Sashe 4
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: irarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce abila da Masarautunsu ba. SHAFI NA BIYU Ras! Ta ji gabanta ya yi mummunan fa uwa, lokaci aya ta nemi yawun bakinta ta rasa. Cikin firgici ta bu e baki za ta yi magana Fulani Umaima ta katse ta. "Me kike yi a nan kuma uban me kike le e?" Maimuna ta zube a asa jiki na rawa ta furta. "Ki yi mini aikin gafara uwar gijiyata, na zo na ji ko Fulani nada bu atar wani abu kafin na tafi." Da hannu Fulani Umaima ta nuna mata hanya, sum sum sum Maimuna ta fice jiki na karkarwa. Fulani Umaima ta le a Fulani babba da ke kwance, ta saki murmushi mai auke da ma'anoni a hankali ta furta. "Mu zuba mu gani idan tusa na hura wuta, in dai ni ce yanzu kika fara gani." Daga haka ta fice daga akin. Fulani babba ta jima a haka sannan ta farka, a hankali take sauke ajiyar zuciyata. Duk da a mafarki ta ga Mai martaba yana kusantarta abin ya yi mata da i, ta ji farinciki matu a saboda idan ba mantawa ta yi ba rabon da wani abu ya shiga tsakaninta da Takawa tun cikin jikinta bai fi wata biyu ba. Danshin da ta ji a jikinta ne ya sa ta kai hannunta, da mamaki take kallon makwancin nata. Da yar ta yun ura ta tashi nan take fitsarin da ke na e da zaninta ya fara iga, da farko ta yi tsammanin ko faya ce ta fashe mata tun da a halin da take ciki tana iya haihuwa a kowane lokaci, musamman da take jin ciwon mara sama-sama. Sai dai zarni-zarnin da ta ji ne ya sa ta shinshina hancinta. A hankali ta furta. "Fitsari? Ni kuma? Kai ina jin dai faya ce ta fashe." Gudun wasu-wasi ya sa da kanta ta ebo ruwa ta sa a katifar ta sauya kayan jikinta amma har lokacin gani take faya ce ta fashe mata. Ban aki ta shiga ta yi wanka ta fito sannan ta an ci abinci, a hankali ta ji mararta na ci gaba tsikararta daga baya bacci ya sake yin awon gaba da ita. Fulani Umaima kai tsaye sashenta ta wuce don a ranar ba ta jin sha'awar zuwa wurin Mai martaba. Da shigarta babu jimawa sai ga Jakadiya ta shiga angarenta da sa on Mai martaba na gayyatarta zuwa turakarsa, ba don ta so ba haka ta amsa mata. Jakadiya har za ta tafi Fulani ta dakatar da ita. "Jakadiya ba na son ki yi nisa da sashen Fulani babba." Jakadiya ta amsa mata sannan ta fice. Cike da kissa Fulani Umaima ta shirya kanta da sihirtattun turarrukan da Bamaguje yake ha a mata, ta arasa turakar Mai martaba. Zamanta babu jimawa suka ji wata arar busar sarewa. Da sauri Fulani da le a kusurwar turakarsa idonta ya sauka a kan aton shurin da gudajen turuwa suka zagaye da ke cikin akin, gabanta ya yanke ya fa i don ta san tun da ta ji wannan sarewar a yau mai afkuwa za ta afku. Mai martaba ya saci kallonta, haka kawai yake jin shakkarta a zuciyarsa. Amma ko shakka babu wannan busar sarewar da shuri ya saki na da ala a da cikin jikin Fulani babba wanda yana da ya ini za ta iya haihuwa a cikin daren nan. Ya so ya tanka wa Fulani Umaima amma sai ya fasa, hakan ya sa ta saki murmushi cikin kissa. "Jikina yana ba ni Fulani babba na gab da kawo mana Yarima, wannan abin farinciki ne. Tun da shuri ya saki sarewa na tabbata a yau za mu iya samun aruwa a gidan nan." Fa a murmushinsa ya yi, ya janyo Fulani Umaima jikinsa ya furta. "Wannan haka ne yanzu me kike ganin ya kamata a yi?" "Ina ganin zai fi kyau a yi dakan aka shi aka... sai a kira Jakadiya ta zauna a wurinta koda ciwon zai tashi tana kusa da ita, a madadin a kira Ungozoma. Amma sai yadda kace ranka shi da e farin jakada." Fulani Umaima ta arasa magana tana sunkuyar da kai asa. Ajiyar zuciya Mai martaba ya yi, "Na baki wu a da nama mai farar zuciya Allah ya yi miki albarka." Fulani Umaima ta amsa sannan hirar tasu ta fara sauya salon faranta ran ma'aurata. Zuciyar Fulani Umaima al ta je ta samu Jakadiya da zancan Takawa, Jakadiya na gama sauraronta ta yi asa da murya tana an waige sannan ta ce. "Wani ma ya yi rawa ma ballantana an maka i? Ai wallahi sai mun ga abin da ya ture wa buzu na i. Ina mai yi miki albishi tauraruwar Mai martaba gobe war haka Fulani Babba na nan cunkushe da ba in ciki fal irjinta, idan an isa a yi Yarima ba a akinki ba shegiya nake." Fulani Umaima ta saki dariyar eta. "Jakadiya tamkar zuma haka kike ga za i ga harbi. Na aminta da ke fiye da haka ma za ki iya aikatawa." "Ai shi abin kasuwa na mai ciniki ne, ni ta ki ce Fulani har abada ina bayanki. Fulani kin manta ayan kirarin nawa kaska rabi mai jini ki bar shi da gashi." Fulani Umaima ta jinjina kai alamun gamsuwa. Jakadiya ta sake asa da murya. "Allah ya taimake ki ni zan arasa zan biya na taso Baiwa Maimuna da zarar haihuwa ta taho gadan-gadan zan turo miki ita." Murmushi Fulani Umaima ta yi har Jakadiya ta yi gaba ta sha gabanta da sauri ta furta. "Jakadiya a kawo mini kayan Bayi sashena, sannan a tabbatar an bawa Maimuna ta kawo mini cikin hanzari." Shiru Jakadiya ta yi tana nazaratar Fulani. Cikin zuciyarta tana ayyana warewarta a mugun makirci da uduri. Da sauri Jakadiya ta wuce angaren Fulani Babba a lokacin da ta arasa dare ya tsala sosai, sai da ta yi sallama sannan ta shiga har cikin akinta. Shigar Jakadiya ya yi daidai da farkawar Fulani babba, arasawa ta yi gabanta ta ce. "Allah ya taimaki uwar akina ya arawa Fulani lafiya. Yanzu haka Mai martaba ne ya turo ni a kan na kwana da ke saboda yanayin da kike ciki, domin tuni shuri ya saki sarewa." Murmushi Fulani ta yi don ko ba komai ta ji da in yadda Takawa ya ba ta kulawa, hannu ta mi a wa Jakadiya alamar ta taimaka mata. Wani abu ta ji ya tsira wa mararta ha e da bayanta. Cije baki ta yi jin ciwon na ara tsanani gadan-gadan. A haka ta mi e ta arasa ban aki da yar don ta gyara jikinta, a lokacin da ta tashi ta sake lura da fitsarin da ya ji e makwancinta sharkaf, na wannan lokacin har ya fi na baya yawa da wari. Fulani na dawowa kafin ta shiga akin ta ci karo da wata mata ba irin a tsaye a dokin ofa. Hannu ta mi a mata cikin wata irin murya ta furta. "Ba ni cikin jikinki!" Da Mamaki Fulani ke kallonta har lokacin ciwo na cin ta, "Wace ce ke? Me ya sa zan baki cikin jikina?" Tana rufe baki ta ga matar ta mi a hannuwanta masu auke da wa ansu irin ba en farata da za wa-za wan yatsu, ta mi a hannun da niyyar shafa saman cikinta, Fulani da sauri ta ja baya ha e da furta. "A'uzubillahi, Innalillahi..." Da gudu ta ga matar ta shige cikin sashenta, wata uwar ara ta walla nan take sai ga Jakadiya ta nufo wurin da gudu. Jiki na karkarwa Fulani ta ce, "Jakadiya baki ganta ba?" Jakadiya ta waiga hagu da dama ta ce, "Wa kenan ranki shi da e?" Dum! Fulani ta ji kanta ya yi nauyi tana son tuna a kan abin da Jakadiya take tambayarta amma ta manta, gumin da ke tsattsafo mata ta share ta ce, "Ba komai mu je Jakadiya marata ciwo take. Wash! Bayana zai alle." Jakadiya ta taimaka mata suka arasa ciki, kafin fitowar Fulani daga ban aki tuni Jakadiya ta gyara wurin ta ha a gaba aya kayan kar ar haihuwa. Ganin za i ha e da jini ya fara bin afar Fulani ya sa Jakadiya ta shimfi a mata atuwar le a, Fulani da yar ta yun ura ta hau kai tana jin asanta tamkar a zai fa o. Fulani Umaima ce ta yi sallama daga bayanta Baiwa Maimuna na biye da ita, yadda Fulani Umaima ta marairaice tana yi wa Fulani babba sannu sai ka rantse zuciyarta cike take fal da tsoron Allah. Wani jan o ta mi a mata ta furta, "Mai martaba na cikin tsananin damuwa da jin halin da kike ciki, musamman da ya tuna da mutuwar Marigayya Fulani Samira. (Matar Sarki Abdul'aziz ta uku ce da ta rasu wurin haihuwa.) Ya umarci da a kawo miki wannan yanzu na kar a a hannun Shamaki." ago kan Fulani babba ta ga Fulani Umaima ta sauya mata a kammani, har take ganin kamar ta ta a sanin kamannin, sai dai kuma ba ta jin za ta tuna kalar fuskar. Baiwa Maimuna da ke tsaye jikinta ya yi sanyi don ta san garin maganin ba ya wuce na wurin Bamaguje. Fulani Babba ta kar e za ta kai baki ta ji wani irin nishi ya taso mata, cikin tsananin azaba ta wurgar da waryar gefe ta ri e Jakadiya da ke gefenta, take jaririn ya fa o ya fara mutsu-mutsu yana tsanyarewa da kuka. Wani irin ba in ciki ya turni e ta Jakadiya ta waiga tana kallon Fulani don sanin irin hukuncin da za su yanke, da sauri Fulani Umaima ta fita sakamakon manta kunamar da Bamaguje ya bata. Jakadiya ta tsugunna ta sa reza ta yanke masa cibiya, a tunaninta ko Fulani Umaima ta zubda makamanta ne tun da jaririn ya riga da ya zo duniya. Ta gama yanke masa cibiya kenan Fulani Umaima ta fa akin hannunta auke da wata atuwar kunama, a daidai lokacin Fulanin ta sake wani yun urin babu jimawa wani jaririn ya fa o. Kusan mutuwar tsaye gaba aya suka yi, fuska babu walwala Fulani Umaima ta arasa ta ora kunamar a kan jinin da