ta yi nasa haka ba ta bu atar ya yi mata rakiya. Sai gab da magriba Sulaiman ya koma cikin Masarautarsu a nan ya tarar an kawo masa amarensa biyu, wani irin takaici ne ya kama shi amma da ya tuna a yanzu Fargi ta zama matarsa sai ya ci gaba da walwalarsa har wasu daga cikin dangi suna tsokanarsa wai har ya sauko daga iyayyar auren, saboda da farko ya nuna gaba aya ba ya aunar auren ha in da za a yi masa. Boka Shaddas bayan ya mayar da littafin yana juyowa daga can wurin wannan rijiyar ya ji wata irin ku a ta ratsa majiyar sautinsa, ajiyar zuciya ya sauke don tun da ya ji wannan ku ar ya san akwai wani muhummin taron gaggawar da ake bu atarsa a fadar Sarkin Aljanun dajin Hubud. Sai da ya arasa wurin Basiru sannan ya furta, "A yanzu haka na samu kiran gaggawa daga wurin madogarar da suke ba ni warin gwiwa dangane da sirrin tsafi da sihirina, duk wani aiki da ba zai gagare maka ba ka aiwatar da shi don na san kai in gwani ne kuma hatsabibi ne." Wani asaitaccan murmushi Basiru ya saki har sai da gaban Boka Shaddas ya fa i, don bai san dalili ba haka kawai yake jin zuciyarsa na wasu-wasi a kan Basiru. "Yaushe za ka dawo? Don gaskiya ina da aikin da zan aiwatar a cikin tsakiyar dare kuma ba na jin a nan zan aiwatar da shi." Basiru ya fa a wa mahaifinsa wannan maganar don ya kawar da tunaninsa daga zarginsa. A fili Boka Shaddas ya fa a fara'arsa munun fuskarsa ya aru, kalaman Basiru suka yi tasiri a ransa. "Ka yi mini uzuri ba na jin zan shafe sa'a guda." Basiru na gama sauraron mahaifinsa ya wuce can bakin wutar da Boka Shaddas ya tanadar masa wacce yake binciken duk wani abin da ya shafi al'amarinsa na tsafi. Shugaba Zurufu uri ya yi wa Jakadiya da ke gurshe en kuka, kuma ya yi mamakin ganinta bayan ya san Boka Shaddas ne ya yi mata iso a can kwanakin baya. Yana shirin katse kukan nata ta sake rushewa da kuka tamkar wacce sa on mutuwar Mahaifyarta ya riske ta. "Ya shugaba mai shugabancin wannan yankin ka taimaka miki ka shiga lamarina, duniya ta yi mini unci yayin da bala'o'i suke rufto wa rayuwata da ta 'yar auta." "Shaddas ya jima yana yaudararki don haka matsawar kika ta e a wurinsa bu atarki ba za ta ta a biya ba." Shugaba Zurufu ya furta wa Jakadiya yana watsa wata jar asa saman allon arfen da ke onewa a kan wuta. "Na jima da fuskantar haka Shugaba don haka na sato afa a yanzu da na kawo ziyara wurinka domin kaine mai share mini hawayena." "Abu aya za ki yi mini matu ar kina son bu atarki ta biya, ni nan da kike gani tun da na sa tsafi a gaba nake ganin ci gaba don haka tsafi ba zai ta a ba ni kunya ba. Yau ina matashiya Fargi da ke nuna za ta iya kara wa da ni, tana in a yanzu? Babu ita tun da na shafe babinta. Jakadiya bu atarki za ta biya kamar yadda na fa a miki amma sai kin kawo mini Basiru an Boka Shaddas, kuma sai kin ha o mini da littafin hannunsa. A yanzu haka zancen da nake yi miki Basiri ya mallaki wannan kundun littafin domin ba aramin hatsabibi ba ne, Duk hatsabibancin mahaifinsa shafar mai ne a kansa. Idan kika cika wannan Umarnin Sailuba za ta warke, zan iya kashe miki Umaima idan kuma sabautata kike bu ata ayi nan take zan zartar da shi." Baki na rawa Jakadiya ta furta, "Shugaba a baya Boka Shaddas ya sha yi mini irin wannan al awarin amma ko ka an ba ta sauya zani ba..." "Dataka Jakadiya! Shaddas ko afarmu bai kama ba ballantana ki ha a tsafina da na shi, idan kika kuskura kika sake yi mana wannan furucin za mu shafe ki a doron asa." A razane Jakadiya ta hau girgiza kai, ta zube asa tana ba shi ha uri sai da ya kar i tubanta sannan ya dam a mata magunguna da kayan binne-binnen da za ta yi, ta shiga zabga masa godiya har ta juya za ta tafi Shugaba ya dakatar da ita. "Waccan ziyarar Boka Shaddas ne ya biya miki tukwicin ziyararki, a yanzu kuma dole ki biya wa kanki domin wannan zuwan kanki da kanki ne." Gaban Jakadiya ya fa i, a sanyaye ta furta. "Mene ne tukwicin ya shugabana?" "Tun da wannan zuwan da kika yi zai zame miki tamkar zuwan farko ne, da farko zan ha a ki da an autan ba an aljanun asan ruwa ya yi mu'amala da ke." Da sauri Jakadiya ta ja da baya hannuwa biyu dafe a irjinta cikin tashin hankali ta furta. "Yau ni Salame na shiga uku na lalace! Shugaba ka yi mini rai kada ka yi mini haka wallahi rabona da wannan lamarin har na manta, marigayi Malam Bukar yau shekara Ashirin da biyu kenan." Shugaba Zurufu ya tamke fuska don tuni Jakadiya ta fara tunzura shi, ya nuna ta yatsa yana fa in. "Kada ki kawo mana wargi yanzun nan na mayar da ke Fanteka ko kumbo. Jakadiya wannan doka ce ga duk wanda ya ziyarce mu a ziyararsa ta farko. Don haka da ki amince da karki amince Aljani Buguzu zai amarce da ke a daren yau, gata ma na yi miki da ban ha a ki da Bulku ba, domin shi zai iya yin fata-fata da ke." Jakadiya ba aramin firgici ta shiga ba, cikin tashin hankali ta fashe da kuka har da majina tana fa in. "Ka yi mini rai Shugaba kada ka sa Aljani Buguzu ya turmushe ni wallahi ni ko an autan bunsuru ban ta a ma'amala da shi ba, idan ka ha a ni